Sashe 16
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Raka shi suka yi har bakin Titi suna yi masa ihu tuni Yaran suka ƙara yawa sun fi Talatin, haka suka yi masa wanka tsaf da kwata.
Shi kuwa ko Uffan bai iya cewa ba.
Sai da suka zo Titin ne suka gamu da Bukar ya dawo daga gantalinsa yana tafiya yana haÉ—a Hanya, ganin abinda suke yi ya sa shi fara yi musu magana yana danna musu ashar.
Ɗaya daga cikin Yaran ne ya bashi labarin ce Ƙanwarsa Leelah ita ta saka su. jin haka ya sa shi rarumar dutse ya fara binsu yana Haɗa musu ashar "Don Abutakazar Ubanku don ta sa ku sai ku yi? Ku ma ba kwa so ta yi Aure mu huta ko dan Jatta abin ubanku??!, Shegu munafukai Ƴan hassada!!"
Watsewa suka yi kowa ya fara gudun ceton Kansa, sun san tsohon Ɗan Ganja ne yanzu sai ya bugawa Mutum Ƙaton dutsen kuma bala'in Ƴan Gidansu ma kaɗai ba zai bari a ƙwatar maka Ƴancinka ba.
Cikin Unguwar ya bisu suka ci gaba da raba Wuta, hakan ya bawa Aliyu Damar nufar inda Motarsa take, tin kafin ya ƙarasa Qadri ya matso da ita, shiga kawai ya yi ba tare da ya yi masa magana ba duk da Qadri ɗin yana ta tambayar dalilin faruwar hakan.
Bhaba da Maa suna zaune a Katafaren Falon da ke tsakiyar Gidan suna hira. Bhaba ne ya ƙara faɗaɗa murmushinsa yana cewa "Na manta ban gaya miki ba Ɗanki fa ya kusa Aure". "Shi??" ta faɗa a taƙaice, amsa ya bata da cewa "Haydar, ya yi mini magana akan ya samu wadda yake so, na yi farin ciki da hakan don kuwa ni ma ina da shirin yi masa ko bai shirya ba." Murmushi ta saki har haƙoranta suka bayyana "Ma sha Allah!, na yi farin ciki ni ma, ka ga yanzu sai ya san ya girma ko?" ta faɗa tana tsirawa Bhaba ƙwala-ƙwalan idanunta. Sosai ya ji daɗin nuna farin cikin da ta yi a kai, Cikin fara'a ya ce "Sosai ma kuwa, kuma dai cikin ƙanƙanin lokaci za a yi, gobe ma in Allah ya yarda za su je nema masa Auren wajen Iyayenta." "Oh! za su je ko kuma za ku je??" "Ni fa ba zan je nemawa Haydar Aure ba, Ɗan Farko ne fa!!, kuma ai yana da iyaye da yawa, Alhaji Awwal, Alhaji Ibrahim, Alhaji Abdussalam, MD, Alhaji Yusuf, su na wakilta su yi komai. "Achcha!, na san za su yi komai fiye da yadda za ka yi da kanka, Allah ya sanya Alkairi"
Kafin ya yi magana suka ga Aliyu ya shigo tsamo-tsamo.
Ya zama Kurman Dole, ko sallama bai yi ba sai shashshekar kukansa dake tashi kaÉ—an-kaÉ—an, bai kula su ba ya wuce hanyar sashinsa.
Da ido suka raka shi su duka Bhaba ya cika da mamakin ganinsa haka, ya miƙe zai bi bayansa Maa ta yi saurin tashi ta nufi Sama cikin gudu-gudu sauri-sauri.
"Subhanallah!" kawai ya furta don ya san yau akwai artabu.
Dole ya fasa zuwa wajen Aliyu ya bi bayanta.
A baranda ya sameta tsaye ta riƙe ƙarfen dake gabanta tana kallon ƙasa, kusa da ita ya ƙarasa jiki a sanyaye ya ce "Moonath...." saurin ɗaga masa hannu ta yi cikin shashshekar kuka ta ce "Kya ƙyaleni ba na son jin komai!" "Ba zan iya ƙyaleki ba Moonath!, kuka fa kike yi! me yasa haka? ni ban ga abinda za ki zauna kina yiwa kuka a nan ba." Goge hawayen ta fara yi gami da yin murmushin takaici "Kai a wajenka ba abin Kuka ba ne ni kuma a wajena abinda ya fi hakan ma zan yi!, ko Mutuwa ya yi kai kana da wani Ɗan, a wurinka za su dawo biyu ne ni kuma zan tashi da guda Ɗaya, Shi ne kaɗai Ɗa Namiji da na Haifa kuma watan wata rana shi zai zamo min Uba; kafin na sameshi babu irin wahalar da ban sha ba, kai da kanka sai da ka Guje ni ka Auro wata, haka danginka duk suka Juya min baya na zama Abar Gori da cin Mutunci sabida ban haihu ba, yanzu kuma na haifa shi ne kake cewa kar na damu da damuwarsa?? anya ka yi min Adalci kuwa Jaan??" jinjina kai ya yi Zuciyarsa sam ba daɗi, a sanyaye ya ce "Ni ma damuwar Aliyu damuwata ce don ko a yanzu ba ni da wani tamkar shi tinda shi ne me tausaya min kuma me Mutunta ni, sannan ban ce kar ki damu da damuwarsa ba amma abin zai yi min yawa Moonath, Ke kina kuka shi yana yi za ku jefani cikin wani hali, don Allah ki yi haƙ......" katse shi ta yi da cewa "Kar ka ba ni haƙuri don ba zan haƙura ba; Ni ban taɓa sa Ɗana kuka ba, kuma ban haife shi don ya yi Kuka ba, duk wanda ya sa shi kuka sau ɗaya ni zan iya sa shi ya yi na har Ƙarshen Rayuwarsa; Jaan! Billahillazi huwar Rahman indai Yarinyar nan ta bari Roshan ya faɗa mugun hali ta Dalilinta sai na yi mata mummunar Ɗaukar da su kansu iyayenta sai sun gogeta daga cikin Tunaninsu, indai wani abu ya faru da shi babu shakka sai na Lalatawa duk danginta Farin cikinsu!!!" Cike da damuwa Bhaba ya ce "Komai fa da maslaha ake binsa, kar ki nuna Ƙarfin Ikonki akan wata Ƙaramar Yarinya, na san Ƙuruciya ce kawai take damunta, ki bari ni zan shiga lamarin, zan je in yi magana da iyayenta komai zai yi daidai in sha Allah". "Ba na buƙatar ka shiga lamarin, ka je ka yi maganar Auren Haydar kawai ni kuma zan samawa Ɗana farin cikinsa, kuma ka san da ba zan iya ba ba zan ce zan aikata ba".
