← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 35

Sashe 33

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ɗora idonsa akan Salma da ke zaune a bakin Gado, ba aikin fari ba na baƙi amma ta yi zaune kamar butum-butumi, da alamu ita ma ta tafi Duniyar tunani, "Salamaath!" numfashi ta fizga gami da zaro ido, ba ta yi tsammanin jin sunanta a bakinsa ba a daidai wannan lokacin, kasa amsawa ta yi bare har ta juyo ta kalle shi, "Me yasa kika kasa sakin jiki da ni har yanzu?? ko dan na ce miki wata ran za mu rabu?" da sauri ta girgiza kai alamar a'a, ɗan murmusawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Me ya sa to kina kallo na kasa bacci amma kin kasa tambayar lafiya ta??" sai a lokacin ta yi saurin juyawa ta zuba masa idanu don kuwa ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, ta daɗe da lura yana cikin tsananin damuwa sai da ta ga kamar abinda ya shafi danginsa ne ba ta son matsanta bincike a kai, musamman da ta san ba wai ya Aure ta ba ne don su zamo tsintsiya maɗaurinki ɗaya, wata rana dole rabuwa za su yi. Kaifin idanunsa ya sa ta sunkuyar da nata idanun ƙasa, cikin sanyi ta ce "Ina shirin tambaya sai ka riga ni sabida karambani irin na Yarinta". dariya ya yi gami da cewa "Eh! lallai kin ga makwancina Salamaath, har yarinta kike jona min ko??" dariya ta yi gami da cewa "Ƙanwata fa kake so, ka ga dole ne ka ba ni girmana, kuma kai ma kanka na ba ka watanni Shida, don haka a matsayin Ƙanina na ɗaukeka". lumshe idanunsa da suke yi masa yaji ya yi, ɓoyayyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya buɗe idanun nasa ya zuba mata gami da cewa "Ni kuma ban ɗauka haka ba, matsayin Matata na ɗauke ki; yanzu dai ki ajiye wannan zolayar ta ki, labari nake so ki ba ni wanda zai sa na yi bacci ba tare da wata damuwa ba".
"To fa labari kuma?, ni ban iya bayar da labari ba" "Ai kuwa za ki koya don ni bana bacci haka salin alin, Mamata da Ƙanwata sun riga sun sabar min sai ina jin motsin wani na fi samun nutsuwar yin bacci" abin dariya ma ya ba ta don haka ta dara tana cewa "Tab!, ai kuwa kana lukutin yanayi, ni kam ban iya wani labari ba sai dai in na ƴan Gidanmu kake so". "Ba komai, hakan ma na gode ai, dama ina son tambayarki wai ina Leelah take samun Manyan Kaya da waya da take amfani da su in za ta fita?" ƙara tuntsirewa ta yi da dariya tana cewa "To kai ina ruwanka?" "Babu ruwa na don na ma shanye shi, amma ina so ki ba ni naki. "Allah dai ya kyauta!!, wallahi wurin wata suke karɓo Haya, ita sana'arta kenan bayar da Hayar kaya tsala-tsala har da wayoyi da haka take samun kuɗi, haka za ka ga ƴan Matan Unguwarmu Ƴan Ƙarya suna ta zaryar zuwa Gidanta, wallahi abin dariya yake ba ni, lamarin Duniya sai Du'a'i !" ta ƙarasa maganar tana tuntsira dariya, shi ma dariyar yake yi yana jinjina lamarin na su Leelah, in Mutum bai sani ba in ya gansu sai ya rantse daga Gidan masu Ƙumbar Susa suka fito, "Gaskiya Mutanen nan Ƴan jirgi ne na asali, su kuma aikin su kenan bayin Allah, ke kuma ya aka yi kike wankau? ba kya yin Askin Aljihun ke?"
Zaro ido ta yi tana cewa "Ina ni ina Haɗiyar Gatari Aliyu?!!, ai ni wallahi tsarin da na taso a kai ban yarda da yin rawa da Bazar wani ba, haka Mahaifina yake yana da ƙoƙarin neman halak ɗinsa, bai yarda da bibiyar wani don neman temako ko bashi ba, haka muke rayuwa ranar da ya samu a ci ranar da bai samu ba a haƙura, hakan ne ma ya sa ni da Umma muke wankau don mu dinga Temaka masa muna temakon kanmu, daga baya ma Umma take ɗan fama da ciwon Ƙafa sai kawai nake yi ni kaɗai, da kuɗin muke ɗan kashe matsaltsalun Gida har Umma take sayen ƴan Kayan Kicin tana tara min."
tinda ta fara magana ya tsira mata ababen ganinsa yana murmushi, sai da ta gama sannan ya ce "Ashe ra'ayin mu ya zo ɗaya, shi yasa jinin mu ya haɗu sosai; ni ma kin ga Duk Kuɗin iyayena na fi son na tsaya da digadigaina, Mahaifiyata babbar ƴar kasuwa ce da ake damawa da ita a wasu daga cikin ƙasashen Afirka, sannan ana yi da ita a irin su China, India, Singapore, Australia, Pakistan, ke na manta sauran don ko ina ana iya jin ta, a ƙasar nan duk wani kwallin Roshan Kohl nata ne, haka irin lallen nan baƙi da Ja wanda ke da laƙabin Khushi duk nata ne, a ɓangaren Mahaifina ma Ɗan Kasuwa ne na ƙasa da ƙasa, amma hakan bai dame ni ba, ina kula da Dukiyarsa haka kuma ina neman nawa halal ɗin, na yi aiki tuƙuru kafin na fara kafuwa, yanzun haka na mallakin Kamfanin da ake sarrafa Robobi, sai dai ni na fi ganewa Kasuwancin haɗaka, wato wanda ake haɗa hannun jari, saɓanin Mahaifina wanda yake Taka rawarsa a Fage shi Kaɗai, ni ma ina son denawa amma na kasa sabida na riga na saba".
baki buɗe take kallonsa har sai da ya dasa aya sannan ta sauke wani gwauron nishi, "Allah ya gani ga Cuci Leelata Aliyu, me ya sa ba ka faɗa mata gaskiya ba?, ka san Allah tana sonka kawai don dai tana da son ƙyale-ƙyalen Duniya ne ya sa ta ture ka ta zaɓi Yayanka, gaskiya ba ka kyauta ba wallahi, dole ne ma na yi ƙoƙarin samar muku da farin cikin ku gabaki ɗaya".
Murmusawa ya yi kafin ya ce "Shi ya sa kullu yaumin ake yi mana wasiyya da cewar a dena raina Halittar Allah ko da ba Mutum ba ce halittar, bare kuma Ɗan Adam wanda Allah ya yi wa baiwa iri-iri kowa da kalar ta shi, kullum nasiha ake yi mana a kan raina Ɗan Adam da kuma ƙasƙantar da shi; Leelah ta sa ranta a wulaƙanta Ɗan Adam in banda haka da in ta ƙare min kallo za ta gane ni ba irin yadda take zato ba ne; ina so ne na koyar da ita darasin Rayuwar Duniya shi yasa na zaɓi ɓullo mata ta bayan Fage, hmm! da ta san waye ni da ba za ta taɓa Kallon Haydar a matsayin Namiji ba, ni kaina ina da arziki bare na shiga Rigar Iyayena, shi kuwa Haydar Mamarsa ta dogara ne da Arzikin Bhaba, asalinta kuma iyayenta ba masu ƙarfi ba ne, shi kuma Haydar ya kasa ɗaukar nasihar da muke yi masa ni da Bhaba a kan ya dena shiririta ya fara nema, shi ba shi da aiki sai shaye-shaye da biye-biyen Mata sai kashe kuɗi kawai don ya gansu kamar a banza, wai a hakan ma Bhaba yana taka masa burki, abin yana yi min ciwo na rasa yadda zan yi da shi, ni ina ƙaunarsa sosai, amma shi gani yake ba shi da Maƙiyi sama da ni sabida Bhaba ya fi jituwa da ni sannan kuma ina gaya masa gaskiya, irin halayensa yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke damuna". Sosai jikinta ya yi sanyi tuɓis!!, kallo ɗaya ta yi masa ta gane asalin gaskiyarsa duba da yadda idanunsa suka kawo ruwa fuskarsa sam babu alamun walwala, a gefe guda kuwa tausayin Ƴar Uwarta ya kama ta, ashe ma Ɗan shaye-shaye Mazinaci ta je ta Aura sabida tsabar son abin Duniya. Numfasawa ta yi kafin ta yi ƙoƙarin danne ta ta damuwar ta kawar da zancen ta kawo Labarin yadda suke haɗa wasan kwaikwayon ban dariya a Gidan su.
Sun sha surutu kafin suka sanyawa bakinsu sakata suka yi addu'a suka tinkari bacci.

