← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 35

Sashe 18

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zaune kan É—aya daga cikin Kujeru biyun da suka sa wani É—an Table a tsakiya, hankalinta kwance take shan Ice cream tana yi tana lumshe ido, hankalinta sam ba a kusa yake ba ta yi nisa a Duniyar tunani.
Ta yi matuƙar tsorata jin Azaan a kusa da ita ya kira sunanta cikin wata maraitacciyar murya, ta yi tunanin gizo muryarsa ta fara yi mata, da ta buɗe ido ta gan shi ƙwadagwas a gabanta sai razaninta ya ƙara ninkuwa, "Ba na son ganinka Azaan Ple...." saurin katseta ya yi da cewa "Kar ki fusata, magana nake so mu yi."
miƙewa ta yi a fusace tana cewa "Aap mujhe kya bataane ja rahe hai?!!" ƙara yin ƙasa da murya ya yi ya marairaice kamar zai yi kuka ya ce "Tum baith jao please!" ido ta zuba masa ganin yadda ya zama wani abin tausayi kamar ba shi ba, lokaci guda jikinta ya yi sanyi, komawa ta yi ta zauna har lokacin idanunta na kansa kamar wani kayan gabas.
Ya Lumshe idanunsa gami da haɗiye yawun wahala, a hankali ya buɗe idon gami da ɗorasu akan kyakkyawar fuskarta, ya rasa me zai ce mata, shin wane irin zaɓi zai bi a cikin zaɓukan da Zuciyarsa take ba shi? shin da wane ɓangare zai yarda?, "Azaan! tum...." katse mata maganar ya yi da cewa "Mainne tu...." kasa furtawa ya yi sabida nauyin da kalmar ta yi masa, anya in ya faɗa mata haka kuwa bai cuci kansa ba?, wai me ta yi masa ne a rayuwa da ba shi da burin da ya wuce muzguna mata??, to amma ya zai yi da Umarnin da Mammi ta ba shi??, tunanin da ya faɗa kenan, gabaki ɗaya jikinsa ya ƙara mutuwa, ya rasa wane irin al'ajabi yake ji a tare da ita.

Ido ta zuba masa kawai tana kallon ikon Allah, za ta iya cewa tinda take ganinsa a Duniya ba ta taɓa ganinsa cikin irin wannan yanayin ba, wani sashin na Zuciyarta ya cika da son sanin damuwarsa, wani gefen kuwa wani ɗan guntun tausayinsa ne ya fara yi mata tsiro. Ganin tana shirin faɗawa wata Duniyar ya sa ta miƙe zumbur tana cewa "Na lura ba ka da abin cewa!" cikin wani irin zafin nama ya cafke hannunta gami da kiran sunanta cikin wata susutacciyar murya, cak! ta tsaya ba tare da ta juyo ba sai ma rintse idonta da ta yi da ƙarfi, gabanta ya shiga faɗuwa a jajjere, "Main... tumse bahoot... pyaar karthi hoon Khushi!!!," ya faɗa cikin rawar baki kamar me shirin rushewa da kuka. Bugun Zuciyarta ne ya ƙara tsananta tsoro da razani suka ƙara dirar mata, da sauri ta girgiza kai tana cewa "Naa!, ba zan iya ba!, ban yarda da kai ba Azaan, main tumse pyaar nahi kharta!!!!"
wani irin surfe da sussuka Zuciyarsa take yi, tuni jikinsa ya ɗau karkawa idanunsa sun ciko da ƙwalla, cikin fitar hayyaci ya ce "Sabida me ba kya so na Kushi??! ko dai kina son Roshan ne??" sai a lokacin ta juyo tana zuba masa idanunta da suka burkice, wani shegen kallo ta kora masa wanda ya ƙara juya hantar cikinsa. "Kai fa dama Mahaifinka Kafiri ne Azaan!, kuma kai ma haka, to ko a Addininku haramun ne Yaya ya Auri ƙanwarsa bare kuma mu da muke Musulmi, wannan ashshar ma da kake yi ko a Addinin naku haramun ne; ni ka sakar min hannuna!!"
Sakin hannun nata ya yi ya shiga yamutsa tarin Sumar kansa, wata zazzafar iska ya furzar kafin ya ce "Ni ma Musulmi ne Khushi!! Addinin Mahaifiyata nake bi ba na Bhabana ba". murmushin takaici ta yi gami da cewa "Jhoot batao tum, babu yadda za a yi Musulmi me hankali ya yi abinda kake yi, ita kanta Uwar taka yanzu Kafira ce don babu danshin Muslimci a tare da ita!!" "Me yasa kike min haka don Allah?? ina so ki sani a kanki idanuna sun rufe, na riga na haukace kuma zan iya aikata komai don na samu abinda nake so, kar ki bari mu taka matakin da za mu yi abu mara daɗi Khushi! ki yarda da ni tin kafin Imanina ya ƙarasa gushewa; ni ina sonki ne ba wai ina son cutar da ke ba, kyun Kushi! me yasa ba za ki amince da ni?" Tsaki ta yi kafin ta ce "Jao aur mujhe jagah do!, aur main tumse shaadie nahi karoonga!!"
Ba ta jira abinda zai ce ba ta yi gaba cikin sauri, wajen Mota ta je ta tsaya don jiran Suhailat, baƙin ciki ya haɗe mata goma da ashirin, ga Suhailat ta zo ta shanya ta ga shi kuma ya zo mata da surutan banza, tunaninta ɗaya ma ko waye ya gaya masa ta zo wajen?.

