← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 35

Sashe 5

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Imran ne ya ɗaga kiran yana cewa " Yaya Irfan ɗin ba shi da lafiya zazzaɓi yake yi, yanzu ma Mommy ce ta ce na zo na kirashi ya yi breakfast, tinda safiya ta yi bai fita ba" rintse idanunsa ya yi yana furta "Ya Allah!!" "Ko in ba shi wayar?, ya ce kar a dameshi ne!" Imran ya faɗa cikin sanyin jiki.
Da sauri ya ce "Yeah ina buƙatarsa Imran, ka ba shi haƙuri please"

Miƙa masa wayar ya yi yana cewa "Ya ce ka yi haƙuri" "Waye ne?" "Yaya Aliyu ne" da sauri ya karɓa har murmushi na suɓuce masa, "Ya aka yi ne shege ka sa ni zazzaɓin wahala, ya Kushi ta kwana don Allah??, wallahi na kasa yafewa kaina hankalina ya ƙi kwanciya."
Sassanyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce "Kushi tana lafiya tinda da ita kaɗai ka damu, amma fa Umma za ta dawo daga Singapore sai dai in ta dawo ma labarin canjawa zai yi, a kaina za ta samu labari ba a kan Kushi ba; amma ya kamata ka tambayeni lafiyata ni ma!!." ya ƙarasa maganar cikin salon shagwaɓa.
Dariya Irfan ya yi kafin ya ce "To ya ka kwana Yayana!" ɗan tsaki ya yi kafin ya ce ''Ba fa ƙalau ba, ni ma da zazzaɓin na kwana; a cikin baƙinka na jiya na gamu da wadda ta yi zabarin Hankali da mutsuwata, a kanta na kiraka don Allah in ba damuwa ka zo mu haɗe sai mu tattauna, wallahi ina buƙatar ganinta Irfan!, ko a kan kaina na kasa yin tunani sai tunaninta, ka ganni nan ina Company amma na kasa aikin komai har an fara yi min ƙorafi."
Dariya sosai Irfan ya ke ƙyaƙyatawa har sai da Roshan ya ce "Abin dariya na zama ko Irfan? kenan ba za ka iya temakona ba?" Tsagaitawa ya yi kafin ya ce "Abin ne wallahi ya yi min citta, kullum cikin tsinewa masu soyayya kake amma yau kai ne kake ce min wata ta yi zabarin hankalinka, ai kuwa dolenta ta dawo da shi; wai ni don Allah Ƴar waye ita a cikin baƙin nawa? gaskiya ba ƙaramar Ɓarauniya ba ce tinda ta iya ɗaukar Zuciyar Zinaren nan". "Irfan Please ka bari!!, na lura a Mahaukaci ka ɗaukeni da gaske fa nake yi wallahi, in ba za ka iya zuwa ba ka zauna ni zan zo in sameka."
yunƙurawa ya yi ya miƙe yana cewa "Tinda fa na ji Kushi ba ta cikin damuwa na ji sauƙi, ga ni nan zuwa."
Nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce "Ina jira!" daga haka ya katse wayar.
Ruwa kawai ya watsa ya zura Jallabiya ya zabari key É—insa ya fice ko mai bai tsaya shafawa ba.

