Sashe 26
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alamu sun gama nuna mata kowa ita yake jira ya ga gudun ruwanta.
Umma Aisha ce ta yi mata jagoranci don ta fi samun ƙwarin gwiwa sai dai duk da hakan ba sauƙi sai ma ƙara burkicewa da ta yi. Ta lura indai ba ta yi abinda suke so ba yau fa ba lallai su bar ta ta yi bacci ba don haka ta yanke hukunci zaɓa ko a mutu ko a yi rai. Akan ta farko ta fara tare da Addu'ar Allah ya sa daga haka shi kenan. Ji ta yi an fara yi mata dariya har ita kanta Matar da take tsugunne a gabanta, dafe kai ta yi ta fashe da wani mugun kuka kamar ta yi karo da Mutuwa har shirin shiɗewa take yi. Umma Aisha ta fara rarrashinta gami da nuna mata hakan fa ba komai ba ne. Mama Aminatu ce ta ƙaraso wajen tana cewa "Ke bar min Ƴa ta huta, yanzu dare ya yi ma sai a raka wa gobe, ta gaji da yawa ta je ta yi bacci."
Umma Aisha ta ce "Allah ya kaimu, ni ma hakan nake shirin cewa".
Hannunta ta kama ta ja ta zuwa wajen da su Roshan suke tsaye, hannunsa ta kama ta damƙa masa na Salma tana cewa "Ga ta nan, maza ka je ka rarrashe ta, gobe in Allah ya kaimu sai a ci gaba". ƙasa ya yi da kai ba tare da ya ce komai ba.
Su kuwa suka yi masa banza suka juya.
Irfan ne ya talle masa ƙeya yana cewa "Ɗan iska da kana jin Kunyar kuma ka tattagi Auren?" kafin ya yi magana Muzaffar ya ce "Amarya gaskiya kin bayar da Mata wallahi, sai ka ce an kawo ki cikin Aljanu?"
Mohseen ya yi magana cikin Hausarsa irin ta Æ´an koyo, "Shi bai sani mu ba". Dariya suka sa har da Aliyu, kallonsa ya yi kafin ya yi magana cikin harshen Hindi "Meraa Patnee ladhki hai, ladhka nahi"
Dariya ya yi yana cewa "Oh Achcha!" Irfan ya ce "Mutum ne da naci wai shi a dole sai ya iya Hausa." duk da Mohsin ba wani gama sanin abinda ya ce ya yi ba ya san da shi yake don haka ya zuba masa harara.
Aliyu dai jan hannun Salma wadda ke ta famar ɓurari ya yi yana cewa "Tumhaarie raat achchee beete". "Roshan Bhae!!" Saima ta ƙwala masa kira, tsayawa ya yi kallonta ba tare da ya amsa ba, cikin yanayinta na rawar kai ta ce "Aapka patnee bahut sundhar hai". ya murmusa tare da cewa "Danyavaadh" za ta ƙara wani bayanin ya yi saurin yin gaba, ta bi bayansa da harara tana murguɗa baki.
Sai da suka dangana da bedroom sannan ya saki hannunta yana cewa "Matsoraciya kawai, Sai iyayi kamar gaske ashe duk Damisar takarda ce". Cikin shashshekar kuka ta ce "Ai dai ni ba ka ce min za ka kawo ni nan ba, kuma ai ka ce mana kai ba me kuɗi ba ne, Ni dai don Allah kar ka sayar da ni ka ga ni nake temakawa su Umma" ta ƙarasa maganar cike da tausayin kanta.
Tuntsirewa ya yi da dariya sai da ya yi me isarsa sannan ya ce "Ki kwanta ki yi bacci in Allah ya kaimu gobe sai in yi miki bayani".
Gefe ta nema ta zauna ta ci gaba da kukanta don ba ta jin za ta iya yin bacci a wannan Gidan da ba ta da tabbacin na Mutane ne ko na Aljanu.
