Sashe 27
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tiryan-tiryan ya bata labari tin daga haɗuwarsu da Leelah har burin da yake son cimmawa a kanta, bai tsaya iya nan ba sai da ya sanar mata asalin gaskiyar Aurensu me wa'adi ne, da zarar Haydar ya rabu da Leelah zai sake ta ya Auri Leelan. Hakan daɗi ya yi mata sosai don kuwa gani take kamar ta ci Amanar Leelah ne da ta Auri wanda yake sonta, bayan haka kuma sam Aliyun bai yi mata ba, ta tabbatar ta girme shi ko da ƴan watanni ne, a ganinta kamar faɗuwa ce ta Auri ƙaninta, da ta ji za su rabu kuwa sai ta yi murna tuni ta saki ranta ta dena jeranta shi da Mijinta har da cewa ya dinga kiranta Aunty.
"Af! na manta fa ba ki ci komai ba, ke kuma ba ki yi magana ba, ki tashi mu je ki karya". noƙe kafaɗa ta yi gami da cewa "A'a" "Okay bari na sa a kawo miki" shiru ta yi masa ta ci gaba da zazzare ido tana sa ran t ɗa ga ya tashi, shi kuwa ko niyya bai yi ba sai ma danne-dannen waya da yake yi.
Zaman kurame suka ci gaba da yi har shuÉ—ewar É—an lokaci
Ƙwanƙwasa Ƙofa aka yi tare da yin sallama, Salama ta zazzaro ido tana kallon Ƙofar gabanta na faɗuwa, magana kawai ta ji ya yi sai dai ba ta san me ya ce ba sai gani ta yi an buɗe Ƙofar an shigo.
Ƴan Mata ne guda biyu dukkansu suna ɗauke da tray wanda aka cika su da tarkace iri daban-daban, kallonsa ta yi a ranta tana ayyana anya kuwa wannan Aliyun bai haɗa iri da Aljanu ba?.
Bayan sun dire tray ɗin ɗaya a ciki wadda take bahaushiya ta ce "Yallaɓai Maa tana nemanka, Aunty Khushi ce sai kuka take yi ta ƙi cin Abinci." ido ya zubawa Budurwar Zuciyarsa na wani mugun tsalle, da kyar ya daidaita nutsuwarsa ya ce "Shi kenan!" Ɗan rissinawa suka yi kafin su fice cikin sauri.
"Wai da gaske Ƙanwarka ce??" Har ya yunƙura da nufin tashi ya koma ya zauna sabida jin abinda ta faɗa, tsira mata idanu ya yi cikin mamakin jin tambayar ta-ta, "Kenan ba ki yarda da ni ba?". idanunta ne suka ƙara girma ta yi saurin sa hannu ta rufe bakinta, sam ba ta san lokacin da maganar ta fito ba, a cikin ranta take ta jujjuya ta amma sabida ta damu da sani har tana yin suɓul da baka, girgiza kai ta yi a kunyace ta ce "A'a na yarda, gani na yi kai Kalar Hausawa ne". "Oh! ni da Bhaba nake kama ita kuma sai ta kwaso Dangin Umman mu na India, kuma don dai kallon tsoro kika yi mata amma muna kama sosai". gyaɗa kai ta yi ba tare da ta ce komai ba, miƙewa ya yi tare da cewa "Yanzu zan iya tafiya ko akwai wata Tambayar??" girgiza kai ta sake yi, ya ce "Okay" tare da nufar hanyar fita.
Tana kammala Karyawa ta lalubo ƴar wayarta ta shiga Kiran Lambar Umma, sai da ta yi kira huɗu ba amsa sai a na Biyar ɗin Umma ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama, ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta ce "Wallahi duk na shiga damuwa Umma ina ta kira na ji shiru". Umma ta murmusa gami da cewa "Kin san sha'ani Salama Wayar tana cikin tarkace sai da ƙyar ma aka gano ta yanzun".
"Yawwa to, ina kwana" "Lafiya lau, ya kuka kwana?" "Lafiya ƙalau, Am... Umma ina Salim da sauran Mutanen?" "Duk suna nan lafiya" "To wai ba wanda zai zo min ne? " "A'a ai ko kowa bai zo ba su Umman Nabila za su zo tinda ya zame musu dole" washe baki ta yi tana faɗin "Yawwa na ji daɗi, a gaishe min da su". "In sha Allahu" ta faɗa tare da kashe wayar.
Ajiye wayar ta yi a gefe sai washe baki take yi, duk ta É—auka babu wanda za ta gani yau don haka duk ta tashi hankalinta.
Aliyu ne ya yi sallama ta amsa murya Æ™asa-Æ™asa, Æ™arasowa ya yi yana cewa "Kin gama ko?" ta gyaÉ—a kai, "Okay tashi mu je ki Gaisa da Mutane" lokaci guda jikinta ya yi sanyi ta yi tsumu-tsumu tana rarraba ido kamar an jiÆ™a Æera, jin shiru ya sa shi cewa "Kina da matsalar Kunne ne?" Da sauri ta girgiza kai cikin rawar baki ta ce "Amm... dama....dama.... ina son ce maka su Umman Nabila za su zo". "BaÆ™i za ki yi??" ya faÉ—a yana zaro ido, gyaÉ—a kai ta yi tana cewa "Na kira Umma na tambaye ta shine ta ce za su zo".
