Sashe 8
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gidan Larabawan Asali... sunan ya samo asali ne daga Bleaching ɗin da suka ƙware da yi har Innayi Kakarsu duk girmanta ba ta fasa shafawa ba, da zarar ƴan jikokin nata sun samo tare ake shafewa da ita Allura da ƙwayoyi ne kawai ba ta yi. Waɗanda ba sa shafa mai a gidan daga iyayensu Maza... Ridwan wanda suke kira Baba, sai Ƙannensa, Baba Jamilu, Baba Usama, Baba Habu, sai Umma, sai Yayyensu Maza guda biyu Yusuf (Isuhu) da Bukar, sai Salma wadda Allah ya yota fara tass kamar ba Ƴar gidan nasu ba, hakan ne ya sa Salim yake kiranta Barbela Me Fari daga Allah; wasu daga cikinsu ma suna da nasu hasken daidai gwargwado amma ba su godewa Allah ba, Leelah ma Fara ce amma ta raina natan shi yasa ta shiga harkar Bleachin don ta fi so ta ganta jajir kamar baturiya, musamman yadda ake yi mata kirari da me halittar Larabawa, kuma ta shiga da ƙafar dama don ya yi matuƙar karɓarta, wanda bai gama gane bambancin hasken asali da na shafi ba sai ya rantse a haka Allah ya yo ta. Rabi'u shi ne ƙaraminsu kaf gidan kuma gashi namiji amma hakan bai hana shi shafawa ba, tin yana ɗan ƙaraminsa ake mulka masa har ya tasa ya fara shafawa da kansa, ko da kuwa yana shafawa ana binsa da duka da zagi ne sai ya shafa sai dai me Man ta Mutu.
Cikin wani Koren Yadi Me muguwar Arha, wanda a jerin waɗanda ake kira yi shirunka maraya ma shi ƙarami ne Ya haɗe yake ta zazzare ido. Da kansa ya shiga Kasuwa ya sayo irinsu kusan kala Goma ya bayar aka ɗinka masa, duk cikinsu kuwa ba wani kala me kyau sai masu cika ido, daga fari sai Yalo sai Kore sai ruwan ƙasa, hakan bai isheshi ba sai da ya ƙara zuba su a washing machine ya gurjesu suka yi laushi sannan ya kwashe, ko guga babu ya ninke ya turmutsa abinsa a sif, sai yau da zai fito ya ƙurewa wanka gudu.
Yana tsaye yana rarraba ido don samun wanda zai aika ciki Sumayya ta zo giftawa hannunta riƙe da babbar leda baƙa. Riga da wando ne a jikinta sun yi mugun ɗameta, gashi ba wani mayafin kirki sai ɗan siriri.
Har ta wuce shi ta jiyo tana binsa da wani kallo tin daga sama har ƙasa.
Ɗan risinawa ya yi gami da gaisheta, ba ta amsa ba sai wani taɓe fuska da take yi, "Me kake yi a nan? ina fatan dai ba Kajin Mutane kake fako ba?" ta tambaya a yatsine, faɗaɗa fara'arsa ya ƙara yi har fararen haƙoransa suka bayyana, "A'a na zo wajen Leelah ne!" "Kai ne Ali?" gyaɗa mata kai ya yi, ta zuba masa wata shegiyar harara kafin ta saki wani dogon tsaki ta ci gaba da tafiya.
Sai da ya dena ganinta sannan ya bawa dariyar da take cinsa damar fitowa, yau ya ga ikon Allah.
Fuskarta ɗauke da murmushi ta shiga gidan, tsabar sauri har tana haɗawa da gudu, tana shiga ta saki shewa tana cewa "Leelah!!! fito na karɓo miki kayan, Shegiya Ƴar wahala wai da ba za ta bayar da hayar ba sai an bata kuɗi, sai ka ce ta ga muna cinye mata." Da sauri Leelah ta taso tana cewa "Yawwa na gode, Ɗan iska so nake ya gane duk da ba gidan Masu Kuɗi garemu ba mu ba tsaransa ba ne!"
"Hehehe!! tab, ai wallahi tallahi Ba don ba abinda za ka yi da talauci ba da ba ka tsallake Yaron nan ba". Sumayya ta faɗa cikin zaƙuwa akan bada labarin, Da sauri Haja ta ce "Me kika gani?" "Wallahi kyakkyawa ne na ajin farko ajin ƙarshe, ke kin ganshi kuwa? ni fa ina ga iyayensa ɓatan Dabo suka yi ba Ƴan Najeriya ba ne, Ɗan iskan Yaro yana talaka amma sai kyau, wallahi kalar Madara ne Yaron; gaskiya Talauci bai yi masa adalci ba". Zumbur Rabi'a da Haja suka miƙe tare da nufar ƙofa a tiriliyan. Rabi'a ta ce "Da a baka labari gwara ka bayar". Ikilima ta ce "Wai da gaske kike Anti?" "Wallahil'azimu da gaske nake, kuma ki leƙa ki gani, ba don talaka ba ne in kika Auri wannan ai kaf Kurna ba lallai a samu wadda ta Auri kyakkyawa kamar ki ba." gyale Ikilima ta zabara tana cewa "Wajibin ne in ganewa idona tin kafin mu fita yi masa rashin Mutunci."