Har ya watso ruwa ya fito tana nan zaune tana kuka, banza ya yi mata ya yi shirin bacci sannan ya kwanta ba tare da ya ƙara bi ta kanta ba.
Sun É—ebi lokaci a haka ba tare da ta gaji da kukan ba, tashi ya yi ya zauna dafa'an don kuwa ta hana shi rintse ido ma bare ya yi baccin, "Ki yi min shiru don Allah, in ba za ki iya yin baccin ba ki bar ni na yi". banza ta yi masa kuma ba alamun za ta dena É—in.
"Kin san Allah na fi ki lalaci, idan na fara nawa kukan ba wanda zai iya rarrashina, gwara ma ki yi min shiru ". "Ni dai ka mayar da ni gida" ta faɗa tana ƙara ɓarke wani sabon kukan.
Zazzafar iska ya furzar kafin ya ce "Ba dai Dangina kike tsoro ba??, ai kuwa indai ba za ki yi min shiru ba zan ɗauke ki na kai musu, kuma kin san Allah ba za ki ƙara ganina ba ma".
Cikin sauri ta fara ƙoƙarin haɗiye kukan sabida jin abinda ya faɗa, da so samu ne ma kar idonta ya ƙara gane mata su bare har ya je ya jefar da ita a wajensu, gashi da alamu zai iya aikatawa ba tare da ya tausaya mata ba.
Tini ta gimtse kukan ta kama kanta ta haÉ—e tsokar jikinta, sai rarraba idanu take yi tana sauke ajiyar Zuciya.
"Na gode Allah" ya faɗa a cikin ransa, ƙara haɗe fuska ya yi murtuk! ya dubeta ba alamun wasa ya ce "Taso ki kwanta!'' sum-sum ta tashi ba tare da musu ba, a gefen gadon ta raɓe ta kwanta gami da takure jikinta tsam!!.
"O'o !! Allah buwayi gagara misali!" ya faɗa tare da riƙe haɓa cike da mamakinta, inda bai sani ba tsaf zai rantse ba daga Gidan su Leelah ta fito ba don ɗabi'unta da yawa sun bambanta da nasu.
Zamewa ya yi ya kwanta yana bin bayanta da ido Zuciyarsa cike da saƙe-saƙe kala daban-daban.
Dukkansu ba su san lokacin da bacci ya yi awon gaba da su ba.
Kiran Sallah da ake yi ne ya sa ta farka, tana buɗe idonta ta ganta a wani baƙon wuri gabanta ya yanke ya faɗi, a take abubuwan da suka faru suka shiga fawo mata, "Subhanallah" ta faɗa tana ƙara wararo idanu, "Ni kuwa yau wane irin bacci na yi haka ban san inda kaina yake ba?" ta jefawa kanta tambayar cike da mamaki. Tashi ta yi ta zauna tana tuna ashe fa wai ba ita kaɗai ce a ɗakin ba, dube-dube ta fara yi amma fayau ba kowa, mamaki ne ya ƙara kama ta ganinta a tsakiyar Gadon har da wani ƙaton bargo da aka jibga mata, takaici ya lulluɓeta kamar ta yi kuka.
Zaman karanta wasiƙar Jakin ɓata lokaci ne don haka ta sauka ta nufi banɗaki.
SHARE FISABILILLAH
*Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira ÆŠari Uku 300 kacalâ˜ºï¸ TuntuÉ“i Lambar Waya👉🽠09079885632*
*©ï¸INDO*[12/7, 8:51 PM] INDO: *🪻HAÆŠIYAR GATARI🪻*
17
©ï¸
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*
FREE PAGE...........
Tinda ta idar da Sallah ta yi Addu'o'i ta koma ta kwanta bata ƙara sanin inda kanta yake ba har sai ƙarfe goma na safe.
Da ƙyar ta iya tashi, gabaki ɗaya jikinta duk ya mutu.
