← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 35

Sashe 12

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare suka fito Haydar ya yi saurin bin bayan Bhaba yana ƙara maimaita masa buƙatarsa, banza ya yi masa ya shige Motarsa ya bar Companyn.

Aliyu ma wajen ta shi Motar ya nufa yana shirin shiga Haydar ya ƙaraso wajen yana hayaƙi.....
"Ba dai junin ka Munafurci ba? to wallahi za ka gane na fika iyawa, ka je ka zuga shi ka yi bakan-bakan akan komai na shi ba wanda yake kalla da Mutunci sai kai sai Uwarka, to wallahi sai na yi maganinku!!" Zuwa yanzu abin na shi ya fara tunzura Aliyu, bai taɓa biye masa sun yi sa'insa ba bare faɗa, ko da wani ma bai taɓa yi ba bare ɗan uwansa, a yanzu kuwa ji yake ko dakuwa ce zai iya buɗawa a yi.
"Na baka haƙuri ka dena bi nan da sharri, ni tafiyata zan yi, sai ka je ka yi duk abinda za ka yi ina jiranka!. a fusace ya ce "Ni kake gayawa haka? ai kuwa za ka gani, wallahi wataran sai na hana ka rintsawa da sunan bacci, shege Ɗan gidan taƙi zama, Ɗan me jan kunne Juyayya me zubin Karuwai, ". idanunsa da suka canja launi sabida tsabar ɓacin rai ya zuba masa, jikinsa har karkarwa yake yi "To Alhamdulillahi tinda Ita juyayyar Biyu ta haifa ita kuma wadda ba a juye take ba ta samu ɗaya, ka ga ko a nan ta farke ta ƙara!!, kuma duk abinda za ka yi ka guji sako Mahaifiyata a ciki, haƙurina ya yi low wallahi yanzu daidai nake da cin Uwarka!, Shege Ɗan Amarya!!!!".

SHARE FISABILILLAH

*Samu Ƴancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632*

*©️INDO*[11/21, 8:48 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
8

©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*

*G.W.F*

"To Alhamdulillahi tinda Ita juyayyar Biyu ta haifa ita kuma wadda ba a juye take ba ta samu ɗaya, ka ga ko a nan ta farke ta ƙara!!, kuma duk abinda za ka yi ka guji sako Mahaifiyata a ciki, haƙurina ya yi low, wallahi yanzu daidai nake da cin Uwarka!, Shege Ɗan Amarya!!!!".
Sosai maganar ta daki Zuciyar Haydar, ya yi kansa a fusace yana cewa "Ni kake cewa ɗan Amarya? wallahi zan canja maka kammani a wurin nan!!!!" "Na faɗa, in ka isa ka ce ba Amaryar ba ce ba mana!, banza Fasiƙi, Mazinaci, Ɗan Giya!!" Kukan kura Haydar ya yi yana shirin shaƙararsa MD ya doka masa tsawa, dakatawa ya yi yana huci gami da cewa "Ni wannan zai kira Mazinaci!!?? wai ni sa'an wasan shi ne Dan uwarsa?!!" "Na faɗa mazinaci !!!,,, in ka yi Zuciya ka dena!!; Kuma ka dena sawa a ranka ka girmeni, na tabbata da Haihuwar wuri ta yi sai dai ka kirani Ubanka don na zama Babban Yaya!!"
sake haurowa ya yi yayo kansa zai haushi da duka MD ya yi saurin riƙeshi a tsawace ya ce "Wai ba haƙuri nake baka ba??, me ya sa ba ka jin magana ne??" Aliyu ya ce "Da ka barshi ya zo mu buɗa in nuna masa Ƙarfin Mutum me hankali daban na ɗan shaye-shaye daban, wallahi da sai na yi maka Shegen Dukan da ba za ka gane Gidanku ba!!!" A fusace MD ya ce "Ashe kai ma ban isa na faɗa ka ji ba Aliyu?? ka duba fa ka gani ko'ina Mutane ne suka taru suna kallonku!, ina ganin na isa da ku ashe ba haka ba ne??" Ƙwafa ya yi kafin ya ce "Na haƙura dai sabida kai, amma wallahi da ba ka wurin nan sai na yi masa dukan da ba zai ƙara marmarin yin faɗa da wani ba." MD ya ce "Na san ai kai za ka ji maganata dama, maza ka yi tafiyarka!" Fizgewa Haydar ya yi yana cewa "Ni kuma wallahi sai na cirewa Yaron nan raini!!, ba zan taɓa haƙura ba sai na ga na yi masa lahani wallahi!, kuma indai ka shiga Motar nan ba za ka je inda za ka je lafiya ba." Rai a ɓace MD ya ce "Kar ka shiga Aliyu, tsaya ni zan kai ka gidan da kaina sai in ga tsiyar da zai iya yi!!, kai Manager maza ka sa wannan shashashan a Mota a fitar da shi daga Companyn nan!!" ya faɗa yana kallon Manager wanda ke tsaye a gefe yana kallon Ikon Allah. Amsawa ya yi kafin su ƙaraso da shi da wasu daga cikin Mutanen wajen suka fara kiciniyar janyeshi.

