← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 35

Sashe 14

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni fa wallahi ko ta halin yaya ne sai na ga bayan Aliyu tinda ke kin kasa yin komai!!, idan na ɓatar da shi sai Daddy ya dawo kaina tinda yanzu ba wanda yake gani sai shi!" Aliyu ya faɗa a fusace kamar zai daki Mamin ta shi, cike da masifa ta ce "To wai Uwar me kake so na yi Haydar?, na yi duk iya ƙoƙarina amma abin ya ci tira, tin wata rana da na taɓa Asirce Almustafa ya zamana ba wanda yake saurara sai ni ta shiga ta fita ta karya Asirin tin daga nan ban ƙara cin galaba a kanta ba, duk wani shiri nawa sai ta tarwatsa shi, ta riga ta zamo min ƙarfen ƙafa yanzu shawara nake yi akan ta inda zan fara Yaƙarta amma kai ka zo kana yi min hayaniya, na fi ka jin zafin abin fa!." "To ni ki zuba min ido zan yi mata halin ƴan zamani kuma za ki gani." "Kai dallah can!!" ta faɗa gami da kai masa hamɓara, "Kai ba ka san wacece wannan shu'umar Matar ba, duk wani abinda kake ji da shi a kan farcenta kake, wallahi ko loma ɗaya ba ka isheta ba, bare kai halin ƙuruciya kawai za ka nuna, ni kuwa a matsayina na uwarka zan yi nazari kafin na san abin yi."
yana shirin yin magana wayar Mami ta fara ƙara, da sauri ta ɗauka tana cewa "Yawwa MD ne".

bayan sun gaisa ya sanar Mata Aliyu ya fara aiki a garage bai kuma san dalilinsa na yin hakan ba, yana da kyau su bincika su gane.
Godiya ta dinga zuba masa don ita a ganinta shi ne me ƙaunarta da yake kwaso zance yana gaya mata.
"Shi ma fa MD ɗin nan sai na ci Uwar Babarsa!" Haydar ya faɗa yana huci, "Shi yasa na ce kai ƙuruciya gareka fa, to MD me ƙaunar mu ne, shi ne yake gaya min duk halin da Aliyun yake ciki har ma da Daddyn naka, in ba shi ɗin ba kuwa wa ka ga yana yi mana haka?, yanzu ma gaya min ya yi wai Aliyun ya fara aiki a garage wai gyaran Motoci, ka ga kuwa ai akwai wata ƙulalliya." "Me?! gyaran Mota fa ??" ya tambaya a kiɗime, tabbaci ta ba shi kafin ya ci gaba da cewa "Lallai wannan Yaron shaiɗani ne, to Uwar me zai yi da gyaran Mota??, ai kuwa wallahi sai na gane dalilin". "To ka ji dai, Ɗan Wahala wai gyaran Mota, yanzu sai ka ƙara tabbatar da shu'umancin uwarsa, ƙila ma ita ce ta sa shi don ta ƙulla mana wani sharrin."

Shiru ne ya biyo baya kowa yana na shi tunanin, wata dubara ce ta faɗowa Mami ta saki murmushin farin ciki sannan ta ce "Ina wannan Abokin nasa Ari??, kai ma ai Abokinka ne ko?" a daƙile ya ce "E Abokinmu ne mana, kuma yana faɗa mana sirrinsu". "To da shi za mu yi amfani wajen gane dalilin, ka same shi ku yi magana, na ji an ce sun samu matsala kwanaki da ya gayyaci Azaan birth ɗin nan, to ka sa shi ya je ya bashi haƙuri har ya jiyo mana komai.
Murmushi Haydar ya saki, sai yanzu ma ya tuna da yin hakan, ashe dai tana da gaskiya da ta ce ta fishi sanin makamar aiki.

A daren ranar Haydar da Ari suka gama magana, kafin gari ya waye Ari ya bawa Aliyu haƙuri tare da nuna nadamarsa a sarari.
Shi kuwa da yake ba shi da riƙo ga haƙuri tuni ya manta da komai.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya ana kwana ana tashi.

Aliyu bai ƙara zuwa Gidan su Leelah ba sai dai yana takura mata da Kira da Message ba dare ba rana ba safiya ba yamma har Asbaha ma bai fasa ba.

A ɓangarenta kuwa yawan nasiha da Tsadaddun kalaman da yake zuba mata tuni sun fara ratsa Zuciyarta kuma sun fara cin galaba a kanta, duk da tana fuskantar zuga daga wajen su Sumayya da iyayensu.
Idan ta yi kamar ta yarda da shi sai su bushe mata kunnuwa.

Tuni Ari ya samu duk abinda yake son samu ya faÉ—awa Haydar da Azaan kasancewar duk layinsu É—aya.
Azaan bai damu akan hakan ba don ba huruminsa ba ne, muradinsa dai kawai ya samu sa'a a kan Khushi.

A ranar Mami ta sanarwa Bhaba cewar Haydar ya samu Matar Aure kuma cikin Sati Uku ko huɗu take so a yi Auren, har da ƙaryar Likita ya ce ayi masa Aure cikin gaggawa.
Kasancewar DR ɗin Bhaba da su Roshan daban nata ita da Ɗanta daban Bhaba bai gane komai ba kuma bai sa a ransa zai yi bincike a kai ba, dama shi ma yana cike da ƙudurin yi masa Auren ko Allah zai sa ya rage rashin hankalin da yake yi.

