Sashe 13
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana zaune a garden kan wata haɗaɗɗiyar Kujera ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya tana taunar cingam, Azaan yana zaune a gefenta yana yi mata sambatu a kan Khushi ta yi masa banza kamar ba da ita yake yi ba.
Gajiya ya yi ya fara fusata yana cewa "Ni wallahi tinda ba za ka iya yi min komai ba zan yi da kaina, kuma kar wanda ya ce ban yi daidai ba." dariyar da ta fara yi ce ta dawo da shi cikin nutsuwarsa, ya zuba mata ido yana mamakin dariyar. "Ni fa na ce zan yi ba kai ka sa ni ba, don me za ka zo ka takura min??, na ce zan yi maka to ka jira lokaci kawai " "Ni fa Mammi ba na so ki yi abinda za ki cutar da ita don ni sonta nake yi." ido ta zuba masa na ɗan lokaci kafin ta kawar da kai ta ce "Ba na jin akwai wata rana da za ta yi maka bayan ka gama amfani da ita, bai kamata ka so ta ba don ita ma ba za ta taɓa ƙaunar ka ba; babu wani so da zai haɗamu da waɗannan Mutanen sun riga sun tarwatsa shi tin farko! don haka ina so ka cireta daga Zuciyarka, koda kun yi Aure to ba me tsawo ba ne ka dinga tuna hakan!". Jikinsa ne ya yi sanyi liƙis, duk da shi ma ba shi da burin Aurenta har ƙarshen rayuwarsa amma yana jinta har cikin ransa kuma ba ya son abinda zai cutar da ita, a wani gefen na Zuciyarsa kuwa yana jin kamar in ya kashe kwaɗayinsa da ita zai ji ta fice masa a ka lokacin ba shi da wani hurumi da ita zai iya zubawa Mammi ido ta yi duk abinda za ta yi.
"Lokaci ya kusa wanda zan sa Moonath zubar da hawaye, sannan na lalata rayuwar wanda ya Lalata tawa rayuwar." cikin yanayin sanyin da jikinsa ya yi ya ce "Wai Mammi meye tsakaninku da su haka? waye ya Lalata rayuwarki??" murmushi me cike da manufofi ta saki gami da shafar kumatunsa sannan ta ce "Lokacin da za ka sani bai yi ba, ka tashi ka je ka yi sha'aninka"
Ba don ya so ba ya tashi ya bata wuri Zuciyarsa cike fal da tambayoyi.
Yau Roshan ya fara zuwa Aiki a garage tin Misalin ƙarfe biyu ya je sai Ƙarfe biyar ya nemi damar tafiya Oga kuwa ya Amince don girmama shi yake yi sosai, ko aiki kasa sa shi ya yi sai da ya takura a ba shi abin yi tukunna, kuma ya zage ya yi aikin da iya ƙarfinsa. Kuɗin Aikinsa ya bashi daidai da yadda ya yi sannan suka yi sallama ya ɗaware.
Bai zame ko'ina ba sai Gidan su Leelah.
Ya yi wani kicin-kicin da shi kamar an ƙwatoshi daga bakin Kura. Irin Yadin ranar ne ya saka amma yau fari ne, duk ya ɓaci da datti na aikin Mota, shi kansa ma ya yi duhu.
Rabi'a, Haja, Ikilima, Baby, Nana, Leelah.
Daidai lokacin suka fito daga Gida kowacce ta sha kwalliya, kamar ba gobe, Ikilima, Rabi'a, Haja, duk Riga da Wando ne a jikinsu wanda suka yi bala'in kama jikinsu, sai wani ɗan siririn mayafi da suka zagaye kai da shi, Leelah kuwa irin ɗan siririn siket ɗin nan ne a jikinta, ita ma ya ɗame ta sosai sai ɗan ƙaramin mayafi da ta yana a kai ita ma, Baby da Nana kuma Ƴar Atamfarsu suka sa sai dai su ma ɗinkin ba na kima ba ne.
Wani mugun takaici ne ya tsire Zuciyarsa sa'in da ya ganta ta fito a haka ko Kunyar Allah ba ta ji bare ta jama'ar gari, gashi Unguwarsu ba a raba ta da Mutane ga Matasa ƴan zaman sa ido Ƙungiya-Ƙungiya.
Turus suka tsaya suna kallonsa cikin mugun mamakin sake ganinsa.
"Tirƙashi!! yau ga Maye!" Rabi ta faɗa tana riƙe haɓa, bai ma san tana yi ba don idanunsa na kan Leelah wadda kishinta yake neman tarwatsa masa Zuciya.
Ita kuwa ta kasa ko ƙwaƙƙwaran Motsi sabida mamaki, ba ta taɓa haɗuwa da Saurayi me naci irinsa ba, kowa da ya zo ko bai san halinsu ba in suka yi masa sau ɗaya to zai samu masu faɗa masa gaskiya akan kar ya dawo don gaba sai ya fi haka, sai gashi shi gori da zagi da cin Mutunci ba su sa ya sauke bakarsa ba.
Kallon kallo suke yiwa juna kowa da irin tunanin da yake a Zuciyarsa.
Cikin nutsuwa ya taka zuwa daf da ita yana ƙara zuba mata narkakkun idanunsa, cikin muryar da take ƙara bayyanar da damuwarsa ya ce "Yanzu Leelah a haka za ki ratsa duk Mazan da suke taruwa a Unguwarku?, Don Allah ki koma ki sauya wasu kayan, wannan sam ba su dace da Mace me Daraja irin ki ba."
