Sashe 21
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Salim ne ya lallaɓo ya janye Salama daga cikin tawagar ƴan ganin lefe ya jata gefe, cikin takaici ya ce "Wai ke Salma don Allah ba ki san ke ma Amarya ce ba? kamata ya yi ki dinga jan ajinki, amma kin je sai washe baki kike yi kina murna akan lefen da ba naki ba." Harara ta zuba masa tana cewa "Me kake nufi da hakan? wai kana nufin ba zan taya Leelah murna ba?" sassauta murya ya yi kafin ya ce "Shiga za ki yi ɗaki ki yi bulum! kamar ba kya gidan, in ya so sai ki yi ta tsalle a ɗakin ke kaɗai, ƙarewar murna kenan, ni fa na fi so ke ma ki dinga jan aji, ba ki ga yadda Leelah take yi ba? sai hura hanci take yi magana ma yanzu ba kowa take yiwa ba?" Salma ta rausayar da kai kafin ta ce "To! ni me zai kai ni in dinga hurawa Mutane hanci? ni ko me kuɗin zan Aura ba zan yi haka ba bare ina talaka wanda zan Aura ma haka, ni dai ka barni in yi murnata tinda Leelah burinta ya cika, ni dai Allah ya nuna mini ranar da za a ɗaura Auren, ka san fa tana matuƙar son ta Auri me kuɗi, ko a Littafi ta ji an yi lefe me yawa irin haka sai ta ji dama ita ce " ta ƙarasa maganar tana dashare baki, taɓe baki ya yi gami da yi mata wani kallon tara saura kwata, "Gaskiya ke dai kalarki daban Salama, wallahi duk gidan nan ba me yi miki farin ciki don kin samu irin wannan kayan, kowacce ji za ta yi dama ba ke aka kawo ba ita aka kawowa, kin ga daga haka dole sai hassada ta samu; ni ba ma haka ba yanzu, ni fa na shiga damuwa sabida ban ga an kawo naki lefen ba, kar fa mu je su ce ba za su yi ba, ai kuwa da an ga salawaitun bala'i don wallahi ba za mu ɗaukeki sukutum guda mu ba su ba tare da sun yi mana lefe ba!" ya ƙarasa maganar yana tattafa hannuwa gami da jujjuya idanu.
Jikinta ne ya yi sanyi, tabbas ita ma tana wannan tunanin, indai kuwa ba za su yi mata ba sun jawo mata gori, amma ba yadda za ta yi haka nan za ta jure. Ganin Salim yana ta cika yana batsewa ya sa ta yi murmushi cikin son kwantar masa da hankali ta ce "Yo kai banda abinka saura kwana huɗu fa yau, ka ga wasu ma fa sai ranar ɗaurin Aure suke kawo lefe, to ƙila su ma haka ne, kuma ko ba su yi ba mu ina ruwanmu? ba ka ga Babana ya sayo min Atamfar da zan saka ranar ba? ka zo ka raka ni ma na karɓo ɗinkin in zo in gogeta tin yau, Kawuna ma ya ce zai ɗinko min leshi, ka ga ai ina da kayan sawa." "Wai ke don Allah Salama ba kya jin ba daɗi ne? kina ji fa har maƙota munafukai sai habaici ake yi miki, amma shi ne kike wani lissafin ko ba a yi lefe ba ina ruwanki?" zuwa yanzu Zuciyarta ta gama karyewa don ya tuna mata abinda yake ta cin Zuciyarta tana ƙoƙarin danne shi, kamar za ta yi kuka ta ce "To wai yaya zan yi Salim? tin fa ranar da Leelah ta sa aka kori Ali daga gidan nan ban ƙara ganinsa ba, gashi ni ko waya ba ni da ita bare ya kirani, bai ƙara bi ta kaina ba bare ya san halin da nake ciki, iyayen nasa ma tinda suka zo sau ɗaya ɗinnan ban ƙara jin ɗuriyarsu ba, sai dai na ji Babana ya ce wataran sun yi waya da su; ni dai ka manta da su kawai ai lefe bai zama dole ba Sadaƙi shi ne dole, shi ne in ba su bayar ba ba wanda zai yarda a ɗaura Auren". cikin sanyin jiki ya ce "Kin fi ni faskiya kuma, to Allah ya tabbatar da Alkairi".
Hira suka ci gaba da yi akan abinda ya shafe su, a nan su Sumayya suka same su, zama suka yi suka fara zuga Salama akan kar ta karɓi lefe kaɗan bare ma har a ƙi yi mata.
Ita dai jinsu take yi ba ta ba su amanna ba har suka gaji suka ba su wuri.
Sai da suka watse Salim ya ce "Kin ga waÉ—annan masu buÉ—ewa Mutane ido akan abin Duniyar? wallahi kawai so suke su cuci Mutum su sa masa son Duniya su jefa shi a wahala, ni dai na rasa me yasa Æ´an gidanmu suke a haka."
Murmusawa ta yi gami da cewa "Mu yi musu Addu'ar Allah ya shiryesu."
Ya ce "Amin in masu shiryuwa ne."
Washe gari....... ba iya Salim ba kowa ma ya sa ran ganin an kawo lefen Salama sai dai har aka kwana aka hantse shiru, haka aka ƙara kwana har yamma ta yi ba labari.
