← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 35

Sashe 11

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama, Rabi'a, Haja, suna zaune a É—akin Maman sun haÉ—e kai suna tattaunawa.......
"Dan Ubanku a gidan nan kowa yana abin arziki amma banda ku!, ke dama Rabi'a Ranar nan ina ji ina gani wancan Ɗan Daudun ya gama ce miki Ɓarauniya, Dan kan Ubanki kina mace amma kuɗin Ɗan Man Bulitin ɗin ya gagareki sai kin haɗa da sata!, kuna kallo Laila yadda take fantamawa da Samari iri-iri, ji wannan dai da ya zo Talakan nan, ko ni da na leƙa na ganshi sai da yawuna ya tsinke, kuma da yake Ɗan Halak ne har da Ƴar Ledarsa ya tawo, to ko irinsu kuke tarawa ai za a rage, ko ba komai za a ce kina da kyakkyawan Saurayi me zubin Larabawan Sudan, yanzu fa Rabi'a a matsayinki na Babba Samarinki Biyar fa kacal, kuma Ƴan iska duk ba sa sakin hannu ma kamar na Hajara" Mama ce ke maganar cikin ɓacin rai da takaici, su dai sun yi shiru suna saurarenta sai da ta gama sannan Rabi ta ce "To ba kya ga Leelah ta fi mu kyau? kuma ita fa tana shiga cikin Manyan masu kuɗi ba ta da Ƙawa ko Aboki Talaka, kin ga kuwa mu ina za mu samu irinsu?" "Ubanki na ce!" Mama ta faɗa tana watsa mata daƙuwa, ci gaba ta yi da cewa "In banda rashin godewa Allah me Laila za ta nuna muku??, kuna da gaba kuna da Baya, kawai don haskenta irin na Turai ne shi kenan?? ɗan hancin ma da take taƙama da shi kuna da shi sai dai kawai ta ɗan fi ku karan hancin, wallahi da Rabi'u mace ne da na huta, ku na ga ba abinda za ku iya yi min, gashi Rabi'un ma duk da shi ne Autana ya fi ku kyau". Haja ta ce "Gaskiya fa Mama kina kan hanya, ni ma abin nan yana damuna, ya kamata mu nemi mafita, kowa ya fi mu Samari da Kuɗaɗe a Gidan nan, ki duba ki ga su Anty Summy don Allah, su ci me kyau su sha me kyau su sa sittira me kyau, ita kanta Leelah wani lokacin a wajen Summy take aron kaya take sakawa ta fita tana burge Samari ". "Rabi'a ta ce ita fa Summy maganar gaskiya tana Karuwanci, ni kuma da in je in yi Zina in samu kuɗi wallahi gwara da an aje in sata." Mama ta ce "A'a ai ni da ɗan sauran haddata, gaskiya ba zan bari ku yi karuwanci ba, sai dai ɗan shan mintin nan indai za su baku kuɗi to ku yarda, ya kamata fa mu kori Talauci Ƴaƴan nan!!, hmm!! kuna ji har yada mana da magana ake yi??"
Haja tace "To Mama yanzu yadda za a yi ki ƙara nemo mana maganin farin jinin nan mu ci gaba da yi, in ƴan Samarin suka zo sai mu sauya Salo mu dinga kame Zuciyoyinsu." Mama ta washe baki gami da cewa "Yawwa Ƴata ta kaina, ai na san ke kanki yana ja, gobe zan je wajen Malam Manu zan karɓo muku, zan je wajen Yayarku Hasiya na karɓi ko ƴar Dubu biyar ce in tana da su, in ya yi mana aikin a Dubu uku sai in sayo muku Man da ƴar hoda da janbaki na dubu biyun ku dinga shafawa, yanzu sai da kwalliya wallahi".
Sosai hakan ya yi musu daÉ—i suka ci gaba da tattaunawa a kan lamarin.