Dogon tsaki ta ja cike da takaicin jin abinda ya faÉ—a, wai har wannan Kalan Hanjin ne zai zo yana nuna Kishinta sabida tsaurin Ido?.
"Dakata Malam, nawa ka bayar na Sadaƙina?, kai idan Gobe ake shirin Ɗaura mana Aura in ka haifu ka ce ka fasa don na fita a haka, wai kai Shekararka nawa ne ma dududu da kake zaƙewa a kaina? na tabbata na girmeka don haka ban ga alamun zaka isheni rayuwa ba." "Ko ban bayar da Sadaƙinki ba ai ni me sonki ne, bare ina sa ran wataran zan bayar, kin ɗauki soyayya tamkar tatsuniya ko? hala ba ki taɓa tsintar kanki a cikin irin halin da nake a yanzu b...." katse shi ta yi da cewa "Ka ga! ka bar ƙofar gidan nan ko in sa a yi maka shegen Duka wallahi!" ta yi tsaki gami da ci gaba da tafiya tana cewa "Ku gama min da shi sai ku biyo ni" ai kuwa kamar jira suke yi suka yi masa caa!!! kowacce tana kwalɓa masa baƙar magana.
Rabi'u ne ya shigo Gidan da gudu yana cewa "Salim!! zo ka gani, ga wannan Saurayin Leelan ya dawo yanzu su Rabi'a suna can suna yi masa Jaraba". Da ƙyar ya miƙe daga sunkuyon wankin da yake yi yana riƙe Ƙugunsa gami da cewa "O'o ni Sa'adatu Sa'ar Mata, yanzu shi wannan Ɗan sallamammiyar dawowa ya yi?, kai mu je in gansa, last warning zan yi masa." yana ƙoƙarin tafiya Salma ta riƙe masa hannu cike da takaici ta ce "Wallahi Salim in ka tafi ba zan ci gaba da tayaka wankin nan ba, don ka samu ma ina tayaka shi ne sai ka dinga tafiya kana barina da zarar ka ji Munafurci?" "Haba me wanki da guga!, don Allah ki ƙarasa min zan biya ki kuɗinki, ki haɗa har da wancan da kike bi na" "A'a ni ba na kuɗi nake yi maka ba don Allah nake taya ka, in na kuɗin zan yi maka ina za ka samu ka biya ni?, kawai ka zauna mu ƙarasa in ya so sai ka je ka yi duk abinda za ka yi." "Don Allah ki bar ni in je in yi Ido Huɗu da wannan taɓararren, yanzun nan zan dawo ki ɗan tsaya ki huta."
Momi ce ta fito daga Madafa (Kitchen) tana cewa "Wai ba dai Talakan nan ba ne ya tare mini Ƴa?, GRA fa za ta tafi shine Munafuki ɗan baƙin ciki zai tare ta??" "Sa ranki a inuwa Momina ai yanzu zan fita in yi miki maganinsa" Salim ya faɗa yana tattafa hannaye.
"A'a zuwa da kai ya fi Saƙo, bari in je da kaina" ta faɗa tana yafitar mayafinta akan igiya.
Da sauri ya tare ta yana cewa "Haba Momi kar ki bayar da mu mana! ki bar dai masu halin fita su zage siriki su yi amma ke ban sanki da haka ba!". "Kai ubanka! na ce ubanka!, ko ba na yi yau zan fara don na lura Maye ne yaron nan ba zan bari ya lashe min kurwar Ƴa ba, ba abinda za ta yi da shi don haka dole sai ya bar ta ƙwalamamme!"
Innayi ce ta ƙaraso wajen tana cewa "Ke Dije ba na son iskanci, ki bar Yara su yi mana, ke ina ganin ba kya fita ki yi faɗa da Sirikan shi ne yau za ki fara?, ai gwara ki bar ni ni da nake Kaka in fita in yi duk abinda zan yi, kin san dai ko Aure aka tashi yi in ban amince ba iyayen Ƴar ba za su Amince ba, don haka ki bi ni a hankali; kai Jikana tawo mu fita" ta ƙarasa maganar tana kallon Salim, ba don Momi ta so ba ta cire gyalen ta rataye ta fara zazzagar masifa tana zage Aliyu.
Lokacin da suka fito tuni su Ikilima sun saita masa hanya ya ƙara gaba.
Masifa Salim ya dinga yi yana cewa an ci da rabonsa.
Nan fa suka kafa zancen kowacce tana faɗen abinda za a yi masa in ya ƙara dawowa....
SHARE FISABILILLAH
*Samu Æ´ancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira ÆŠari Uku 300 kacalâ˜ºï¸ Domin Ƙarin bayani 👉🽠09079885632*
*©ï¸INDO*
[11/25, 8:42 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
9
©ï¸
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*
FREE PAGE...........
Haka ya koma gida jeme-jeme ransa a dagule. Tinda Maa ta kalleshi sau ɗaya ba ta ƙara bi ta kansa ba, tamkar ba ta damu da halin da ta gan shi ba, a ranta kuwa ta gama Ɗaura niyar yi wa Leelah da danginta abinda har abada ba za su taɓa Mantawa ba, tana ji tana gani wai Ɗan da ta fi so da ƙauna fiye da komai a Duniya ya zo gabanta yana kuka akan wata Ƴar Matsiyata.
Khushi ce take ta ƙoƙarin rarrashinsa duk hankalinta ya gama tashi, yana yin Sallar Magrib baccin wahala ya yi awon gaba da shi.