Sashe 4
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hasale Leelah ta ce "Kai ka san na fi ƙarfin Manka wallahi!!, kuma ka sani ni ban tsotsi Sata ba sai ka je ka nemi ɓarawo!!!." wata shegiyar harara Rabi'a ta doka mata gami da cewa ''To wa kike son cewa ɓarawon??" Leelah ta yarfa hannu tana cewa "Oho!! ba da kowa nake ba amma duk wanda ya tsargu ya shiga layi!!."
Rabi'a za ta yi magana Salim ya katseta da cewa "Kun ga!! ba cecekuce na ce ko zo ku yi ba, a faka a fito mini da Mai wallahi ko kuma a ga yadda ake tsintsinar rashin Albarka a gidan nan." Salama ta zuba shewa gami da tafa hannuwa kafin ta ce "Ina bayanka daram! ni na ɗaure maka abin wallahi, Manka bai fi kwana uku ba sabida haka a fito da shi ko mu yiwa Mutum Alƙunut; don an ga muna da haƙuri sai a dinga takamu yadda rai ke so!!" Salim ya watsa hannu yana cewa "Gane min hanya fa!! ai haƙuri riga ce rashinsa ma haka, yau dai Rigar haƙurin na jingineta a gefe, ban ƙi a casu ba wallahi; daɗina da ke akwai faɗar gaskiya Me Wanki da Guga, ai wallahi da duk Matan Duniya irinki ne da ba a yi Yaƙi ba tin asali."
Sumayya ce ta doka tsaki ta koma É—aki tana cewa "Ai tinda ba ni na É—auka ba ban ga dalilin zamana a wurin ba tinda ba haifata ka yi ba."
Rabi'a ma tsakin ta yi sannan ta shige É—aki.
"Kan Doron Masifa!!!!? wato ina magana ma kuna kakkaɓe jiki kuna shigewa ɗaki??!!!, yadda kuke ji da rashin Mutunci fa ni ma haka nake ji da nawa, wallahi Ƙudrat daidai nake da Ƙugun kowace Ƴa a gidan nan!!!!" ya ƙarasa magana yana tafi gami da jijjiga jikinsa alamar a shirye yake.
Rabi'a ce ta fito ta cillo masa Man tana cewa "Gashi nan jarababbe Ɗan kalan talauci, daga an ɗan ari abinka sai bala'i da masifa ai ni na fi ƙarfin ɗan man nan naka bare in sata, banza kawai!" a fusace take maganar sai ka ce ta fishi gaskiya.
Shewa Salama da Salim suka sa suka tafa kafin Salim ya ce "Heeee!!!! ni Furangaɗi Ni Gallo!!!! Amma dai an faɗi ba nauyi, jeki mun ji, ni ne ƙarfamfana Ɗauɗar Aljihu ƙarewar Talauci, amma hakan bai sa na iya bizi ba."
hararar sama da ƙasa ta zuba masa kafin ta buga wani dogon tsaki ta faɗa ɗaki cike da baƙin ciki da takaici.
Juyawa ya yi kan Salma gami da cewa "Allah dai ya biyaki Uwar masu miƙa wuya, Barbela me Fari daga Allah!!, ke dai Allah ya hutashsheki shafe-shafe bare Talauci ya sa ki yi sata."
Kafin Salma ta yi magana Mama ta fito daga É—an É—akinta tana kakkaÉ“e zanin Æ™ugunta gami da gyara masa É—auri, "Wallahi ahir É—inka Salim!! ka fita shirgin ƳaÆ´ana tin kafin na yi maka Rashin Mutuncin Æ™are dangi!! da sanyin safiya ka kafa mambari kana kiran Æ´ata Æarauniya uban me ka ajiye da za ta satar maka??"
Taɓe baki ya yi gami da sunkutar Bokitinsa yana cewa "Kowa dai ya gani ita ta fito da abin, Anty Salma kin ga tafiyata tinda Manya sun fara shiga lamarin, sa'a ma aka ci wannan me baki duk Goron ba ta fito ba." Salma ta yi ƙasa da kai ba tare da ta ce komai ba sabida nauyin Mama da take ji, duk fitsararta ba ta son yi a gaban Iyaye.