Aliyu, Bhaba, suna zaune a Office ɗin Bhaba suna tattaunawa Aliyu ya ce "Bhaba ni fa aiki nake so." da ɗan mamaki ya ce "Aiki dai? wane iri kenan bayan wanda kake da shi?" "Garage ɗin Abdussalamu me yi mana gyaran Mota za ka kaini, zan fara aikin gyaran Mota." ɗagowa Bhaba ya yi daga kallon Takardun hannunsa ya zubawa Roshan idanu yana nazartarsa, "Meye dalili? so kake ka jawo min zagi ne??" girgiza kai ya yi gami da cewa "Naa Bhaba!, duk me hankali ba zai zage ka ba sai dai ya jinjina maka, za a ga cewar duk kuɗinka bai sa ka lalata Ƴaƴanka ba, ni fa a tsarina Bhaba ina so na san zafi da daɗin kowace irin Rayuwa, na fi so ko me zan yi in yi shi da jikina ba wai in dinga shiga rigarku ba Bhaba!; amma dai gaskiya ina da dalilin koyon gyaran Mota a wannan lokacin." jinjina kai ya yi gami da cewa "To in ji dalilin!" ƙasa ya yi da kai tare da sassauta murya "Bhaba... am... gaskiya na kamu da tsananin son wata Baiwar Allah ne, don ita nake so na koyi gyaran Mota". ya faɗa yana tsirawa Bhaba idanunsa da suka kawo ruwa kamar da an ce ar!! zai fashe da kuka.
"Ikon Allah, wacece ita? Æ´ar waye??" Bhaba ya jera masa rubdugun tambayoyin cike da mamaki.
Girgiza kai ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Bhaba na san kuna son Farin Cikina kuma kuna yi min komai, Ina tsanin sonta, kar wani abu gareta ya sa ku yi ƙoƙarin nesanta ni da ita!" Numfashi Bhaba ya sauke kafin yace "Duk na ji wannan Aliyu, amsata ita nake buƙata!" "Na san masu kuɗi su ake kira Wasu, wane, wance!; Ita ɗin ba kowa ba ce, kuma ba ƴar kowa ba ce, iyayenta Talakawa ne ita ma haka, sai dai tana da son kuɗi kuma ba ta son Talaka kwata-kwata, tana da son ƙarya sannan ta sa a ranta ba za ta Auri Talaka ba; Sabida halinta na raina Mutane ne ya sa da ta dubeni don ta ga Yadi a jikina ba ta san adadin Kuɗin da aka sa aka saye shi ba, ta yi zaton ni Talaka ne shi yasa take yi min kallon ƙasƙanci, ni kuma ina son Aurenta a matsayin Talaka, ina son sauya tunaninta na gyara mata rayuwa, bugu da ƙari kuma ina so ta so ni ne, ba Kuɗina nake so ta so ba, kuma ta so ni domin Allah ba don ƙyale-ƙyalen Duniya ba, shi ya sa na yanke wannan hukunci; don Allah Bhaba kar ka ce min a'a ka daure ka Amince da ita ka so ta tamkar yadda kake Sona. hawayen da suka fara tsere a kan Kumatunsa ne suka dakatar da maganar ta shi ba don ya kai ƙarshe ba...
Bhaba ya murmusa kafin ya ce "Lallai yau na ga yadda Kiyashi yake yin Nasara a kan Zaki; Aliyuna ne ya saka ni gaba yana yi min kuka akan Mace??" goge hawayen ya fara yi, murmushi ya suɓuce masa, cikin sassanyar muryarsa ya ce "Bhaba Zuciyata tana yin rauni a duk lokacin da na tuna halin da nake ciki; su ɗin Ƴan Gargajiya ne suna da tsauri sannan ka san ba sa shakkar Cin Mutuncin Mutum, sun ɗauka son ƙarya nake yi mata ba na gaske ba, ba su san cewa zan iya komai dominta ba, ina da babban aiki a gabana Bhaba!!."
"Tunaninka me kyau ne don haka ba zan daƙile ka ba, duk wanda ya ga wani a cikin wani hali kuma ya yi silar shiryuwarsa Lada yake samu; Allah ya ida nufinka na Alkairi Jarumina!; Zan yi magana da Abdussalamun" Bhaba ya faɗa yana murmushi, sosai abinda Aliyu ya yi da kuma wanda yake shirin aikatawa ya yi masa daɗi, yana matuƙar farin ciki a duk lokacin da ya yi duba ko ya tuna irin kyakkyawar Zuciyar ɗan nasa.
Godiya Roshan ya shiga zubo masa, Bhaba yana shirin yin magana suka ji an banko ƙofar Office ɗin da ƙarfi.