"Kenan fa dole ki koma inda suka ajiye ki Jiya, kuma gashi nan ma wani Bikin Muke yi, amma bari na tambayi Maa na ji ko za ta yarda a Ɗauke ki" marairaicewa ta yi kamar za ta fashe da kuka ta ce "Don Allah ka mayar da ni can, ina so in ga Ƴan Uwana". ƴar dariya ya yi kafin ya ce "Bayan na iya yau ne za ki gansu? gobe fa ba lallai ba." kasa cewa komai ta yi don ta san ya fi ta gaskiya, ta yi ƙasa da kai tana jiran ƙiris ta kama kuka.
Sai da ya yi zama dafa'an ya rarrasheta sannan ta yarda ta bi shi don ta kwashi Gaisuwa.
Suna kammala Gaisawa ya rakice ta suka koma Gidan Jiya.
Salma murna kamar ta dinga tsalle tana faÉ—uwa ita kaÉ—ai, suna zuwa ta fara aikin share-share da goge-goge kamar wadda aka sakawa batiri.
Shi dai yana daga gefe ya zuba mata ido yana kallon ikon Allah, yadda take ta fara'a ita kaɗai ya yi matuƙar tafiya da hankalinsa, da farko danne-dannen waya yake yi daga baya sai ya mayar da ita abar kallonsa yana yi yana murmusawa.
Sai da ta gama sannan ta dawo ta zauna ko hutawa ba ta yi ba ta ce "Yanzu Girki zan ɗora" dariya abin ya ba shi don haka ya yi kayarsa sannan ya ce "Ba kya gajiya ne?, ki bari za a kawo komai" "Ni dai na fi so in yi da kaina" "Af! kin fi ni gaskiya, ashe fa a nan ba a matsayin Aliyuna nake ba ko?, to yanzu menene me ɗan sauƙi-sauƙi?" "Ni kam ko meye ma zan iya yi" "Oh! ba haka ba, ina nufin menene wanda za a yi ba tare da kowa ya yi tunanin komai ba??" langaɓar da kai ta yi gami da cewa "A yi shinkafa da wake kawai" "Kai! haba dai gwara dai a yi shinkafa da Miya ko?" ya faɗa yana dariya, ɗan murmusawa ta yi ta ce "E" "To akan me za a yi Girkin ko sai an sayo Gas?" girgiza kai ta yi ta ce "A'a Umman Nabila ta sayo min Kurfeto na Alminiyam kawai da shi zan yi, yanzu dai Gawayi za ka sayo kawai, sai Kayan Miya da sauransu". "To, amma lissafa min duk abinda zan sayo kar in yi miki shirme"
dariya ta yi gami da cewa ''Ko a rubuta maka ne?" "Ke! Duk girman kan nan nawa sai na kasa riƙe wasu ƴan tarkace?, faɗa min kawai".
Lissafa masa ta yi sannan ya kama hanya.
Sai da ya sha wuya kafin ya gama sayo komai don duk bai san inda zai dosa ya same su ba sai da ya haÉ—a da tambaya.
Koda ya dawo sai ya yi ruwa ya yi tsaki akan shi zai yi Girkin wutar ma shi zai kunna, tinda ta ga ya nace ta sakar masa ta koma gefe ta zuba masa ababen ganinta.
Waje ya fita ya tarkato ledoji ya jibga akan Gawayin, yana shirin ƙyasta Ashana Salma ta dakatar da shi da cewa "Ba fa haka ake yi ba ka bari in kunna" "Ke na fa fi ki iyawa, tashi ki tafi ɗaki ki kwanta, in ba haka ba hana ni aikina za ki yi."
Ba musu ta tashi ta koma ɗaki ta mimmiƙe, da yake a gajiye take ba wahala kuwa bacci ya yi awon gaba da ita.
Ya yi sa'ar gawayin irin na Ƙiryar nan ne me wuyar kamawa, Ledojin da ya ɗebo sai da suka ƙone tas! wutar ba ta kama ba. Fita ya yi ya ƙara tattaro kan wasu ya zuba ya cinna musu wuta su ma suka ƙone ba labarin kamawa. Haka ya ƙara fita ya lalubo sai da ƙyar ya samu ba yawa sabida duk ya gama kwashe su. su ɗin ma ba sa'a don gawayin baƙi ƙirin da shi sai zafi da ya ɗauka. Kamar zai fashe da kuka ya kuma fita ya tarkato Yayi da Kwalaye, kamar ɗan bolaji shi ne har Wasu layikan, sai da ya tattaro da yawa sannan ya dawo ya zauna ya ci gaba da basu wuta, nan fa tuƙuƙi da hayaƙi da ƙauri suka ce salama alekum. Haka nan ya daddaure yana hawaye yana sharcewa yana tari yana komai ya ci gaba da azalzala Wuta.
https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx
Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi Æ™iba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃ðŸ½ðŸ’ƒðŸ½ðŸ’ƒðŸ½ðŸ˜˜ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace â¤ï¸ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136