"Uban me ka ce Salim???!! zan sa Isuhu ya yi maka bugun gangar jajiberi wallahi!" Mama ta faɗa a masife, "A'ahh!! me ya yi zafi ido zai ci wuta?! kwantar da hankalinki kamar kin yi baƙo ya mutu, cewa na yi Allah ya bawa Anty Rabi'a gida da Mota mu dinga kwasar arziki, ai abunta tamkar namu yake."
Washe baki ta yi tana cewa "To ko kai fa! daɗina da kai ai akwai sauƙin kai, Allah ya amsa zazzaƙan harshen nan naka Salim na Salima!!, ai za a ci Uwar sabada lokacin."
Dariya me haÉ—e da shewa ya saka ba tare da ya yi magana ba ya ci gaba da tafiya yana kakkaryewa tamkar Zabiyar Mata.
Salma ma da sauri ta gudu É—akinsu tana dariya ciki-ciki.
*PAID BOOK, 300 ONLY 09079885632*
*©ï¸INDO*[11/19, 10:03 AM] INDO: *🪻HAÆŠIYAR GATARI🪻*
4
©ï¸
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*
FREE PAGE...........
Dukkansu alla-alla suke gari ya waye su fece daga gidan don za su fi samun damar sararawa. Tare suka fita Bayan sun dire Kushi a Makarantar da take karatu suka wuce da Roshan Kamfanin Bhaba wanda yake ƙarƙashin kulawarsa kasancewar Bhaban ba ya Ƙasar.
Tana zaune a Garden hannunta riƙe da chocolate tana ci. Jefi-jefi takan tankawa Suhailat dake famar zuba mata surutu akan abinda ke damunta.
Suhailat tana É—agowa idonta ya sauka akan Mammi wadda ke tsaye a kansu tana binsu da wani shu'umin kallo, sai da gabanta ya yanke ya faÉ—i, har ga Allah ta É—an tsorata amma sai ta maze ta ce "Mama lafiya kuwa??" jin ta faÉ—i haka ya sa Kushi ta É—ago don ganin da wa take maganar, haÉ—a ido suka yi Kushi ta yi saurin É—auke nata gami da doka tsaki ta gutsiri cakuletinta.
Murmushi ta saki kafin ta yi magana a gadarance "Wurin Kushi na zo ki gaya mata ina magana." Suhailat ta zunguri Kushi tana cewa "Kin ji, ana yi miki magana." "Waye??" ta tambaya kamar ba ta san da kowa a wajen ba, "Wai ba kina kallo ba? ki kula mana ke ta zo nema fa!" "Ke ni fa ban ga Mutum É—in da zan kula a nan ba, ko dai kin fara gane-gane ne??" Suhailat ta dafe goshi tana cewa "Oh my God!" ta gane sarai Kushi tana sane take raina musu hankali daga ita har Matar.
Abin ya yiwa Mammi ciwo amma sai ta maze ta ƙara faɗaɗa fara'arta ta ce "Ba ki ganeni ba ne Kushi??, ni Uwarki ce fa, ko ba a gaya miki hakan ba ne???" Wani shegen kallo ta bita da shi kafin ta saki murmushin rainin hankali, miƙewa ta yi ta matso kusa da ita suna fuskantar juna duk da cewar Mammi ta fita tsayi, cikin ƙarfin hali gami da tsaurin ido ta ce "Sa idonki cikin nawa!!!!, ko da wasa karki ƙara kiran kanki da Uwa a wurina, ba ki haifeni ba wannan Ɗan Iskan Azaan ɗin kika haifa, kuma har Abada ko a mafarki ba za ki taɓa taka matsayin Uwa a wurina ba!! ina fatan kin fahimta!" ta ƙarasa maganar tana huci kamar za ta hau kanta da duka.