Tinda ya ji Abbi ya kira shi don su yi magana jikinsa ya ƙara yin sanyi salam. Gashi bincike ya tabbatar masa gaskiyar Haydar ne ya je wajen Leelah da zancen Aure. Haka nan yake yawo shi ba me lafiya ba shi ba mara lafiya ba.

Abbi na zaune kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun Kujerun da aka ƙawata Falon hannunsa ɗauke da takardu yana duddubawa. Ba tare da ya ɗago ba ya amsa Sallamar Roshan. Kusa da ƙafafunsa ya ƙarasa ya zauna yana cewa "Abbi ba a rabo da karance-karance". Murmushi kawai Abbi ya yi ba tare da ya ce komai ba, sai da ya kammala sannan ya ɗago yana zame siririn glass ɗin da ke kan idonsa, "Barka da dare Abokina" ya faɗa yana ƙara faɗaɗa murmushinsa, firgigit ya yi gami da cewa "Na'am!!" ganin haka ya sa Abbi ya ce "Tashi zauna kusa da ni." cikin sanyi ya tashi ya koma kan Kujerar ya zauna yana cewa "An gama kenan!" "Eh na gama har ina gaisheka kana ce min na'am" dariya Aliyu ya yi yana cewa "Abbi ka san Duniya sai da nazari, gabaki ɗaya ban san me ka ce ba ne." "Okay, shi kenan, dama na lalubo ka ne akan batun Auren Ɗan uwanka da ya taso." Rass!!!! gabansa ya faɗi, da kyar ya daidaita nutsuwarsa sannan ya ce "Ina saurara Abbi, Allah ya sa dai kai ma ba ƙara Auren za ka yi ba". dariya Abbi ya yi kafin ya ce "Ai in ƙarawa zan yi sai na ji wadda kake so tukunna sai na Aure ta, a wannan lokacin ba Haydar ne ya dace da yin Aure ba kai ne, kana buƙatar me kula da kai har ma da Ƙanwarka, maza faɗa min, wacece Abokiyar tamu?, ina so ne a haɗa Auren naku rana ɗaya da Ɗan Uwanka, ka ga shi jiya ma an je an gama magana, nan da Sati uku in sha Allah zai zama Ango."
Kasa cewa komai Aliyu ya yi, ya zama kamar wanda aka dasa a wajen, yau fa ya ga ranar da ake kira Baƙar Rana!. Jin shirun ya yi yawa ya sa Abbi yin gyara murya gami da saɓule Tabarau ɗin nasa duka, kallonsa ya yi a tsanake kafin ya ce "Na lura kamar ba ka cikin yanayi me kyau, amma ina so ka sani ko da ba wadda kake so a yanzu ba zan iya jurar ganinka kai kaɗai ba, dole zan nema maka ko a cikin dangi ko a Abokan Ƙwarai, gwara ma ka faɗa min gaskiya". sai da ya haɗa da Addu'a sannan ya fara samun nutsuwa, da ƙyar ya tattaro duk jarumtarsa ya yi murmushi sannan ya ce "Abbi ni ma ina da wadda nake so!". "Anya kuwa??, ya akai na ga duk ka firgice ? wai shin me kake ɓoyewa Abokin nan naka?". Ƙara faɗaɗa murmushinsa ya yi a cikin ransa yana neman temakon Allah don samun tsira daga Tuhumar Abbi, shi ba yaro ba ne bare a yi masa ƴar burum-burum bayan haka kuma shi Alƙali ne, don haka in ya ritsa Mutum sai dai Allah ya ƙwace shi.
"Abbi da gaske nake, kawai na ji abin ne ya zo min a baibai, ban shiryawa Aure ko nan da Shekaru bakwai ba ma bare Sati uku, Abbi idan na yi Aure wa zai dinga kula min da ƙanwata?" cikin sa'a kalamansa suka hau Zuciyar Abbi suka yi ɗaram!, murmusawa ya yi kafin ya ce "Ai yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sa na ce ka yi Aure, kai fa Namiji ne wanda aka sani da Fita ba zaman Gida ba, yanzu duk lokacin da ba ka nan fa Bayi ne ke kula da Ƙanwar taka, kai ma babu me kula da kai indai Iyayenka ba sa nan sai dai ka kula da kanka ka kula da ita, amma da zarar ka yi Aure ka ga kun samu wata Uwar, ko da Maimunatu ba ta nan za ku dinga ganinta, za ta kula da Ƙanwarka sannan kai ma za ka samu kulawa daga gareta; ina nuna maka kana rintse ido sai an yi Auren kuma mu ga kana ɗan Tumbi ko??" ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya.
Murmushi haÉ—e da ajiyar Zuciya ya yi a tare, "Kana da gaskiya Babba Sarkin nasara!" ya faÉ—a cikin salon zolaya kamar yadda ya saba faÉ—a masa.
Murmusawa ya yi kana ya ce "To yanzu faÉ—a min Wacece???"

Nan fa Ɗaya wai an cewa shege ina Ubanka, yanzu wa zai ce yana so?? tabbas da ya yi tsalle ya ce da wadda yake so ƙarya ya yi don gujewa Ɗan Uwansa ɓacin rai, sama da ƙasa ya tabbata ba wadda yake so sama da Leelah gashi yanzu tana neman yi masa nisa, to kenan wa zai ce??, Suhana? ko kuma ya faɗi gaskiya kawai???............

(Sai ku ba shi Shawara masu Karatu🚴🏼‍♀️)

SHARE FISABILILLAH

*Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632*

*©️INDO*[11/28, 7:40 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
12

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*GORGEOUS WRITER'S FORUM*

FREE PAGE...........
Chapter 18 · 0% Book details