← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 35

Sashe 31

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haydar ne ya shigo fakam-fakam yana tafiya kamar wanda ake hankaɗowa bai iya sallama ba don haka bai tsaya yin ta ba ya ƙaraso kan Leelah ya tsaya ƙerere ! sai huci yake yi tamkar garwashin da aka watsawa Ruwa. "Maza ki tattara kayanki zan aiko a ɗauke ki, barin Gidan nan za mu yi!!" ya faɗa a fusace tamkar ita ta yi masa laifin.
Wani sabon tashin hankalin, indai ba gizo kunnenta ya yi mata ba ji ta yi ya ce barin gidan za su yi, wannan wace irin masifa ce??, idanunta da suka fara yaji da suya ta zuba masa cike da son ƙarin bayani, tana son tambayarsa amma ta kasa.

Muguwar Kibiya me ɗauke da dafin Azaba gami da Kishi ta soki ƙahon Zuciyarta har sai da ta zabura, Zuciyarta ta dena harbawa na wucin gadi. Ba komai ne ya jawo mata ba face ganin Alina a cikin Ƙirjin Haydar tana wani irin kuka me tsuma Zuciya gami da rikita lissafin me sauraronsa.
Hankali tashe ya fara tambayarta abinda ya faru, ƙara ƙanƙame shi ta yi cikin shashshekar kuka ta ba shi labarin Leelah ta yi mata Zagin tsamar nama, har da gori da goruba.

https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx

Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136

Tamkar Zakin da ya shekara Biyar bai ci komai ba sai yau ya yi Tozali da nama haka ya nufi kan Leelah jikinsa har rawa yake yi, cikin matsanancin tashin hankali ta miƙe tana yin baya-baya gami da girgiza masa kai, bakinta sai karkarwa yake yi sabida son furta kalami amma ko ɗaya ya kasa fitowa, cikin zafin nafa ya kwarfa mata wani azababben mari kafin ta gane inda kanta yake ya ƙara sakar mata mahangurɓa wato marin bayan hannu.

Wani azzalumin duhu ne ya mamaye fitilun dake haska ganinta, kanta ya shiga wata irin hajijiya da taratsi tamkar wanda aka jona wa shocking, yayin da hawayen azaba suka gangaro kan kumatunta ba tare da ta sani ba, gefen bakinta kuwa tuni ya fashe jini ya fara bi-bango. Durƙushewa ta yi kan gwiwoyinta cikin wani irin mawuyacin halin da kimanta shi ma aiki ne.

Rufe ido ya yi ya fara zazzago masifa ba ji ba gani Auren Kurma da Makaho, "Har ke kin isa ki ɗagawa wadda na kawo cikin Gidana murya??, har me akai aka yi ki?? uban me gareki da har kike tunanin yin Kishina??, a tunaninki wata tsiyar na gani ta burgeni a jikinki da ta sa na aureki? uban me kike da uban me za ki iya ba ni da har za ki ciwa wadda take min komai Mutunci??, wallahi tallahi akan Ƴan Matana sai na illata miki rayuwa don ban ga abinda zan so a jikinki ba bare har na yi maneji, yanzu sai in tattara ki in kora ki Gidanku Shegiya Ƴar matsiyata!!".

Sai yanzu da masifar ta kai masifa ta tuno da ambaton sunan Allah, Innallillahi ta fara jerowa cikin ɗaga murya tamkar wadda ta Taka Mutanen Ɓoye.

Tana kallo ya rungumi Alina suka yi ciki, zamewa ta yi ta ƙarasa zama daɓar!!! kamar an juye laka, "Me ya sa za ka yi min haka Haydar??, me ya sa ka yaudareni? me ya sa ka Aureni bayan ka san ba So na kake yi ba?, ina matsayin Matarka amma Karuwarka ta fi ni muhimmanci a wajenka?, ashe da gaske Haydar kai Mazinaci ne??, me ya sa ? ta yaya na Auri irin wannan Mijin da bai san kima da martaba ta ba?? , na shiga Uku na lalace shi kenan rayuwata ta gama yawo" sai a lokacin wani mugun kuka ya samu Ƴancin fara nasa aikin.

Ta sha kuka kamar ranta zai fita, a wajen bacci me nauyi ya sace ta.
Bayan wani É—an lokaci ta fara jin sautin muryarsa a kanta, a bala'in firgice ta farka tana zazzare Kadarar Mujiya. Daga shi sai É—an Gajeren wando Alina tana gefensa cikin wasu arnan kaya wanda ba su da maraba da tsirara.
Wasu sabbin hawayen ne suka fara yin ambaliya akan kumatunta.
Masifar da ya shiga surfa mata ta sa ba shiri ta miƙe ta nufi ɗaki ta fara haɗa kayan nata.
Koda ta tafi ɗakin sai da ya bi ta ya ƙara zage ta tatas!!! ya bi ta da gori da cin Mutunci ba ita kaɗai ba har Danginta da iyayenta ba su tsira ba.

A ranar suka tattare duk kayansu aka dinga fitar da su zuwa Gidan Mami.
Tin da ya samu labarin Maa ta sayewa Aliyu Gidan ya hau Dokin Zuciya ya ce ba zai karɓi wani Gidan a Hannun Bhaba ba gwara ya zauna a ɓangarensa na Gidansu.
A can aka yiwa Leelah sabon jere da Kayan É—akinta, shi ma na shi aka jera masa a É—akinsa.
Haka Leelah ta kwana cikin mawuyacin hali, ga wasu mugayen mafarkai marasa daɗi da suka taso ta gaba, ga zazzaɓi da ciwon kai ga tunane-tunane.

