← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 35

Sashe 15

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tuni Iyayen ƴaƴan suka hau shi da caccaka kamar ba za su bar shi da rai ba, har ita kanta Mahaifiyarsa don gani take tamkar zai kashe mata kasuwar Ƴaƴanta su da har kwana suna yi a waje, Momi ma har da cewa hassada yake mata kuma baƙin cikinta da ƴaƴanta shi zai kashe shi.
Inna da Momi an ɓula musu sun ga jini nan, suka kafa tasu masifar akan Mazajensu sun tara musu ƴaƴa amma sai lalaci ba sa ma fita neman bare su samu sai zama a bakin bishiya sai iya shiga majalisa a zauna.
Sai da ya yi nadamar tanka musu da ya yi, dama can wannan dalilin ne ya sa ya dena yi musu faɗan yanzun ma ƙara ƙureshi suka yi.

Yau kowa sai da ya sha Habaici daga wajen Momi musamman Salma da ko saurayi É—aya ba ta da shi duk da cewar ta girmi Leelah ma. Su kuwa Inna da Mama abinda suka saba yi ne ta jefa musu su jefa mata. Umman ce dai ba ta iya cewa komai duk da abin yana damunta.

Tin goman dare tsakar gidan ya yi tsit kamar babu kowa a cikinsa, wanda ko Ƴan Matan ba sa nan akwai Salim da Salma da Innayi su ne masu haɗa camba sai masu tayasu su Momi da Mama, Inna ma ba ta fiye shiga ba don ita zubin Salihai gareta a sarari a ɓoye kuwa sam ba haka take ba.

"To kun ga dai masu Ƙashin Arziki!, wai ɗan Alhaji Mustafa Naira shi ne ya zo gidan nan neman Aure kuma ba wajenku ba, wai Yaron ba jika ne kenan a wajen Alƙali Kabiru Mai Zafi ba?? ai asalinsu Ƴan Cikin gari ne, ni na san su sarai in gaya muku, waɗannan su ne asalin Kano Uwata da kuka sani ta yi aikatau a gidan Alhaji Mai Zafi; ku dai wallahi kun jawo wa kanku zagi da gori, ni wallahi dama ni na haifi Laila!!" Mama ce ta zage tana zubawa su Rabi masifa, shiru suka yi mata don abin ya sosa musu rai don dai ba yadda za su yi. Sai da ta gama ƙare musu tas sannan ta haƙura ta kwanta tana ci gaba da yi musu gori akan ubansu bai tashi ya nema ba su ma sun ƙi nemowa su kawo mata.

Haka suka kwana tare da ƙudurin dole sai sun yi Auren kece raini su ma.

A ɓangaren su Sumayya ma zancen da suke yi kenan har bacci ya kwashe Inna sannan suka koma ɗakinsu.

Salma ma yau abin Duniya ya isheta a kan gori da goribar da suke yi mata na cewar ba ta da mashinshini, kuma ba samu ne ba ta yi ba ita ba za ta iya kula samarin banza ƴan jagaliya ba shi yasa duk wanda ya zo take taka masa burki, don kuwa yawancinsu samarin Unguwar ne Ƴan jagaliya ƴan zaman bati siddan wanda Saurararsu ma ba ta da amfani.
Kuka ta dinga yiwa Umma tana cewa duk wadda ta ƙara ci mata Mutunci sai ta rama, Umma dai sai haƙuri take bata tana rarrashinta har ta samu ta nutsu.

Su ma su Leelah suna É—aki suna shewa suna taune-taunen abinda Haydar ya kawo.
Duk abinda take yi hankalinta na kan wayar da ta gani a cikin kayan ko za ta ga kiransa amma shiru.

Abin kamar wasa har dare ya yi ta koma É—akinsu shiru, tafi-tafiya har wayewar gari.

SHARE FISABILILLAH

*Samu Ƴancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632*

*©️INDO*[11/26, 4:58 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
10

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*G. W. F*

FREE PAGE...........

Abu kamar wasa har yamma ba ta ƙara jin motsin Haydar ba, Zuciyarta duk ta tsinke ta shiga damuwa, kowa na sabgoginsa amma ita ta kasa sukuni gabaki ɗaya hankalinta na kansa.

Salim ne ya kalli Salma murya ƙasa-ƙasa ya ce "Anti Salama kin san menene?" girgiza kai ta yi alamar a'a tana ƙoƙarin ɗaure kayan da ta gama Gogewa.
"Haƙuri nake son ba ki akan abinda aka yi miki jiya a gidan nan, na san wallahi kin ji ba daɗi kawai dai kina haƙuri ne. murmusawa ta yi gami da cewa "Kai waye ya faɗa maka?, ni ban ji komai ba kwata-kwata, koda an yi min laifi farin cikin da Leelah take ciki ai ba zai bari na ji komai ba; wallahi na ji daɗi sosai Allah ya tabbatar da Alkairi, ni dai ina so in ga duk mun yi Aure ko don mu ragewa Iyayenmu nauyi." taɓe baki ya yi gami da yin farr! da ido sannan ya ce "Allah Sarki!, ai wallahi Na san kina farin ciki amma dole ne sai abinda aka yi miki ya yi miki ciwo, batun Aure kuma ku da kuke son yi Allah ya tabbatar waɗanda kuma Yaudara suka sa a gaba su ma Allah ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba ya yi birgima!" Dariya ta yi tana cewa "Ni tashi ka rakani in kaiwa Hajiya Yalwa kayanta, tin jiya take yo mini aike to sai yau Allah ya sa na gama Gugar". tashin ya yi yana cewa "Ai wallahi ni kina burgeni Salama, ba kya bin Samari don samun kuɗi, kuma ba kya Sata, ba ki sawa kanki Son Duniya ba kin riƙe Ƴar Sana'ar wanki da Gugarki kina samu kina temakawa Iyayenki". ƙullin kayan ta jibga masa a kansa tana cewa "Maganar ce ba ta isheka ba!, ni karɓar min wannan". Ƙaramar ƙara ya saki kafin ya ce "So kike ki ɓalla min wuya ki sabauta ni? ke daram da ke yanzu za ki ga an yi wuf da ke ni kuwa in kika ɓalle min wani abu babu Ƙatuwar da za ta yarda ta Aureni."
Dariya ta sa ba tare da ta bashi amsa ba ta yi hanyar fita.
Bin bayanta ya yi yana ci gaba da ƙorafi har Matar da ta kawo wankin ba ta tsira ba.

