Sashe 25
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Khushi ta ce "Ba ka gabatar da ni ba fa". "Okay Sorry" ya faɗa kafin ya mayar da kallonsa kan Salma, "Wannan ita ce Khushi, Ƙanwata ce ita kaɗai na Mallaka duk Duniya, kuma na fi shaƙuwa da ita fiye da kowa, haka kuma ina matuƙar Ƙaunarta, tana da tsokana sosai sai kin yi haƙuri da ita.
Ƙasa ta yi da kai tana wasa da yatsun hannunta, kalaman nasa sai yawo suke yi mata a ƙwaƙwalwa, Ta yaya zai nuna mata Baturiya kuma ya ce Ƙanwarsa? ko dai ya ɗauka ta haukace ne??.
Khushi ce ta katse mata tunanin, "Ki shirya kar dare ya yi sosai, ni bari na je wajen Irfan, ba zan iya zama a nan ba".
Ba Aliyu kaÉ—ai ba har Salma sai da ta raka ta da ido.
Ganin jikinta ya ƙara yin sanyi ya sa shi cewa "Share waccan tsarabar Indian don Allah, maza shirya mu wuce jiranmu ake yi". ƙwal-ƙwal ta yi da ido za ta fara kuka, cikin rawar murya ta ce "Ban san ina za ka kai ni ba, don Allah ka ƙyaleni a nan". idanu ya zuba mata kawai ba tare fa ya mayar mata da martani ba. Gabaki ɗaya ta sakankance don har ta ɗauka ma ya ƙyaleta kawai sai ji ta yi ya rungumo ta yana ƙoƙarin zuge zif ɗin rigarta. Da iya ƙarfinta ta fizge jikinta na rawa, "Ka bari zan sa da kaina" ta faɗa tare da fashewa da kuka.
"Okay zan je in dawo" ya faÉ—a tare da tashi ya nufi hanyar fita.
Yana fita ta canja kayan cikin sauri don gudun kar ya dawo, iya rigar ta saka ta ture sauran ababen Adon don ta lura ma ba ta san ta ina za ta fara saka su ba, gashi tsoronsu ma take ji.
Ba ta daɗe da komawa ta zauna ba ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, kasa amsawa ta yi sai ma ƙasa ta yi da kai tana ficincina idanu, ta rasa me yasa yake yi mata Mugun kwarjini, ko muryarsa ta ji sai ta ji wani iri a jikinta.
Ƙarasawa ya yi kusa da ita ba tare da ya ce komai ba ya ɗauki danƙareriyar Sarƙar ya fara ƙoƙarin ɗaura mata, ba ta yi gardama ba don ko motsi kasa yi ta yi har sai da ya gama ɗaura sarƙar sannan ta samu yin ƙwaƙƙwaran numfashi, hannunta ya riƙe ya zura mata awarwaro sannan ya damƙa mata ƴan kunne ya ce ta saka, ba musu ta karɓa ta fara ƙoƙarin saka cikin sanyin jiki.
Paayal ya ɗauka gami da durƙusawa ya ɗauki ƙafarta cilak ya ɗora kan cinyarsa ya fara ƙoƙarin ɗaura mata.
Kasa saka ɗankunnen ta yi sabida jikinta da yake wata irin hajijiya gabaɗi ɗaya sai ta rasa nutsuwarta sai aikin binsa da ido take yi cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa, har ya kammala ba ta iya saka ko guda ɗaya ba, ganin ba zai iya jira ba ya sa shi karɓa ya saka mata.
Da kansa ya ƙarasa shirya ta sannan ya umarce ta da tashi su tafi, da ta fara gardama sai da ta ga ya ɓata rai tukunna ta saduda ta bi shi.
Sai da hantar cikinta ta ƙara yin kuka ganin jerin Motoci sama da goma a layin wai kuma duk ita aka zo ɗauka, ta riga ta saduda an sayar da ita, don dai ba yadda za ta yi ta tsira shi ya sa kawai take bin sa sawu da ƙafa.
Sai da ta fara shiga sannan ya rufe ya zagaya kusa da Khushi wadda take ta aikin kuka ya fara rarrashinta. Gabaki É—aya ya kasa gane kanta, sai kuka take yi ba tare da cikakken dalili ba, tin yana tambayar abinda ke damunta har ya gaji ya fawwala wa Allah.