Ta zo sauka daga kan gadon ta ci karo da kaya, ɗauka ta yi ta fara warwarewa, Atamfa ce me matuƙar tsada ɗinkin riga da zani, rigar ta sha kwalliya kuma ta tsaya tsam!, sai mayafinta da takalmi. Ture su ta yi gefe ta nufi toilet Zuciyarta cike da tambayoyi.
Leelah sai bayan ta fitar da ran za ta ga Haydar sai gashi kwatsam, lokacin har ta yi nisa a bacci. Sosai ta yi farin ciki da ganinsa ko ba komai ya goge duk wani zarginsa da Zuciyarta ta fara yi.
Da yake gwani ne a Gado cikin sauƙi ya samu kanta tare da siye duk ilahirin Zuciyarta, sai yau ta ƙara jin wani mugun sahihin sonsa ya kamata. Kwana suka yi suna karkashe love har gaf da asbahi sannan suka samu rintsawa. Da yake dukkansu ba damuwa suka yi da Sallah a kan lokaci ba ba wanda ya farka har garin Allah ya waye.
Tinda Haydar ya ɗaskwara wanka ya fice daga Gidan ba ta ƙara jin Ɗuriyarsa ba, ita kaɗai take ta zazzare ido sai Ƴan Aiki da suke temaka mata.
Tin Safiyar Momi ke ta famar kiranta tana shaida mata su wance da wance ma za su zo, su Sumayya ma sun kira ta ya fi gaban a ƙirga. Tin tana ɗoki har suka fara bata haushi don ta lura gayya za su yo mata irin ta jiya, da masu aji da marasa aji kowa zuwa zai yi, ita kuwa hakan zubar mata da Mutunci ne a idon Dangin Miji, a cewarta.
Zama ta yi dirshan tana tunanin irin Wankan kece rainin da za ta yi don ta nunawa kowa ta wuce tsara, wani dakakken Less baƙi me adon fulawoyi Orange ɗinkin doguwar riga Bubu an yi masa adon beads work tin daga sama har ƙasa, shi kaɗai hankalinta ya fi kwanciya da shi don haka ta ɗauka ta mafa ta cokara ɗaurin ture ka ga tsiya ta koma ta ƙyafe kan Sofa tana danna tafkekiyar wayarta.
Ba ta daɗe da gama shiryawa ba Aliyu ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, ƙasa-ƙasa ta amsa tare da yin ƙasa da kai.
sanye yake da shadda Fara ƙal! ɗinkin kayan ciki da babbar riga wadda ta sha aiki Aska Tara, ya ɗora hula Miyaram, sai zuba ƙamshi yake yi. A kusa da ita ya zauna yana ƙare mata kallo, "Kin yi kyau fa sosai Salamaath!" ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi, ɗan kallonsa ta yi ta mayar da kai ƙasa gami da cewa "Ina kwana!" "Lafiya lau, ina kwana!" ya faɗa cikin sigar zolaya, turo baki kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Shiru ne ya ɗan ratsa tsakani kafin Aliyu ya ce "Sai kika gan ki a baƙon wuri ko?" gyaɗa kai ta yi alamar "E" ya ci gaba da cewa "Nan shi ne Gidanmu, waɗanda kika gani kuma Dangina ne na India da kuma na Nigeria, sai kuma Abokan Kasuwancin Iyayena da suka halacci Bikinmu, dukkansu ba bare ba ne; Maganar gaskiya ni ne Aliyu Almustafa Naira, wasu kuma suna kirana Aliyu Me Sanyi". cikin mamaki ta waro ido tana kallonsa cike da son ƙarin bayani, "To idan kai ne Aliyu Almustafa Naira shi kuma wanda ya Auri Ƙanwata fa??, kuma me ya sa ba ka faɗa mana tin farko ba?, me yasa kuma ka aureni bayan Laila kake so?"