Washegari
Irin wankan Yamman nan da suka saba yi su fita gantali Unguwar masu kuɗi yau ma sun yi sun fito kenan suka yi alaragab da Mota a Ƙofar gidansu.
"Wow Anti Leelah kalli wata shegiyar Mota!, Allah ya sa wurinki aka zo" Nana ta faÉ—a tana washe baki.
Ita ma Leelan Addu'ar da take yi kenan a ranta amma a zahiri ko gezau ba ta yi ba da sunan ta ga Motar sabida duk iya shegenta tana da aji da kamun kai.
Dukkansu sun kasa tafiya sun yi cirko-cirko sai mokaÉ—e baki suke yi ana gyara salon tsayuwa don dukansu ransu ya biya.
Ikilima ta kasa jurewa ta taka zuwa wajen Motar cikin wai irin taku na rangwaɗa da ƙwarewa ta fannin bariki.
Tin kafin ta ƙarasa ya fito ya jingina a jikin Motar yana zubawa Leelah wani shegen kallo wanda ta kasa gane ma'anarsa, ita ma kallonsa take yi a Zuciyarta tana tsananta addu'a akan ta samu shiga a wajensa, lokaci guda ta ji ya fara tafiya da ɗan sauran lissafinta.

Tinda Ikilima ta ga suna bin juna da kallo baƙin ciki ya kamata ta koma cikin gida tana mis-mis da baki....
Ƙarasowa ya yi inda take tsaye yana sakar mata wani malalacin murmushi wanda ya ƙara narkar da Zuciyarta, surutansa ne suka dawo da ita cikin hayyacinta "Ki yi haƙuri na ga kamar fita za ki yi ni kuma na dakatar da ke!" ɓoyayyar ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta ce "Ba komai, Allah ya sa lafiya". shiru ya ɗan yi yana tunani, shi sam bai iya Soyayya ba bai san yadda ake yinta ba bare wasu ƴan kalamai nata, shi tsakaninsa da mace kawai ya yi sharholiyarsa da ita ya sallameta, gashi ko ƙanwa Mace ba shi da ita bare ma ya san ta yaya ake rarrashinta.

"Da alamu ba ka da abin cewa" ta faɗa tana ƙoƙarin wucewa.
Cikin sauri ya ce "Aliyu Almustafa Naira!, shi ne sunana na z....." katse shi ta yi ta hanyar zunduma ashar ɗin da ta kuɓuce mata, "Aliyu Mustafa Naira???, wai kuma da gaske kake?" farin ciki ne ya lulluɓe shi ganin ta ruɗe da jin hakan, murmushi ya yi gami da cewa "Ƙwarai kuwa, na san za ki yi mamakin ta yadda na sanki; tin da muka haɗu a Birthday ɗin Irfan Mohammad na ganki kuma na kamu da sonki, na kasa jurewa shi yasa na nemo address ɗin ki don ina so ki zamo Matata!" duk yadda ta kai ga iya jan aji yau sai da ya tsinke mata. Murmushi kawai take fafatawa ba ji ba gani, a ranta tana tunanin Da akwai irin wannan alkairin zai zo mata amma wannan Matsiyacin Talakan ya zo ya addabi rayuwarta? me ya sa ma ta yi garajen fara son Irfan? rashin sanin cewa Aliyun da ta daɗe tana son gani zai zo har ƙofar gidansu neman soyayyarta. Tufka da warwara kawai take yi yayin da murmushinta ya kasa ɓoyuwa.

Haydar kuwa shi kansa ya jinjinawa ƙoƙarinsa duk da ya kwana da sanin ba wai iyawarsa ce ta sa ta cikin shaukin nan ba kawai jin daga inda ya fito ne, shi kuwa da yake ba son gaske yake mata ba bai damu a kan hakan ba, in banda ma yana son muzgunawa Aliyu ai wannan ko a Ƴar Aiki ba zai iya ɗaukarta ba yadda ta fito daga wannan gidan me kama da Dandalin almatsutsai.
Taushe Zuciyarsa ya yi ya ce "Na ji kin yi shiru ko ba kya so na ne??" wani ɗan banza kallo irin na yaudara ta jefa masa gami da cewa "Wa ya isa ya ce ba ya sonka?" "Kin amince kenan?" farr! ta yi da ido tana ƙara yalwata murmushinta "Ƙwarai ma kuwa!" ta faɗa tana wani yauƙi da silɓi.
Kamar ya mangareta haka yake ji amma sai ya danne ya ce "Yaushe za mu yi Aure Sweerheart?!" zaro ido ta yi gami da cewa "Aure?! ko gama fahimtar juna fa ba mu yi ba, ka bari zan sanarwa iyayena duk abinda suka ce zan gaya maka."
Yanzu komai dai ya zo ƙarshe, ya faɗa a cikin ransa.

Ƙarya ya shuka mata akan ana jiransa zai tafi, a zahiri kuwa gajiya ya yi da tsayuwar wajen.
Ba don ranta ya so ba ta yarda suka yi sallama ta shige gida, da so samu ne ba za ta gaji da ganinsa ba har sai lokacin bacci ya yi.
Tana shiga ya bawa yara jibgin ledojin da ya yi mata siyayya suka kai mata ciki shi kuma ya fece.

Tuni Gidan ya hargitse masu murna na yi masu nuna hassadarsu a zahiri suna yi, wasu kuma dai suna taya murnar amma ta ciki na ciki.

Isuhu ne ya shigo yana famar zuba faɗa akan halin nasu tare da barazanar duk ƴar da ya ƙara gani ta tafi gantaln yamma ko na dare sai ya ɓallata.
Chapter 14 · 0% Book details