← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 35

Sashe 10

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Yaushe kika dawo Umma?" "Hmm! kwana biyu na lura kana son titsiyeni; na daɗe da sauka har na je wajen Abbi" idanunsa ne suka ƙara girma, cikin kaɗuwa ya ce "Me kika yo a wajensa??" cikin ƙasaitaccen takunta ta ƙarasa kusa da inda yake tsaye ta zauna sannan ta ce "Irfan a zauna mana!" cikin sanyin jiki Irfan ya zauna a kan Carpet har lokacin kansa a ƙasa kamar tsohon munafuki, mayar da kallonta ta yi kan Aliyu sannan ta ce "Vah hai Meri Bhaba Roshan!, ka ga dole ne na je na gaisheshi". sirrintacciyar ajiyar Zuciya ya sauke, ya yi tunanin har abinda ya faru tsakanin Khushi da Mammi ya risketa shi ya sa ta je wajen Abbin.
Wurin zama ya nema ya zauna yana cewa "Mommy kin yi mana bazata fa" "Eh dama hakan na yi niyar yi"
Gaisheta Irfan da Muzaffar suka yi ta amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsu iyayensu, Muzaffar ne kawai ya amsa.

"Irfan da kai na fi yarda don haka ka gaya mini abinda ke faruwa, na lura Roshan kamar ba daidai yake ba." gyaɗa kai ya yi kafin ya ce "Haka ne Umma daga Unguwa muke." "Kenan fitar da kuka yi ce ta kawo sauyin?" Khushi ta zumɓuro baki ta ce "Ni zan faɗa miki gaskiya Maa, wallahi wa....." da sauri Muzaffar ya ce "Maa wannan ƴar Adawa ce ni zan faɗa miki." murmusawa ta yi gami da cewa "Ina saurara!"
Gyara zama ya yi sannan ya shiga bata labarin duk abinda ya faru, Irfan da Aliyu ba su ce komai ba sai zare ido.

Labarin ya taɓa ta har cikin rai amma sai ta yi kamar ba ta damu ba, "Abinda ba za ka iya faɗa min ba kenan Roshan?" ta tambaya tana tsare shi da idanu, murmusawa ya yi gami da cewa "A'a Maa, kawai dai na fi so sai komai ya daidaita ne sai in gaya miki, na yi zaton komai zai zo da sauƙi." "Achcha!, ni ma Ina Sonta, ka ƙoƙarta ka shawo kanta; sai dai ina so ka san ba zan iya jure ganin ana wulaƙantaka ba, ya zama dole ka kula, su ma su kula". "Ni Mommy kawai ki je ku yi maganar Auren, ko ba sa so ki sa a yi da kanki!". Khushi ta faɗa tana taɓe fuska.
Yalwataccen murmushi ta yi gami da cewa "Ba komai ne KuÉ—i ke iya saya ba Khushi, zan iya saya masa Yarinyar amma ba zan iya saya masa soyayyarta ba, duk da kuwa tana da son kuÉ—i kin ga za ta Auri kuÉ—in ne kawai ba Roshan ba, tunaninsa me kyau ne kuma abinda yake so shi nake so don haka zan saurara musu ba zan shiga lamarin ba sai dai in tura ta kai bango".
miƙewa Roshan ya yi yana cewa "Ku tawo mu je sashina Muzaffar; gaskiya Mommy ya kamata Bhaba ya dawo, na gaji da aiyukan nan wallahi."
murmushi kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba don ta san ya riga ya dawo É—in.