"Eh na san ke me faɗe da cikawa ce kuma kina da ikon yi mata komai, don haka ba zan fasa ba ki haƙuri ba, na san shi kansa Aliyu ba zai so abinda zai ɓata mata rai ba tinda yana sonta sosai, yanzu dai ki dena kukan nan ki kwantar da hankalinki, ina so na je wajensa...." kafin ya ƙarasa ta katse shi da cewa "Ka je kawai, ni ma daga baya zan yi magana da shi"
"Okay" kawai ya ce sannan ya nufi sashin Aliyu.
Sai da su Salma suka dawo suka tarar su Rabi na maimaita abinda ya faru cikin nishaÉ—i da jin daÉ—i.
Takaici abin ya basu har Salim da yake ɗan cas da as, cike da takaici ya ce "Amma ku wallahi an yi ƴan Bala'i, in banda abinki ma Leelah ke da kika samu Masoyi wanda ake kira na a zo a gani ina ruwanki da tsayawa Tijara da wannan? ai kamata ya yi ki bi shi ta lallami da lumana ku rabu sabida ke yanzu Darajarki ta ninka ta Da, Allah ya sa zancen ya koma kunnen danginsa su ce ba ki da Tarbiya, kin san dai zancen Duniya ba ya ɓuya, musamman ga manya irin waɗannan kin san dole yanzu duk motsin da za ki yi idanunsu yana kanki."
Tsaki ta yi gami da cewa "Ka ga! Na ci Mutuncinsa ƙarewa ma na sa an yi masa abinda ko maye ne ba zai dawo ba, idan goyon bayansa kake yi sai ka je ka Aureshi." cikin zaro ido Salim ya ce "A'uzubillah! ina Gardi yana Gardi kike ambata mana Aure sai ka ce kin zo a zamanin Jahiliyya?, Allah ya yi min tsari, wallahi bakinki ya sari ƙasa!".
Salama da baƙin ciki ya isheta ta ce "Ki dinga abinda hankali zai ɗauka Leelah, me yasa wai Duniya ta rufe muku ido ne?, akan son Duniya har kike irin wannan furucin da ko Kafiri a wannan zamanin ba lallai ya yi ba; in da ba ki fita ba kika yi masa banza ai da ba zai ganki ba ma bare har ya sa ran za ki saurare shi". "To ke ma Ƴar Wankau ba na son yawan Munafurci da tsugudidi, shi in Namiji ne ai ke macece sai ki je ki Aureshi, dama na ga ko kare bai shinshina ba, kina cin arzikin Mutum kina yi masa hassada." Salama ta yi saurin cewa "Allah ya baki haƙuri Leelah, in sha Allahu ba zan ƙara cewa komai ba; hassadar ma sai ka kai matsayin da za ka yi sannan kake yinta, ai kin fi ƙarfina ban kai matsayin da zan yi miki hassada ba, bare ma ba halina ba ne, kuma in Allah ya yarda ba zan ƙara karɓar abin da za ki ba ni ba tinda abin ya zama na Gori!" Kuka ne ya kufce mata ta yi saurin miƙewa ta bar wajen da gudu.
Shewa Mama ta zuba "Hee!!! yau dai mun ga wasu a rana, komai a ce Salama komai a ce Leelah to dai yau ga abinda muka gani!"
Dariya sauran Mutanen wajen suka sa Innayi ta ce "Lailah ce Ƴar kunama ka gama rainonta ta ɗalla maka cizo!, ai kowa ya san kafin Salama ta moreta sau ɗaya ita ta moreta sau goma."
Salim ma tsaki ya ja ya ce "To Allah ya kyauta miki Anti Leelah, wai me yi maka shi ne tsinanne a wajenka sabida abin Duniya." daga haka shi ma ya bar musu wajen.
Sosai jikin Leelah ya yi sanyi ƙalau, tashi ta yi ta nufi Ɗakin Umma don ta bawa Salama haƙuri, ita kanta ta san ba ta kyauta ba, kawai don tana cike da jin haushin Ali ne shi yasa ta gaya mata magana.
Daren yau dai Kwanan Farin ciki Leelah ta yi don Haydar ya sanar mata gobe Manyansa za su zo a yi maganar Aurensu. Tin a lokacin labari ya karaÉ—e ko'ina su ma iyayen nata aka sanar musu don su shirya. Kwana ta yi tana mafarkai sabida tsabar farin ciki har gani ta yi an ÆŠaura Auren a Mafarki.
SHARE FISABILILLAH
*Samu Æ´ancin karantawa, ta hanyar biyan Naira ÆŠari Uku 300 kacalâ˜ºï¸ Domin Ƙarin bayani 👉🽠09079885632*
*©ï¸INDO*
[11/27, 1:02 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
11
©ï¸
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*