← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 35

Sashe 24

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zaune can ƙuryar Gadon Umma kamar dai ɗazu, Salim ya shigo yana ƙwala mata kira.
Turmutsawa ya yi har ya dangana da ita sannan ya miƙa mata wata ƴar leda yana cewa "Gashi in ji Mijinki!" Rikicaaa!!!!! gabanta ya faɗi, jin ya ambaci Miji a kanta ba ƙaramin tarwatsa lissafinta ya yi ba, har cikin ƙoƙon ranta tsoro ya kama ta, baki na rawa ta ce "Menene?!" "Waya ce!" ya faɗa yana kici-kicin ciro ta daga kwalinta, Sharr!!!! hawayenta da suke ta tsere a kan fuskarta suka ci gaba da buga wasansu.
Duk da Keypad ce ta yi matuƙar burge Salim, fuskarsa ɗauke da fara'a ya ce "Allah ya sa mu a danshinku Amaryar Ali, wallahi wayar nan ta yi kyau, inda kina gida ne kika same ta ai ni garwasai mihandigarau!!" kasa ce masa komai ta yi sai tsilla ido take yi tana hawaye kamar wadda yake shirin yanka ta. Sai da ya gama ƴan latse latsensa sannan ya miƙa mata yana cewa "Karɓi nan, sai ki riƙe da kyau sabida masu dogon hannu, wallahi yanzu sai ki ji hammatarki tana shan iska, bare dama Mama ta gayyato danginta, kin san a wajensu Rabi'a ta Gada". ita dai ba ta ce komai ba, shi ma bai tsaya sauraren amsarta ba don ya san ba lallai ta ce ba.
Ci gaba ta yi da zamanta ba wanda yake bin ta kanta sai dai a shigo a fita ko a leƙo a koma, gajiya ta yi da zaman ta zame ta kwanta, kwanciyarta ke da wuya baccin wahala ya yi awon gaba da ita.

gaf da la'asar wayar ta yi ƙara, Salma ta farka a mugun firgice, jikinta har wata irin tsuma yake yi tin daga sama har ƙasa, ga wayar da ƙara sosai tuni ta karaɗe ɗakin.
Cikin rawar jiki Salma ta lalubo ta ta ɗauki kiran gami da karawa a kunne, shiru ba magana har ƴan mintuna suka shuɗe, "Assalamu alaiki Salamathh!!!" haɗaɗɗiyar muyarsa ce ta yi nasarar dawo da ita daga ɗan ƙaramin mafarkin da ta tafi, a memakon ta amsa sai ta fara kuka ƙasa-ƙasa, "Ki yi haƙuri ki dena kuka, na san ni me babban laifi ne a bisa hakan ina neman yafiyarki Salamath!, in sha Allah zan sanya ki matuƙar farin ciki, ba zan bari ki zubar da hawaye ba, ba zan barki cikin ƙunci ba, na yi miki wannan Alƙawarin Matatah!!" rintse idanunta ta yi da ƙarfi gami da riƙe kanta da yake sarawa da hannunta guda ɗaya, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" kawai take faɗe tana maimaitawa a cikin ranta, anya kuwa ba mayaudari ba ne?, shi da yake son Leelah me yasa zai Aure ta? kuma har yana nuna kamar dama ita yake so?.
"Indai kin yi fushi da ni ki yi haƙuri ki yafe min kar fushinki ya ida tarwatsa Zuciyata, Salamath!! ki ce wani abu don Allah".
shiru ne ya ƙara ratsa tsakani kafin ta fizgo muryarta da kyar, "Ban yi fushi da kai ba, ai ba a fushi da Ƙaddara, yin hakan kamar yi da hukuncin Allah ne, kuma kai ba me laifi ba ne a wajena, don haka ba ka buƙatar yafiyata".
Sassanyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce "Na gode da kika ba ni matsayin zama Mijinki, kuma ba ki yi fushi da ni ba sannan ba ki gaza yafe min ba duk da na ɓata miki rai, na gode!, Bari na bar ki ki huta".
wurgi ta yi da wayar zuwa gefe ta haÉ—e kai da gwiwa tana kuka gami da wasu sababbin tunanin.

Ana idar da Sallar la'asar DJ ya fara tashi a ƙofar Gidan.
Yau Momi ta cika burinta, kamar yadda ta tsara ranar Auren Leelarta sai ta É—auko DJ.
An haɗa mutane a wajen sosai, an sha rawa kamar ba mutuwa. Kan Leelah ya ƙara huruwa kamar balo.

bayan Sallar Isha'i jerin gwanon Motocin É—aukar Amarya suka iso.
Amaryar kanta ta shirya bare kuma masu kaita, hakan ya sa ba tare da ɓata lokaci ba aka fara cika Motocin.
Ana kan wannan ƙadamin Mota biyu daga ɓangaren Aliyu suka iso suka buƙaci a basu Amarya.
Nan fa kallo ya koma sama, kowacce da an tare ta da batun sai ta ce ga fa inda za ta ga Daula ba abinda zai kaita gidan Talaka, musamman da suka san bayan an kai Leelah É—in daga can za a wuce da su wajen Dinner.
Haka Baban Salma da Umma da ita kanta suka dinga kuka, Su kansu Æ´an É—aukar Amaryar sai da suka yi alawadai.
Umman Nabila da Salim da Yaya Rahina Yayar Nabila, sai Baba Zuwaira da Nabila su kaÉ—ai aka samu suka Amince da raka Salma ÆŠakinta. An sha fama da ita kafin ta yarda ta rabu da Umma
Haka aka É—ebesu kwaraf-kwaraf aka nufi Gidan Amarya kowa ransa ba daÉ—i.