Da daddare.....
Tafasa da zaɓalɓala kawai Zuciyarsa take yi, ture wayarsa ya yi zuwa gefe yana jin kamar ya buga ta da ƙasa, ya yiwa Leelah kira ya fi a ƙirga amma duk tana waya, wadda ya tabbata da banzayen samarinta take yi.
"Wai me ya sa ta kasance haka ne?" ya jefawa kansa tambayar da ba shi da amsarta, kamar ya ɗora hannu a ka ya dinga ɓarza kuka haka yake ji, jikinsa ya ɗauki wani irin zafi kamar wanda aka raɓa a wuta.
Har ya haƙura da sake kiran nata amma sai ya kasa jurewa, ƙara janyo wayar ya yi ya tura mata kira, cikin sa'a ta ɗauka gami da sallama cikin wata siririyar murya. Duk da ya san ba don shi ta yi ba amma sai ya tsinci kansa da jin daɗi, da a ce kullum haka take a nutse da ya more, "Yanzu kin kyauta kenan Leelata?" ya yi maganar kamar an yi masa dole.
Sai da gabanta ya yanke ya faɗi har ƙasa, tabbas ba za ta manta da muryar nan ba duk da ba yadda ta saba jinta ta ji ta a yanzu ba, lallai in haka ne ta kwaso wa kanta Bala'i da Ƙara'i ta bakin Salim, "Waye kai??" ta tambaya cike da son tabbatarwa, "Bawan Allahn da Sonki ya yiwa Mugun harbi ne, Na kamu da ciwo wanda ke kaɗai ce maganinsa Leelah!, ki yi haƙuri za ki ga kamar na ƙi jin maganarku ne, na yi ƙoƙarin nesanta kaina da ke sai na ji ba zan iya ba, ba ni na ɗorawa kaina sonki ba don haka ba zan iya yayewa kaina ba; ki temaka min kar ki bari rayuwata ta salwanta!". ya ƙarasa maganar kamar zai fashe da kuka.
Shiru ne ya ratsa tsakani na ɗan lokaci kafin Leelah ta katse shirun da cewa "Ka gama???" "Indai magana ce a kanki ban ga ranar da zan dena ba Leelah! indai za ki saurareni zan iya kwana ban gaji ba." murmusin rainin hankali ta yi kafin ta ce "Ba ka da darajar da zan iya zama ina saurarenka sai dai ka je ka nemi gajarabul irinka, ni ina da waɗanda zan yi magana da su masu kima da Daraja ba mara aji mara Zuciya irinka ba; Kar ka ƙara kiran wayata tinda ba ta sa'arka ba ce, Yaro ɗanye cakal da kai sai shegen naci da rashin Zuciya! mewtch!!" ta ja tsaki gami da kashe wayar.
Rintse idanunsa ya yi da ƙarfi yana faɗin "Ya Salam!, Allah ga ni gareka!". wani irin zafi Zuciyarsa take yi, da zai iya da ya yi kuka ko zai samu sassauci.

"Ki ji fa Haja wannan ɗan shegiyar ne ya kuma kirana, ni dai ina ga da Maye na yi gamo!" ashar Haja ta zunduma cike da mamaki ta ce "Shi wai duk abinda muka yi masa bai haƙura ba?? tab"! ai kuwa sai mun yi da gaske, Talakawa fa tsinannen naci garesu da taurin kai ga uwa uba rashin Zuciya". "Ke ma fa Talakar nan ce Ƴar Talakawa, wannan kalmar ba ta dace ba, a dinga sarrafa Baki, da ma cewa kika yi wasu Mutanen". Salim ne ya faɗa yana watsa mata harara, tsaki kawai ta ja ba tare da ta ƙara magana ba don ta san Salim ya fi ƙarfinta indai wajen tafiyar harshe ne.

Yana fitowa ya yi tozali da Bhaba a Falo, yana zaune yana danne-danne a Laptop, a gefensa Khushi ce a rakuɓe sai surutu take zuba masa, suna yi suna dariya.
Da sauri ya ƙarasa yana cewa "Bhaba kai ma surprise??" Dariya Bhaba ya yi gami da cewa "E mana, zo ka ba ni labari ya-ya ka kwana?" kusa da shi ya zauna gami da kwantar da kansa bisa kafaɗarsa, zazzafar iska ya furzar kafin ya ce "Bhaba kusan ba lau ba, na kwana ina tunani da mafarkai, amma dai kana Lafiya ko Bhaba?, ya kamata ku dinga sanar min kafin ku tawo fa, haka jiya kawai sai na dawo na tarar da Maa a gida." "Ina lafiya Aliyu, kar ka damu za mu dinga sanar da kai in sha Allah, ya kuma fama da ƙanwarka? na shiga Masana'antu na ga ko'ina komai yana tafiya daidai, ina ƙara yabawa da ƙoƙarinka Ɗana." Khushi ta ce "Wai Bhaba har wata ɗawainiya yake yi da ni?" Murmushi Roshan ya yi yana cewa "Share wannan Tsarabar Indian Bhaba, Na gode da yabawarka, dama fa ina da maganganu da yawa har zan biyoka inda kake sai na haƙura". "Yanzu ai ga ni, ina saurara." "Abin sirri ne ba na so wannan Ƴar Madabon ta ji." ya faɗa yana dariya, turo baki ta yi gaba tana cewa "Ai ko an yi a gefe sai Bhaba ya faɗa min, ka san dai tsakaninmu Amanatun Amana!" "Bari in kwanta ta wuce!" Roshan ya faɗa gami da sunkuyawa, "Wai kana nufin Ƙarya nake yi!!!" ta faɗa cikin ɗaga murya tana zaro masa gwala-gwalan idanunta.
"Ni ban ce ba kawai dai na ji ta tawo ne da girmanta kamar za ta lamutseni. "Ka ci sa'a yanzu safiya ce da sai na yi gutsi-gutsi da harshenka" ta faɗa tana huci, "To a bari sai da rana mana?" "Ko kula ka ba zan yi ba!" ta yi maganar tana juya masa ƙeya.
Shi dai Bhaba ci gaba ya yi da aikinsa tare da yi musu dariya.
Chapter 10 · 0% Book details