← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 35

Sashe 6

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*©️INDO*
[11/19, 10:03 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
5

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*GORGEOUS WRITER'S FORUM*

FREE PAGE...........

Ba ta zame ko'ina ba sai kansa, sai da ta jita a jikinsa sannan ta rushe da wani mugun kuka tana faɗin "Wallahi! wallahi!! wallahi!!" iya abinda take faɗe tana ƙarawa kenan, shi dai ya yi shiru yana sauraren Zuciyarsa wadda take rawar Ƴan bori.
Cikin tashin hankali Irfan ya ƙaraso wajen ya durƙusa kan gwiwoyinsa, "Don Allah Kushi ki faɗa mana me yake faruwa?, wallahi Kukan nan naki yana cutar da Zuciyata gani nake kamar laifina ne." murmushin ƙarfin hali Aliyu ya yi gami da cewa "Shiru za ka yi mata Irfan!, indai tana rantse-rantsen nan ba ta iya magana har sai ta gama, haka take tin tana yarinya ko ita ta ɓatawa kanta rai a kaina take juye fushinta". Zamewa ya yi ya zauna dafa'an, kamar zai fashe da kuka ya ce "Ni wallahi duk a tsorace nake, tayuwu akan abinda ya faru jiya ne, kuma laifina ne, daga yanzu ni dai ba zan ƙara haɗa taro ba ko Aurena za a yi gwara kar kowa ya zo." dariya ce ta suɓucewa Roshan, ganin yadda Abokin nasa ya susuce lokaci ɗaya.

Ƙarar wayarsa ce ta dawo da shi daga Duniyar tunanin da ya faɗa, bai yi niyar ɗauka ba sai da Roshan ya yi magana sannan ya ɗauka ba tar da ya duba kowaye ba.
Shiru ne ya fara karakaina a tsakaninsu kowa da tunanin da yake yi, shi hankalinsa sam ba a kan me kiran yake ba, ita kuwa nauyinsa ne yake neman hanata magana.

Sumayya ce ta danƙara mata hararar gargaɗi, numfashi ta ja ta sauke a hankali sannan ta ce "Assalamu alaikum!" amsawa ya yi a taƙaice gami da tambayar da wa yake magana, "Lallai ma Yaron nan, ashe bai yi ma save no ɗina ba" ta faɗa a cikin ranta, dannewa ta yi ta ci gaba da cewa "Leelah ce, jiya ai da na zo birth ɗinka ban samu mun yi sallama ba na tafi." "Ayya!! ina me baki haƙuri fa, wallahi na yi busy da yawa ne shi ya sa" murmushi me sauti ta yi tana cewa "A'a ba komai wallahi, ai dama taro ya gaji haka, kira na yi dama in yi maka ya gajiya."
yadda take wani kashe masa murya tana lanƙwashewa ba ƙaramin takaici da baƙin ciki ta ba shi ba, ba yabo ba fallasa ya ce "Okay na gode, yanzu ina da uzuri ki yi haƙuri, a huta lafiya". katse wayar ya yi yana dokawa Roshan da yake ta aikin hurawa Kushi iska a kunnenta harara, "Ai duk kai ne ka jawo min, a bar ni da abinda yake damuna ba za a iya ba, wai ya gajiya ta kira ta yi min kamar na sa ta" "Ita wa kenan??" a hasale Irfan ya ce "Waccan me kama da ɗanyar awarar mana !, sai ka ma tsaya tambayata?"
Dariya Roshan ya yi yana cewa '' Allah ka dena cin fuskarta a gabana, in ba haka ba babu Kotun da za ta iya rabamu da kai." taɓe baki ya yi yana shirin yin magana Kushi ta katse shi ta hanyar fara tata maganar "Sai na gayawa Abbi ya yi min tsakani da ita wallahi!" "Wacece??" Roshan ya tambaya yana tsirawa fuskarta ido. Labarin abinda ya faru tsakaninta da Mammi ta bashi tana yi tana kuka tare da shan Alwashih indai ta haɗu da Azaan sai ta ɓaɓɓalla shi.

Cikin mugun ɓacin rai ta yi wurgi da wayar zuwa gefe, "Na lura Irfan ɗin nan mugun ɗan yarfi da wulaƙanci ne, kuma zan yi maganinsa."
Ta faÉ—a tana huci.
Rabi'a Da Haja suka yi shewa har da rangaɗa buɗa, abin haushi ya ƙara bata amma sai ta yi musu banza don ba ta shirya Tijara ba.
"Nawa yake da zai ce zai ja da ke ƙanwata! kwantar da hankalinki, ai tinda Allah ya haɗa mana komai ban ga ɗan iskan da zai gagaremu ba, ki bar damuwa a kansa"
Sumayya ta faɗa cike da son ƙwararawa Leelah gwiwa, kuma ta ji daɗin hakan sosai.
Hira suka ci gaba da yi tare da cin buri akan duk lokacin da ya shigo hannunsu ba zai ga da kyau ba.