Tin daga waje Gidan ya
sha ado, ga haske ta ko'ina.
Zare ido kawai take yi gabanta na faÉ—uwa, ji take kamar ta kurma ihu sai dai ko ta yi ma ba ta da matemaki sai Allah don haka ta ci gaba da jera addu'o'i.
Sai da Motocin suka tsaya sannan Aliyu ya fito ya zagayo inda take, buɗe mata murfin ya yi yana cewa "Za ki iya shiga da ƙafarki ko kuma sai na kai ki da kaina??" da sauri ta ce "Zan iya!" gefe ya matsa gami da cewa "To Bismillah" fitowa ta yi cike da tsoro da fargaba, ido ta ci gaba da zazzarewa tana kallon ko'ina, hannunta ya riƙe tare da cewa "Mu je na raka ki!" bin sa ta yi kawai don gudun ta yi gardama ta ji an harbe ta ko a yanka.
Abubuwan ado da take ta famar tozali da su tin a hanya suka ƙara rikita lissafinta. Ba ta ƙara ruɗewa ba sai da ta ji Saukar furanni a jikinta ga wata irin hayaniya gami da waƙa suna tashi a cakuɗe.
Wani mugun kuka ta saki gami da ƙanƙame hannunsa jiki na rawa, "Don Allah ka mayar da ni wajen su Umma, don Allah kar k......" Katse ta yayi ta hanyar sungumarta ya rungumeta cikin ƙirjinsa, sai buɗe ido ta yi ta ganta a tsakiyar Mutane ya direta, su kuwa duk idanunsu na kanta, ita dai ta ga sai fara'a suke yi suna surutu amma ba ta san me suke cewa ba, shi kuwa Aliyu ta ga sai dariya yake yi.
"Barka da zuwa Ƴata!" wata Mata ta faɗa cikin sakin fuska, ta ɗan ji daɗi don ko babu komai ta samu me irin Yarenta.
Aliyu ya ce "Wannan ita ce Mama Aminatu, Ƙanwar Bhabana ce."
Ta ji shi amma sam ba ta fahimci inda ya dosa ba, sai ƴan ƙusha-ƙushin kukanta take yi.
Mama Aminatu ta kama hannunta tana cewa "Tawo Mu je ki ga Dangi". kam!! ta riƙe hannunsa tana binsa da kallo alamar dai ba za ta bar shi ta bi wata ba. Mama Aminatu ta yi dariya gami da cewa "Kai kaɗai ta sani Aliyu!, ka zo mu je tare". Amsawa ya yi sannan ya bi bayansu, Mama Aminatu tana jan ta ita kuma tana jan shi.
Tin daga kan Mutanen da suke kurkusa har na lungu da saƙo sai da suka bi suka gaisar sannan Mama Aminatu ta zaunar da ita kan wata lafiyayyar sofa.
Duk yadda ta kai ga maƙale masa sai da ya sulleɓe ya barta da Mutanen da take matuƙar tsoro, don ma ta ji wasu suna yin Hausa gashi sun ƙi ƙyale ta sai famar yi mata magana suke yi.
Tana nan zaune suka dawo suka ƙara salgafarta wai za ta gaisar da Uwar Miji.
Sai da suka fita babban Falo suka ci burki da ita tare da nuna mata jerin Mata sun kai su Goma ko fi duk fuskarsu a lulluɓe sai idanunsu kaɗai ake gani, suka ƙara mata da bayanin ta zaɓi Uwar Mijin nata a ciki, sannan duk wadda ta zaɓa za ta je ne ta durƙusa a gabanta.
To fa!!!! ana dara ga dare ya yi..............
sai yanzu ta ƙara tabbatarwa ta ga rayuwa ganin idonta, to yanzu a cikin Mutanen nan kowacce fuskarta a rufe ta yaya za ta iya gane Uwar Mijin? ko ƴar canke-canke za ta yi??
Umma Aisha ce ta ƙwarara mata gwiwa gami da kwantar mata da hankali.
Duk inda ta juya sai ta ga kowa ita yake kallo har shi kansa Gogan nata, yana tsaye cikin Abokansa wanda duk kusan kansu ɗaya sai dai akwai Hausawa Akwai Indiawa har da Turawa, da ya kalleta sai ya tuntsire da dariya don ba ƙaramin tsinka masa malejin daɗinsa take yi ba in ya ga tana firgicewar nan.