Kansa tsaye ya shigo har kan Bhaban sannan ya tsaya yana bin Aliyu da wani banzan kallo.
Kawar da kai Roshan ya yi gami da cewa ''Ya haka Haydar? me yasa zaka shigo ko sallama babu kuma ka tsayawa Bhaba a ka?" "Na sa da kai ne???" ya faɗa a masife, banza Roshan ya yi masa, ƙwafa ya yi tare da kallon Bhaba yana cewa "Dad ni kuɗi nake buƙata!" rai a ɓace Bhaba ya ce "Sai ka bugeni ka ɗiba Haydar!!" Masifa ya fara yi "Ni fa ba na son irin wannan rayuwar Daddy!, haba don Allah, ka na da kuɗin nan amma ka bar ni ina yawo da tsiya, komai naka na wannan Ɗan iskan da wannan Shegiyar Yarinyar ne, ni ka manta da ni baka ɗaukeni a matsayin komai ba."
Cike da damuwa Aliyu ya ce "Haba Haydar! wai ka manta da Mahaifinka kake magana?, kana faɗen baƙaƙen maganganu kana ɗaga murya kamar za ka dokeshi, bai dace ba irin haka." ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka, yana matuƙar jin baƙin cikin irin munanan halayen Ɗan Uwan nasa.
Ƙara hayayyaƙowa Haydar ya yi yana cewa "Don Uwarka ina ruwanka?? Daddy ka shiga tsakanina da Yaron nan ka ce masa kar ya ƙara yi min magana ko da shi nake bare in ba da shi nake yi ba!!".

Bhaba ya cire hularsa ya ajiye a gefe sannan ya ce "Haydar!! ba zan taɓa dakatar da shi akan gaya maka gaskiya ba, watan wata rana in da rabonka sai ka gane ka shiryu ta dalilinsa, Kuɗin kuma ba zan bayar ba; na yi maka sittira na baka ci na baka sha, ina kula da kai ina kula da lafiyarka, duk wani haƙƙinka da ya rataya a wuyana ina saukewa, to na sallame ka, babu guminka a cikin Dukiyata, kuma ba ka yi aikin komai ba, don haka ba za ka samu ko Sisi nawa ba musamman a yanzu da ba ka bini ta maslaha ba; kuma in ka taɓa abuna ba tare da sanina ba kai ma ka san Sata ka yi, daidai kake da kowane Ɓarawo ka gane???, idan har kana da Zuciya ka tashi tsaye ka san zafin nema; Shashasha mara hankali!!!" yana kaiwa nan ya miƙe ya yi hanyar fita fuu!!!.
Da sauri Aliyu ya miƙe yana kiransa amma ya yi masa banza, rai a ɓace ya ce "Ka ga irinta ko?? wai me yasa ba za ka gane ba Haydar? ka san nauyin Zunubin ɓatawa Iyaye rai kuwa??" "Wallahi sai na sabauta ka yanzu a wurin nan!, Ɗan iska Munafuki har ni za ka dinga gayawa zancen banzar nan?" "To ka yi haƙuri!" Roshan ya faɗa yana ƙoƙarin ficewa daga Office ɗin.
Chapter 11 · 0% Book details