"Ahahahayye!!, Yaraye nanaye! ayyiriri !! yaraye nanaye Ƴan Mata!!!, Filin cashewa ayyiriri !! filin cashewa Ƴan mata!!, kina da shi juya ahayye!!! kina da shi juya Ƴar Mata!!!" Salim ne ke Waƙar a tsakar Gidansu cikin ɗaga murya yana yi yana karya ƙugunsa da ya ɗaurawa Ɗankwali ya yi ɗamara, ƙarawa ya yi da cewa "Ahayye!!!! ni Salim Ɗin Salama Ɗan Gidan Dije da Usama ikon Allah!!! Kainuwa dashen Allah ba dashen wani Ƙaton Ba!!!, Turmi sha daka!!! sha kwaramniya Gugan Ƙarfe!!!, a yi da kai yanzu a yi da kai Anjima!; Ni dai ina ganin Rayuwa a Gidan nan wallahi!!"
Tuni Zazzaƙar muryarsa ta gama karaɗe Gidan waɗanda ke ɗaki ma saƙonsa ya isa gare su.
Kasancewarsa Kamar me Busa Khusur É—in fara Wasa da zarar ya dasa kowacce sai ta fito sai dai in ba ta Gidan.

Mama ce ta kalle shi gami da cewa "Ɗan Tijara! yanzu za ka kafa dama ai kwana biyu ba ka yi ba". "E na ji, lokaci ne da ya wuce shi kenan" ya faɗa yana farrr!! da ido gami da lallanƙwasa hannuwa.
"Me ke faruwa ne Ƙanina?" Ikilima ta faɗa tana ƴar dariya, Taɓe baki ya yi gami da cewa "Hmm!! mu Mazan Jiya Allah na tuba meye ba mu gani ba?, tinda Allah ya sa aka yi Bikin Leelah da Salama rayuwa ta yi min Tutsun Jaki, Ƙawayena na Gidan nan sun ƙara Kilewa kullum ba sa shan Kokon da ake Damawa sai dai a ci Buredi da Shayi har da Madara da Milo, ni kuma an bar ni da korawa Da markaɗaɗɗen Gero, haka wai da daddare ba a cin Tuwo sai dai a fita a kawo Pizza ko a yo Indomi, ga Samari Ƴaƴan masu Abin na lelewa a Unguwar nan don Ƴan Uwana amma babu wadda ta taɓa gabatar da ni a wurinsu, wataran sai dai na ji Ƙamshin Kaza ko na ga takardar tsire; alawadaran naka ya lalace wai Jakin Dawa ya ga Na Gida!!"
Rabi'a ta yi dariya kafin ta ce "Kafin na kama damata a duk hannayena na sha Iya shege a wajenka Salim, amma yau sabida ka ga Kumatukana sun fara maiƙo shi ne za ka zo da naka ƙauli da ba'adin, dama ai haka Duniya take ɗan hakin da ka raina shi ke tsokane maka ido, amma ba komai tsakaninmu da kai ai akwai Amana!" Mama ta yi murmushi ta hura hanci kafin ta ce "Salim kenan!!, in banda abinka ai ba kai ka fita ka nema ba bare ka sa ran samu". Ikilima ta ce "To in banda abinka nema fa akwai wahala, kai ma faka za ka yi ka fita ka nemo".
"Allah ya sawwaƙe!!, ku ma ku bi a hankali don wallahi Duniya ba gaskiya wai Ɓarawo ya rasa Shaida, yanzu sai ki je ba ki ci Kasuwa ba Rumfa ta faɗo miki, Allah Sarki Aunty Summi tana Garin KD in da tana nan na san ko ba ta ban komai ba za ta rarrashe ni, bare ma na san za ta ba ni".
Haja ta ce "Aikin banza! kai wallahi ka fiye sababin tsiya ma malam!"
"Ke tsaya!! sababi fa ya zama dole, kina kallo Leelah sabida ta Auri ɗan masu Kuɗi ko a waya ba ta ƙara cewa ina Salim yake ba, kin ga ai ni na ga sababi sababi ya gan ni!!" ya yi maganar yana murguɗe-murguɗe da tafe-tafe.
Momi ta ce "Ubanka!! sau nawa tana cewa yaushe za ka je amma sai ka ƙi zuwa?, kai fa ba ka da hali wai uwar akuya a kasuwa, shege da kai kamar sauran Minsileta!"
Dariya suka sa, Salim ma ya saki shewa yana cewa "Heee!! Allah Gatan Kowa, Momi Tawa ni ko na Allah, ni fa ba na son raini ne, gwara ma tin kafin wankin hula ya kai ta dare ki gaya mata Girman kai da Fariya Aikin Shaiɗan ne bayan Shaiɗan kuma sai magadansa, Shaiɗan da Magadansa kuwa kowa ya san Ƙarshen su Jahannama!!".
Wata langa ta wawura a kusa da ita ta miƙe tana cewa "Bari in faskara maka wannan a ka dan Ubanka sai ka ba ni bayani, shege ɗan Hassada". Artawa ya yi da gudu ya fice daga Gidan yana dariya.
Momi ta wurgar da Langar ta tunkuÉ—o kallabinta gaba ta kafa aradun Masifa.

https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx
Chapter 31 · 0% Book details