"A rayuwar nan in an san farkon rigima ba a san ƙarshenta ba Kushi, ki yi haƙuri don Allah, ko Bhaba ba na so ya ji abinda ke faruwa bare Maa, bare kuma har ki ɗaukaka ƙara zuwa gaban Abbi, kin san ba ƙaramar Wuta za ki tasa ba in kika yi haka; kar wata barazana tata ta dameki don ta faɗa ba lallai ya faru ba, Ki ci gaba da Addu'a Allah zai yi mana tsari da sharrinta."
"Kenan ƙyaleta zan yi ta dinga raina min hankali?" "Mammi fa Ba sa'ar yinki ba ce, haƙuri da ita shi ne mafi Alkairi ko a wurin Allah sabida ita ɗin Uwa ce, in kina so Allah ya so ki to fa karki muzgunawa Makusantanki musamman Manya; ko da a hanya kika haɗu da Mutum Allah ya yi mana wasiyya akan kar mu ɓata masa rai, ki yi haƙuri ki manta da zancen mu bar shi iya mu don kar mu ƙara dawo da bara sabuwa, kin san Faɗan Umma ba ya Mutuwa." "To na ƙyaleta sabida kai, amma indai suka ƙara ba zan haƙura ba!" ta faɗa tana sauke nannauyar ajiyar Zuciya. murmusawa ya yi yana cewa "Na gode da kika haƙura sabida ni ɗin, kuma nan gaba ma ina so ki ƙara haƙurin sabida ni da kuma gujewa ɓacin ran Iyayenmu; yanzu dai in Umma ta dawo in ta tambayeki akan wani abu ki gaya mata na haɗu da wadda nake so kuma zan Aureta". Da sauri ta ɗago tana kallonsa gami da cewa "Kohne vah?!" "Sauka ƙasa Irfan ya baki labari shi ya fi ni saninta". kafin ya rufe baki tuni ta zame ta zauna a ƙasa tana fuskantar Irfan wanda ya zauna dirshen yana aikin kallonta.
"Ka ji abinda ya ce?" ta tambaya tana tsare shi da idanunta da suka kukkumbura fulu-fulu. ƙasa ya yi da idanunsa wanda ya kasa yi musu shamaki da kallonta, mamakin yadda ta murmure kamar ba ita ce me kuka yanzu ba ya cika masa Zuciya.
Murmushin ƙarfi da yaji ya ƙwaƙulo tare da cewa "Wai har kin gama kukan? na ga kamar ba ki yi ba don dai idanunki sun nuna!". "To ina ruwanka ni dai ka ba ni labari". Roshan ya ce "Haka take, gwara da Allah ya sa ka gani da idonka, ko wuni ta yi tana kuka da zarar ta gama haka za ka ganta kamar ba ta yi ba." "To fa!! salon naki ya burgeni, da alamu kina da saurin hucewa." dariya Roshan ya yi tare da miƙewa yana cewa "Kai dai ba ta labari kawai, akan Mita wannan da kake gani ta cancanta zama Sarauniya, ni duk ta sagar min da ƙafafu wallahi!" Irfan ya ce "Allah ya ƙara!, kin ga Kushi wata Me kama da Ƙosan yamma ya gani ya kamu da sonta, kuma gaskiya ba ajinsa ba ce don dai ba yadda za mu yi da shi, da alama mugun kamu ta yi masa Mayyar!" Zaro ido ta yi tana cewa "Mayya wadda aka ce suna cinye Mutane??"
"A'a! da wasa nake yi, Mutum ce kamar kowa, kuma da alamunta tana da hankali sai dai akwaita da son abin Duniya."
"To in kuÉ—i take so ai Muna da su, yaushe za mu je mu ganota?"
"Tambayeshi, kai Malam yaushe za mu je? ko in kirata in ce za ku yi magana?" duk suka zuba masa ido cike da son jin abinda zai ce "Ni ko na na tashi zuwa ban gayyaci kowa ba, ba na so ta san ko ni waye; kamar yadda ta ɗaukeni a Talaka a haka zan je mata kuma a haka zan bayyana mata soyayyata, ina so ta soni domin Allah ba don Kuɗina ko wani ƙyale-ƙyalen Duniya ba, tin daga yanzu har zuwa bayan mun yi Aure ba na so ta san asalina, kuma idan ta sani kai ne Malam Irfan. "A'a ni!!? ba dai ni ba wallahi!, ni bakina akwai sakata kuma ban iya kwancewa Mutum zani a kasuwa ba. "To idan ta ce ba za ta Auri Talaka ba fa?" Kushi ta faɗa cike da al'ajabin maganar ta shi,,, "Ba ruwanki da wannan, ko me za ta ce zan iya jura. "Ai kuwa to ni zan fara yiwa Maa Albishir, na san Bhaba ma har tukuici zai ba ni." Aliyu bai tanka mata ba sai murmushi da ya yi, Irfan kuwa tunzurata ya ƙara yi suka ci gaba da girmama lamarin.

10:00pm

Leelah, tana kwance ta rungumi É—an yamulmulin Filon Sumayya tana waya da Saurayinta Abbas.
Nuna masa take yi tamkar in ba shi ba ba ta ga wani Namiji a Duniya ba, shi kuwa sai fasa kai yake yi yana jin daÉ—i tare da burin wata rana a ÆŠaura musu Aure.
A cikin ranta kuwa haushinsa take ji don yau a haka ta wuni tana jin haushin kowa sabida rashin Mutuncin da Irfan ya yi mata.
Ƙarya ta zunduma masa akan kanta yana ciwo za ta yi bacci, duk ya tashi hankalinsa haka nan ta wangarar da shi ta katse wayar.
Da sauri ta miƙe zaune ganin sabuwar lamba ce take ta famar kiranta, a tunaninta Habib ne shi yasa ba ta bi ta kansa ba ta ci gaba da magana da Abbas.
Chapter 6 · 0% Book details