Ido Mammi ta tsira mata Zuciyarta na cika tana tumbatsa tana fusata, "Hmm!! Ke yarinya ce ba ki san komai a Duniya ba, tinda ba zan taka matsayin Uwarki ba zan taka matsayin Uwar Mijinki!!!, kin ga ko ba kya so na zama Uwarki, kuma za ki san kin yi kuskuren cin Mutuncina da kuma Marin ÆŠana!!, akwai ranar da Azaan zai mallakeki ki sa wannan a ranki." cikin tsawa Kushi ta ce "Ba dai ni ba!!! ba ki isa ba da ke da shi!!!"
shu'umin Murmushin nata ta yi kafin ta yi taku uku ƙwarara cikin yanayinta na jin kai da izza, "Kamar yadda Uwarku take yin komai kuma take mallaka muku komai don ta faranta muku ni ma haka nake yin komai domin nawa Ɗan, zan mallaka masa ke ko ta wane hali; ko da babu Aure yake sonki zan mallaka masa ke a matsayin Ƙwarƙwara!!!!!"
Ji take kamar ta fashe da ihu amma a nan ihun ba zai fishsheta ba don babu me rarrashinta, makarin kukanta kuwa bai Wuce Aliyu ba. Jikinta har karkarwa yake yi sabida ɓacin rai, ina ma za ta iya da ta tarwatsewa Matar nan kai ta huta da wannan baƙin cikin, a kausashe ta ce "Tinda kin san tana yi mana komai ai kuwa ki kuka da lokacin da za ta kamaki a bisa laifin takura mana, kuma wallahi sai kin yi baƙar nadama a Rayuwarki, mara Ƴanci Korarriya!!!!" tana gama faɗe ta yi gaba fuuu kamar za ta tashi sama, Zaratan Mazan da suke takewa Mammi baya ne suka sha gabanta dole ta fasa tafiyar ta tsaya tana binsu da wani shegen kallo, a ranta tana ji dama da Wuta a kusa ta watsa musu ko ranta zai yi haske.
Murmushi me sauti Mammi ta yi kafin ta ce "Duk inda ta shiga ta fito ita ɗin jinin Murtala Mai Zafi ce!! Yanayinta ne ya nuna hakan!, zafin kanta da tsaurin hali da kuma Tsageranci sak! Uwarta, sai na ji ta ƙara burgeni Matuƙa!!, Ina da burika da yawa a kanki, kuma zan cikasu ba tare da na sha wahala ba; ku barta ta tafi!!"
Suna buÉ—a mata hanya ta ci gaba da tafiya, da sauri Suhailat ta bi bayanta don ta lura ta gama sabaucewa za ta iya zuwa ta yi wani wurin.
Mammi ma jan tawagarta ta yi suka É—aware Zuciyarta cike taf da mugun Alwashi akan Kushi.
Hannunta Suhailat ta riƙe tana cewa "Ina za ki je ne Kushi??, ki nutsu don Allah ta tafi fa!!, kuma yanzu lokacin fitarmu daga School bai yi ba"
Da kyar ta fizgo muryarta da ta fara dashewa sabida tsabar fusata ta ce "Ki kaini wajen Roshan!!" "Haba Kushi! me ya yi zafi haka?? ni ina na san ma inda Roshan É—in yake??" "In ba za ki kaini ba ba ni mukullin Motarki!"
Suhailat za ta yi magana Qadri ya ƙaraso wajen yana tambayar abinda yake faruwa.
"Kaini wajen Roshan!" ta faÉ—a tareda nufar inda ya ajiye Mota.
Ganinta a burkice ya sa shi bin bayanta ba musu ya shiga aiwatar da abinda ta ce.
A zaune kawai yake amma ya kasa yin komai, tunane-tunane sun yi masa yawa, Yarinyar da ya kwana mafarkinta ita kawai yake muradin gani, gashi bai san inda zai fara nufa ba.
Ya daɗe cikin tsaka me wuya kafin ya tuno Irfan zai iya saninta. Da sauri ya turawa Irfan kira cikin ƙaguwa.