Ɓangaren Leelah kuwa wajen zalamar hawa Mota suka ɓata lokacinsu har aka yi gaba da Salma, sai da aka sha fama kafin aka samu suka daidaita, a hakan ma wasu ba su shiga ba duk yawan Motocin sun yi musu kaɗan sai adaidaita sahu suka hau.

Su Baba Zuwaira sun daÉ—e suna yiwa Salma nasihohi da nusarwa musamman akan abinda ya faru na wariya da aka nuna mata sabida KuÉ—i, da kuma fannin zamantakewa, sannan suka tafi.

Gidan ya rage sai ita kaÉ—ai shiru, gashi ko hasken kirki babu sai Æ´ar wayarta suka kunna mata suka ajiye.
Zuwa yanzu ko kukan ba ta iya yi sai zare ido, ga wani bala'in ciwo da kanta yake yi, tin tana iya gane inda kanta yake har ta dena ganewa sabida bacci ya sace ta.

Ƙarfe Goma da Minti ashirin ta farka, cikin nutsuwa ta buɗe idanunta tana ƙarewa ɗakin kallo, hallau dai babu kowa daga ita sai halinta, Zuciyarta ce ta ƙara karyewa ta shiga tambayar kanta anya kuwa Mutanen nan suna da imani?, su sun kawo ta sun jefar kamar Mushe sun yi gaba, shi kuma wanda ya yi silar zuwanta ko alamunsa babu.
Yunƙurawa ta yi ta gangaro bakin gado ta zauna gami da doka tagumi tana mayar da numfashi, ɗan baccin da ta yi kanta ya dena ciwo sai dai wata muguwar kasala da ta lulluɓeta.

Tana nan zaune tana aikin tunani Khushi ta shigo É—akin bakinta É—auke da sallama, ita ba ma ta san an yi ba bare ta amsa kawai sai jin Mutum ta yi a kanta ana yi mata magana da wani irin yare wanda ba ta san da zamansa a Duniya ba bare ta iya.

Hasken da ya karaÉ—e ÆŠakin ne ya bata damar ganin me yin maganar.

Khushi kuwa ta yi futu-futu da rai ta ƙi yin Hausa.
Tsoro ne ya ƙara ɗarsuwa a Zuciyarta, ido take zarewa Khushi jikinta na rawa, iya kayan da Khushi ɗin ta zaro tana nuna mata kaɗai sun isa razanar da ita. Doguwar riga ce irin ta Amaren ƙasashen Turai, fara tas sai walƙiya da ɗaukar ido take yi, sai mayafi da takalmi da jaka masu irin jikin rigar, wasu mahaukatan Sarƙa Awarwaro da sauransu. Duk da ko a ido Salama ba ta taɓa yin tozali da gold ba ta gane ko ba na gold ba ne sun fi ƙarfin a saka su a jerin waɗanda ta sani.
zuwa yanzu ta gama kaiwa maƙurar rashin Yarda da Aliyu, Zuciyarta ta raya mata anya kuwa ba sayar da ita ya yi ba?.
Wasu Zafafan hawaye ne suka shiga jerangiya akan kumatunta, Addu'ar neman tsari da sharrin wannan Jar mace ta gabanta ta fara yi, Khushi dai ko gezau ba ta yi ba sai surutu take zubawa hankalinta a sume.

Shawarar guduwa ce ta faɗowa Salma, don haka ta tattara hankalinta waje ɗaya ta faki idon Khushi ta miƙe ta zura da gudu.
Kwatsam!!!! ta ji ta shige jikin Mutum, gabanta ne ya ƙara faɗuwa rawar jiki da bugun Zuciyarta suka ƙara tsanani.
Sai da ta fara ƙoƙarin kufcewa sannan ta lura a rungume take katamau a jikinsa, rintse ido ta yi ta fara jera magiya "Don Allah ku ƙyaleni na tafi!, wallahi ban san me na yi muku ba, don Allah ku yi haƙuri, ni kaɗai Ummata da Babana suka haifa".
Kyakkyawar fuskarta ya zubawa ido yana jin tausayinta na ƙara kassara shi, cikin wata irin murya me kama da raɗa ya kira sunanta "Salaamaath!!" cak!!! kukan ya tsaya, tabbas indai ba da aljanu ta yi gamo ba wannan Muryar Aliyu ce, kuma sunan ma shi ta fara jin ya kirata da shi kaf Duniya, wai Salaamaat, ɗago ido ta yi a hankali don tabbatarwa kanta, tana ɗagowa suka haɗa ido ta yi saurin sunkuyar da kanta, wani mugun kwarjini ya yi mata har sai da ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige, ko motsi kasa yi ta yi sai Zuciyarta da ke ta famar tsalle-tsalle.

SHARE FISABILILLAH

*Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632*

*©️INDO*
[12/6, 11:45 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
16

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*G. W. F*

FREE PAGE...........

Khushi ya kalla gami da cewa "Shi ne kika zo kika tsorata ta ko??" Dariya ta yi wadda iyakacinta gefen baki sannan ta ce "Don ban yi mata Hausa ba ne ta tsorata". "To ki yi mata Yaren tsohonki mana!!, in banda neman sababi ta ce miki tana ji ne?"
"Dama ai tsokanarta nake yi" ta faÉ—a tana Æ´ar dariya.
Hannunta ya riƙo suka dawo ciki, a bakin Gado ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna, cikin nutsuwa ya ce "Ki shirya mu tafi Gida Salamaath". Mamaki ya ƙara turmushe Salma, to wai nan ɗin Daji ne ba Gida ba?, ta yiwa kanta tambayar da ba ta da amsarta.
Chapter 24 · 0% Book details