Salim yana fita ya yi turus!! ganin Aliyu a tsaye, ya haɗe cikin ɗan yamulmulin Yadinsa Yellow. Har ta yi gaba ta ji yana cewa "Kai yanzu sabida Allah dawowa ka ƙara yi??, wai kai Gori ma ba ya yi maka ciwo ne?" juyowa ta yi don ganin ko waye, suna haɗa ido da shi ta yi saurin kawar da kai tana cewa "Kai Salim ka tawo mu tafi dalla, magrib fa neman yi take yi". Muryar Aliyu ta ji yana cewa "Ina wuni Aunty!" dariya abin ya bata don haka ta dara sannan ta ce "Ina wuni!" shi ma dariyar kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba.
Salim ya tafa hannuwa ya riƙe haɓa yana cewa "O'o Allah Gwani!!, ina gaya maka gaskiya kana gaisar da wata? shawara fa nake ba ka don wallahi yau in Leelah ta ganka a Gidan nan Allah ne kaɗai ya san Hukuncin da za ta yi maka". "Haba ƙanina! ni fa ba da rigima na zo ba kawai na ga yau Jumu'a ne shi ya sa na zo mu gaisa". Salma ce ta dubeshi a tsanake ta ce "Ba don Salim ba ya sonka yake gaya maka haka ba, gaskiya yake gaya maka, ka san ba a yiwa so dole, kuma da a ce Leelah ba ta samu wanda take so har sun yi maganar Aure ba sai ka ci gaba ƙila za ka iya dacewa." "A to! gaya masa dai!!" Salim ya faɗa yana murguɗe baki.

Kamar Karon Ƙarfe da ƙarfe haka Aliyu ya ji saukar maganar kwaram-kwatsam!! Salma ya zubawa idanu cike da son samun tabbaci, "Maganar Auren Leelah fa?" ya faɗa a kiɗime.
Kafin Salama ta yi magana Salim ya ce "Fes da aniya!, jiyan nan Aliyu ÆŠan Almustafa Naira ya zo wurinta suka gana kuma har sun tsayar da maganar Aure, in gaya maka yanzu komai ya zauna kawai jiransa muke yi ya turo Walidansa".
Gefen leɓensa ya kama ya cije da ƙarfi gami da rintse idanunsa, wani irin kururuwa da kuwwa gami da hanƙoro ƙwaƙwalwarsa take yi, Zuciyarsa kuwa jin ta yake yi tamkar za ta fita daga cikin ƙirjinsa, bayan shi da Ɗan uwansa wanene Aliyu Almustafa Naira? tabbas in haka ne Haydar ya yi masa lahani kamar yadda ya sha Alwashin yi masa.

Sama-sama ya jiyo muryar Salma tana cewa "To ka ji iyakar gaskiyar, kuma maganar gaskiya ga ÆŠan Masu kuÉ—i babu lallai Leelah ta Amince da kai, zai fi maka kyau ma ka yi tafiyarka tin kafin ta fito". Salim ya ce "Kin ga Aunty Salma mu tafi mu kaiwa wannan Lukutar Matar Kayanta kar ta dena kawo miki Wankau É—in mu boni."

Bayan sun yi gaba Salim ya ce "Wallahi Salama ban taɓa ganin Saurayin da yake son Ƴar gidanmu kuma na tausaya masa sama da wannan ba, ni fa na lura wallahi da gaske yake sonta, ƙila sai ta fi ma samun kwanciyar hankali in shi ta Aura." "To ai Salim komai nufin Allah ne, Allah ya zaɓa mata mafi Alkairi kawai. da Amin ya amsa sannan suka saki hirar suka kama wata.

Kasa motsawa ya yi daga wajen bare ya san inda dare ya yi masa, yana nan tsaye har su Sumayya suka zo shiga Gidan suna ganinsa suka ja tinga, Nana ta yi saurin shiga ciki ta sanarwa Leelah, ba jimawa suka fito suka sa shi a tsakiya suka fara kwarkware masa har da cewa idan Haydar ya san yana zuwa wajenta ma ai Mutuncinta zubewa zai yi.

Hakan duk bai burge Leelah ba don haka ta gayyato Yaran Layinsu ta ce su yi masa wanka da ruwan kwata su kore shi, in suka ƙara ganinsa a Unguwar ma su ƙara yi masa haka su haɗa masa har da duka.
A ganinta hakan shi ne mafita in aka yi masa ba lallai ya ƙara dawowa ba.

Cikin gida suka shige suka barshi da gayyar Yara waÉ—anda ke ji da fitina da kuma rashin ÆŠabi'a.
Ai kuwa gamo da kasawa tuni wasu suka fara dukansa, wasu kuma suna kawo gudunmawar ruwan kwata.
Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafafunsa da suka yi wani irin nauyi ya fara tafiya kamar zai kife ƙasa.
Chapter 15 · 0% Book details