Salma dai tuni ta fitar da rai ta fawwala wa Allah, Leshin da Kawunta ya É—inka mata da Atamfar da Babanta ya yi mata su ta goge ta ajiye a matsayin wanda za ta saka ranar bikin.
Salim kuwa sai zumɓure-zumɓure yake yi, gabaki ɗaya haushin kowa yake ji. Momi ta lura da hakan don haka ta zauna ta tuje masa ta yi masa zagin tsamar nama akan dalilinta na ya fi son wata a kan Ƴar Uwarsa, har da cewa baƙin ciki da hassada yake mata don Leelah ta samu me Kuɗi.
Abin ya yi bala'in damunsa, ya yi kuka har ya godewa Allah, ya kasa gane me yasa Mominsa take abu tamkar na marasa hankali, ita kanta Leelah wai haushinsa take ji, shi dai har ga Allah ya san ba wai hassada yake musu ba, kuma ba ya fi son Salma ba ne, sai dai ya shaida akwai shaƙuwa da ƙauna a tsakaninsu, kuma duk da Salma ba ta da kuɗi kafin Ƴar Uwar ta shi ta kyautata masa sau ɗaya ita ta yi masa sau goma, don ko wankinsa wani lokacin ita take yi masa sai ta ci tira ne suke yi tare.
Da daddare ba zato ba tsammani sai ga su Kawu Mahmuda da Akwatu uku. Su Baba suka yi ta murna suna sa Albarka. Suka rabu cikin Mutunci da Mutuntawa. Ana shigar da kayan cikin Gida kuwa su Mama suka fara cewa ai yanzu an dena yin Akwatu uku sai biyar ko shida, a tsiyace shi ne huÉ—u.
Ita dai Umma ko iya haka an biyata don ita ma ta fitar da rai, da ga an kawo kuwa sai farin ciki ya rufeta amma duk da haka ko inda Akwatun suke ba ta kalla ba bare ta ce wani abin.
Duk da dare ne sai da aka tara Maƙota da yake akwai Nepa lokacin sai abin ya fi armashi.
Sai shewa suke yi suna guɗa sai dai mafi yawancinsu ba su yaba ba, daga na Gidan har Maƙotan, har da ƙanwar su Baba, sai cewa suke yi waccan Atamfar me arha ce, wancan leshin ba shi da ƙarko, ai Leelah ita ta mori kaya ta mori Miji.
(Ku ji fa sakarci masu karatu.🤔 Wai ba a damu da Kyawawan Ɗabi'u ko Halayensa ba sabida yana da Kuɗi ake kiran an Mori Miji🥹)
Yau ana i gobe ɗaurin Aure kenan..... tin safe baƙi suka fara sauka kuma tin safen aka fara shirin Party.
Leelah sai rawar jiki take yi har ta ƙagara Daren ya yi.
Su Umma Rakiya Ƙanwar su Baba da sauran dangi har da Ƴan Uwan Momi da Maƙota, suna shirin tafiya Gidan Leelah a cewar su za su je jere sai ga Baba Habu da Motar kayansa, ya zo neman waɗanda za su je yiwa Salama jere.
Nan ma an sha tsalle don kuwa kowacce tirjewa ta yi, su fa ga Gidan da za su sha AC ba abinda zai kai su su sha wahala har da ƙarin cewa ƙila ko Abinci ba za a ba su ba.
Baba Habu abin ya yi masa ciwo har ƙwalla sai da ya yi Musamman da ya ga wai har da Ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗaya a cikin masu cewa ba za su yi masa abu ba sabida ba shi da Kuɗi.
Salim ne ya daki ƙirji ya fita ya lalubo Abokansa duk da ba su gareshi sosai ba, Mutum biyu ne ke kula shi sabida kasancewarsa Kamar ɗan daudu sai kowa ya dinga cewa ba ruwansa da Mace sai ya zama abin tsokana da ƙyama.
Su biyun duka suka sanar da Iyayensu mata akan su temaka su je a yi da su, cikin sa'a suka Amince.
Daga su sai Matar Kawu Ishaq Yayan Umma, sai Salim da Abokansa, suka tafi.
Gida ne ɗan madaidaici me ɗaki Biyu sai Kicin da banɗaki, ya sha fenti fayau ya yi kyau sosai, duk da cewar fentin ma me arha ne amma ko'ina ya yi son kowa ƙin wanda ya rasa.
Da yake kayan ba masu yawan gaske ba ne komai ya hau ya zauna, sai Gidan ya ƙara kyau.
Su ma sun yi tunanin ba za su samu ko ruwan sha ba sai ga shi an kawo musu Abinci har da nama, ga ruwa da lemuka.
Leelah tin Azahar suka tafi kwalliya Sumayya ce Æ´ar rakiyar ta.
Kamar yadda Haydar ya cancare kuÉ—i ya zube haka suke son su yi fita ta fitar hankali.
Salma dai ta tubure ta ce ko kwalli ba za ta saka ba, Aliyu ya ce ba ya son wani Party kuma dama ba ra'ayinta ba ne, ko Æ´ar Walimar da ake yi a Gida ma ta ce ba za ta yi ba don ba ta da Abin da za ta bawa waÉ—anda ta gayyata.
SHARE FISABILILLAH
*Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira ÆŠari Uku 300 kacalâ˜ºï¸ TuntuÉ“i Lambar Waya👉🽠09079885632*
*©ï¸INDO*
[12/6, 11:28 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
14
©ï¸
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*
FREE PAGE...........