Bayan wani É—an lokaci.

Shaƙuwa me tsanani ta shiga tsakanin Salma da Aliyu. Zaman su a Gidan su biyu ya temaka wajen haɗe kansu da sanya musu tsananin shaƙuwa, da yake duk ɗinsu gwanayen rawar kai ne haka suke kacakinsu su ɓarar su kwashe, su lalata su gyara, su yanka su feɗe su soya, su kashe su rufe. Ɓuruntu iri-iri ba wanda ba sa yi.

A ɓangaren Leelah da Haydar abin sai Innalillahi don tsiyatakun ƙara hauhawa suke yi Kamar ba shi da mafaɗi a Gidan, wai sunan Mahaifiyarsa tana nan. Tana zaune sai ya zo ya shige da Matan Banza Bedroom su gama Alfahasharsu su fito suna jefa mata magana gami da bin ta da kallon banza. Tin a satin su na Amarci bai ƙara haɗa Gado da ita ba amma kowane dare yana da Abokiyar kwana. Masifa da Gori kuwa ba kama hannun Yaro ahi ya yi Matan Banza da yake kawowa su yi Mahaifiyarsa ta yi, har ma baƙi in sun yi.

Ga kuɗi ga Daula ga sutturu manya tsala-tsala, ga Abinci me kyau ba shamaki, ga AC ga Kushin-Kushin masu taushi da sanyawa wanda ya hau su nutsuwa, tabbas irin Gidan take buƙatar mallaka a matsayin Gidan Miji sai dai yau an wayi gari ta mallaka ɗin a memakon ta yi ƙiba sai uwar rama da take yi kamar wadda ake ɗiba ana Miya. Rashin kwanciyar hankali da tsananin Damuwa sun zamo abokan rayuwart, Kullum cikin kuka take, idan ta dasa kukan hawayenta har ƙafewa suke yi, tabbas da suna ƙarewa ƙaran-ƙaf da yanzu babu labarinsu, ba ta da wanda za ta raɓa ta ji sanyi, gashi ta kasa gayawa kowa maganar don gani take ana ji dariya za a yi mata, don haka ko Momi ba ta faɗawa ba.
Chapter 33 · 0% Book details