Guɗar da Momi ta rangaɗa ce ta sa suka mayar da hankali kanta, "Allahu Akhbar! Allah me baiwa da ƙari, Allah me cuta da magani, in ya baka tsiya sai ya baka arziki, ya baka Talauci kuma ya baka Kadara; ai wallahi ni na san na haifu, Leelah ki sha shagalinki ni nan na ɗaure miki Ƙarƙashi, Yarinya me Farin Jini daga Allah, ba Boka ba Malam amma duk namijin da ya ganki sai ya rikice!!!!, yau da a ce me kuɗi ne hmm! wallahi ba abinda zai hanani kafa DJ yau a layin nan, ai Tinda Sumayya ta yaba da kyawunsa wallahi Uban kowa ma sai ya Sara ko yana so ko ba ya so!!!". "Kin ga Dije ba ma son magana cikin magana!, Uban waye yake bin Bokaye sabida Farin jini? ai wallahi Ƙaryar Mutum ko Maye ne, kuma in kyawun nan kike taƙama da shi ni nawa Ƴaƴan me suka rasa?" Momi ta ce "A'a ni ban ce ba!, Ƴa ce dai ta zama Kainuwa Dashen Allah ba na Mutum ba" Inna ta yi wani murmushi me cike da ma'anoni daban-daban, "Ai Dije in Allah ya ce ka yi sai ka yi ko ta halin ƙaƙa ne, wannan Karon dai ba a Buga a daidai ba tinda Kyau gareshi ba Asali ba, kin san Kuɗi su ne asalin Mutum yanzu". Taɓe baki Momi ta yi ba tare da ta ƙara magana ba, tunda Inna ta shigo zancen kuma an fi ƙarfinta sai dai kallo.
Innayi ce ta iso wajen tana tafi tana rawa tana ƴan waƙe-waƙe "Allah gwanin Baiwa gwanin Hikima!, me yin Ƴan Matan Mata Duma-duma!!, Ƴaƴan kirki masu ƙashin Alheri!"
"Hajiya Innayi !!" Momi ta faɗa tana dariya da shewa, dariya Innayin ta yi tana cewa "A to gaskiya fa!, Yara ƴan dumurmur Masu abin alkairi, ni bari ki ga fita zan yi wurin Yaron nan, in ya zo da leda in karɓo ta, in bai zo da ita ba in yi masa irin wankin da nake yiwa Fatarina". ta ƙarasa maganar tana gyara wani faskeken baƙin glass dake kan fuskarta.
Dariya suka zuba suna ƙara fasa mata kai, ta hura hanci ta yi gaba, a soro ta gamu da su Rabi'a sun taru sai leƙensa suke yi suna zancensa, kurmutsawa ta yi ta wuce tana cewa "Har da waɗannan ƴan ciri-cirin Yaran da ko abin da za a taɓa ba su da shi ake leƙen Saurayin?" Baby ta zuba mata wani shegen kallo kafin ta ce "Wallahi baralallah Innayi!!, ko yanzu ina da abinda zan bawa Namiji komai girmansa, don ko'ina a cik......." Salim ne ya katse ta ta hanyar kai mata duka yana cewa "Ke uwarki!! shegiya me ƙirar Babe sai rashin Kunyar tsiya, idan ita tsohuwar nan mara kara ba ta jin Kunya ai sai ke ki ji don ke yarinya ce Yanzu Kunya ita ce adonki, ko me gareki ma? shegiya ƙirji kamar farantin Silba!" "Allah ya isa wallahi azzalumin banza!!" ta faɗa tana murguɗa baki, takalminsa ya cire ya yi kanta zai fara jibga ta fice da gudu sai kan Innayi wadda take tsaye tana zarowa Aliyu magana.
"Na shiga ukuna! dan Ubanki so kike ki karyani ki tsugunnar da ni?!" Da sauri Aliyu ya ce "Subhanallah! bi a hankali mana Ƙanwata!!, kai kuma fa babba ne ka dinga haƙuri Abokina!" Baby ta kalleshi a raine kafin ta ce "Allah ya sittira na zama ƙanwarka, ai Zaren ba kalar Yadin ba ne, kalli fa kayan jikinka wallahi ko tsumman gidanmu ya fishi Daraja."
Marairaicewa ya yi kamar zai yi kuka ya ce "Haba Ƙanwata, wannan kayan fa sai Juma'a Juma'a nake saka su, sabida zan zo na ga Hasken Idaniyata ne ya sa na saka shi yau." tuntsirewa suka yi da dariya suka tafa ita da Salim, Salim ya ce "Sabon Salo Bleaching a ɗuwawu!, ka ce wanda kake sawa yau da gobe ma sun fi haka lalacewa!! hee!!!! tab!, lallai Anti Leelah ta ɗebowa kanta Ƙara'i, kai yanzu sabida Allah a hakan kake neman Yarinya me kamar Baturiya?? wai ba ka ji kunya ba??" Baby ta ce "Gaya masa dai!" Innayi ta ce "Kun ga! ku yi mana shiru magana muke yi ni da shi; ka miƙo Ƴar ledar nan ta hannunka sai mu ci gaba da tattaunawa"
Daidai lokacin Leelah da Sumayya har da sauran tarkacen suka iso wajen sai huɗa hancika suke yi suna shaƙa suna busarwa gami da ɗibarsa suna watsarwa.