ko da suka kama hanya tsaki kawai Aliyu yake ja, ya so an barshi ya yi masa ɗan banza duka wataƙila zai dawo cikin hankalinsa.
"Abin fa sai haƙuri Aliyu ka dena damun kan ka In sha Allah komai zai wuce" MD ya faɗa cike da damuwa, jinjina kai Aliyu ya yi gami da cewa "Ba komai, ta wuce!" ba haka Md ya so ji ba amma sai ya maze ya ƙara marairaice fuska ya ce "Na rasa me ya sa shi kwata-kwata ba shi da hankali, bai yi halin Mahaifinku ba, kuma na san duk asalin abun daga Mamarsa ne, ta bar yaro haka sakaka ba tarbiya bai san mutuncin kansa ba bai san mutuncin wani ba, gashi na lura ba ya ƙaunarka kwata-kwata, yanzu ka ji irin munanan kalaman da ya dinga faɗa a kanka da Mamarka." a ƙagauce Aliyu ya ce "Shi irin nasa tunanin kenan, amma wata rana in Allah ya yarda zai dena." "Anya kuwa zai shiryu?, ai ya riga ya yi nisa ba ya jin kira, kana ji fa cewa ya yi in ka shiga Motarka ba za ka je gida lafiya ba, in ba sa'a ba wani tuggun suka shirya maka, shi neman kashe ka ma yake yi, gaskiya ya kamata ka tashi tsaye."
"Kawu don Allah saukeni a nan akwai inda zan je" Aliyu ya faÉ—a cike da takaicin surutan MD É—in.
Md ma takaici da baƙin ciki ne suka kama shi, ya rasa wane irin yaro Allah ya haɗa shi da shi wanda sam ba ya ɗaukar zuga ko tunzurawa, gashi ya lura shi bai ma fiye son a faɗi laifin ɗan Uwan nasa ba. Jin ya yi shiru ya sa ya ƙara cewa "Ina magana fa, akwai inda zan je a saukeni a nan." "Wai kai wane irin Mutum ne Aliyu? wai ba ka ga ko fita kai kaɗai ba a so ka dinga yi ba sai da Masu tsaronka?, kai yanzu a nan kuma ba motar da za ka hau gare ka ba" "Zan ƙarasa a Napep, ai Allah ne me tsare bawansa ba wasu ba. ''Yanzu kamar kai sai a gan ka a Napep? ka dinga nemawa Iyayenka Mutunci mana!" "Kawu Please Ka barni na yi abinda nake so, ni waye in ba Mutum ba? ko a kan iska ake so in dinga yawo?" Faaaa!!!!! MD ya yi gefen Titi da Motar ya tsaya, a fusace ya ce "Ana so a kare lafiyarka kai kuma kana zillewa har da faɗa min magana, to sai ka tafi ai."
"Ka yi haƙuri" kawai ya ce gami da ɓalle Murfin Motar ya fita, shi a rayuwarsa indai za ka aibata wani sannan ka yabe shi to fa ba zai taɓa jin daɗi ba, shi kuma MD halinsa kenan.

Yana yin gaba ya ɗauki waya ya turawa Hajiya Habiba kira. Ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗauka da ta ga shi ne, ko sallama bai yi ba ya fara cewa "Gaskiya Hajiya Habiba kina da sakaci!, yanzu ki duba ki ga Yaron nan Ƙanin Haydar ne amma kar ki ga irin zagi da cin Mutuncin da ya yi masa, da har dukansa zai yi sai da ƙyar muka samu muka hana shi." Wani mashin baƙin ciki ne ya soki Zuciyarta, a fusace ta ce "Ina Almustafan? a gabansa yana kallo hakan ta faru ko? ai duk laifinsa ne wallahi ya fifita wannan Ɗan iskan a kan babban Ɗansa, ai Babba babba ne duk inda yake." Da sauri MD ya ce "Ina!!, ba ya wurin, amma dai duk shi ya assasa fitinar don yana fita daga Kamfanin sai ga Aliyun ya zo ya fara tayar da hayaniya, bai kamata a ce Haydar ne babba kuma ana yi masa irin wannan ba, ai sai Duniya ta zage mu, wallahi Hajiya Habiba kar ki ga irin Zagin cin Mutuncin da ya yi miki ke da Haydar ɗin." "Dole zan ɗauki Mataki MD na gode maka da kake tunatar da ni, don Allah ka ci gaba da sa min ido a kansu.
Tana gama faɗen haka ta katse wayar tana huci, ya zama dole ta san yadda za ta yi ta fara yun Yaƙin gaba-da-gaba da wannan Matar tinda ta sheƙa na ƙarƙashin ƙasar ta ga ba tsaba.

Cikin farin ciki da murna ya turawa Bhaba kira, cikin sa'a ya samu ya ɗauka. Abinda ya faru da wanda bai faru ba ya gaya masa, kamar yadda ya lintumawa Mami Ƙarya akan Aliyu haka ya muzanta Haydar ɗin a wajen Bhaba.
Sosai ransa ya ɓaci, suna yin sallama ya kira Mami ya ƙare mata ƙalau, hakan ya ƙara tunzura Zuciyarta.

Murmushin mugunta MD ya yi yana cewa "Ai sai na haɗa muku Wutar da ba zaku iya kashe ta ba, Almustafa yana tsaye za a ji ya faɗi daga haka sai Ƙiyama; dole sai na cimma Ƙudurina a kansa!!"

Roshan kai tsaye Gidan su Irfan ya wuce don yanzu komawarsa gida haÉ—ari ne babba, da zarar Ummansa ta gan shi a burkice shi kenan hankalin Gidan ya gama tashi.

Ba ƙaramar Murna Leelah ta yi ba da ta ga Daren Jiya bai kirata ba har gari ya waye, sai murna take yi tana faɗawa Ƴan Uwanta sun yi maganinsa.
Chapter 12 · 0% Book details