Leelah tana zaune tana jujjuya Wayarta, duk ta yi nisa a Duniyar tunanin Irfan. Haja ce ta dubeta kafin ta yi dariya tana cewa "Na ga duk kin rikice Leelah wai meye damuwar ne??" Ikilima ta taɓe baki tana cewa "Meye kuwa damuwar, da alama wani take son yiwa Askin Aljihu ya ƙi askuwa". Sumayya ta yi dariya tana cewa "Ai kuwa in haka ne sai dai ki rungumi sabran don wallahi wasu Mazan ba a cin gajiyarsu." Ikilima ta ce "Tab sai dai in ba ki iya abin ba, ai ni wallahi duk ɗan iskan da ya ce ba zai wanku ba ni ma ba zai wankeni ba, akan me zan zauna ina missing yawuna a kansa?" Rabi'a ta ce "Gane min hanya Lima! ai wallahi Leelah ki rufe ido ki yi masa wankin zanin Mahaukaciya ki rabu da shi". Sumayya ta murmusa ta ce "Wannan ai ba ta fita ba ce, ke!!, mace fa aka ce miki, kin san Kaidin Mace kuwa?? kawai dai Leelan ƙaramar Ƴar hannu ce shi yasa ta zauna yake shirin goge mata hadda".
Dariya suka sa me haɗe da shewa, a ƙufule Leelah ta ce "Ba ku san meke faruwa ba ne shi ya sa kuke tunanin haka, ni fa ba wani wanda nake son yiwa Aski, ba ma sai in ya kamu sannan ake Askin ba?, wai jiya ba na je birthday ɗin wani facebook friend ɗina ba? kun ga abinda na gani a wurin nan kuwa?? wallahi sai jiya na gane duk inda nake takawa ma kaɗan ne, Gaskiya shi kanshi Gayen ya haɗu, kun ga yadda aka dinga ɓarnar kuɗi a wurin nan?" Haja ta gyara zama tana zubowa Leelah idanu gami da cewa "Ke don Allah!!, don Allah ba ni labari". Sumayya ta ce "Dama ni ma ina so in tambayeki wai ya aka ƙare na ga har shabiyu ta wuce ba ki dawo ba; ko dai kin samu Me ƴar Mota ne kin bi shi Shan Minti" Leelah ta taɓe baki gami da cewa "Allah ya sittira, ni kadarata ba arha gareta da zan dinga rabawa kowa ba; Kawai Mutanen da na gani masu arnan kuɗaɗe da kyawawan Samari Ƴan hutu su ne suka tafi da hankalina, kin ga wata Yarinya Ba'indiya da ta shigo wajen nan!!? wallahi ke kowa sai da ya girgiza, kin ga wata muguwar shiga a jikinta?!! ke da kin gani kin san Ƴar Naira ce ba Ƴar Tsaba ba, amma gaskiya ni haushi ta ba ni sabida ko kallona Irfan bai yi ba amma da ta shigo duk sai ya dinga nan-nan da ita; Hee!! ai jiya an yi film wallahi!" Rabi'a ta ce "Ni fa wallahi ina Mugun son masu kuɗi ko da a labari ne, ki ga kuɗi yanda ki san satowa suke yi". Ikilima ta ce "Rai da lafiya ai wallahi ni a jikina nake jin ni ba talaka ba ce, kuma sai na yiwa Talauci yankan Ƙauna." Leelah ta ce "Ke dai bari!, ni fa yanzu so nake na samu shiga a wajen Irfan wallahi in kika fara soyayya da wannan kin kere Talauci, don Allah ku ba ni shawara ta ina ya kamata in fara??" Sumayya ta ce "Ke soyayyar zamani fa sai kina bayarwa ake yawan ba ki, amma ba komai da rashin tayi akan bar arha, kina da lambarsa ko?? ai ni Namiji komai taurin kansa a matsayin ɗankwali yake a wajena sabida na san ta yadda zan bi da shi, ke ma sai ka ce ba Ƴar Gidanmu ba har sai kin zauna an ba ki shawara akan wani Ɗan Ƙaramin Yaro, Allah na tuba Maza masu shekaru Sittin ma ni na iya juyasu bare wani under 30 " cikin jin daɗi Leelah ta ce "Allah ya iya miki Anti Summiy shi yasa nake ƙaunarki!!!, ga lambar ta shi ya za a yi?"
"Ki kirashi ki ce masa kira kika yi ki yi masa ya gajiyar taro, da haka sai ki fara janshi da hira".
"To wace irin hira??, ku tsara min abinda zan faɗa don Allah wallahi kwarjini yake yi min, kaina ya kulle baki ɗaya na rasa me zan ce masa, tin ɗazu fa zaman da na yi so nake na kirashi amma na kasa." Ikilima ta ce "Abu ɗan sauƙi! dawo kusa da ni ki zauna" tashi ta yi ta koma kusa da Ikiliman ta zauna tana cewa "Don Allah duk ku matso ku faɗi naku, so nake sai na susuta shi yau ɗinnan"

Da'ira suka yi suka shiga tsara mata yadda za ta yi har da irin karya muryar da za ta yi masa.

"Irfan in ba ka manta ba akwai wadda ta ce maka facebook friend É—inka ce ita, sunanta Leelah har da bodyguard É—inta ta zo" ido a waje Irfan yake kallonsa cikin tsananin mamaki "Kar dai ka ce min wannan tsohuwar mahaukaciyar kake so!??, ni fa na ga kamar kai ne bodyguard É—in nata amma sai na basar sabida na ga ba haÉ—i tsakanin biri da gada, ni fa Allah ya gani ba ta burgeni ba".
"Idan Allah ya so sai haɗin ya samu mana, tinda na ganta da kuma yadda ta yi min magana na gane tana da son ƙarya da son burga, ga uwa uba son cewar ita wata ce ko Ƴar wasu, amma hakan bai dameni ba kawai sai na ji duk ta tafi da nutsuwata, hakan ne ma ya sa na yarda na zamo bodyguard ɗin nata sabida ina son gane asalinta kuma ina son alaƙanta kaina da ita. "Tirƙashi!! aiki ga me ƙareka, to wai a ina ma ka fara ganinta kai?? me yasa kuma duk Ƴan Matan wurin nan masu aji da kima sai ita kaɗai za ka zaɓa? gaskiya da alamu SO bai yi maka adalci ba Abokina.
"Ka san in Allah ya ƙaddara abu ba yadda za a yi, tabbas na kamu da so irin wanda ake kira daga kallo Ɗaya; ka dena raina ajinta ko kimarta, Allah yana yiwa kowane ɗan Adam baiwa ba tare da shi kansa ma ya sani ba, kuma kowane Ɗan Adam yana da Daraja; ni kaina na lura ba cikakken kamun kai gareta ba amma hakan bai dameni ba, kuma tin a daren jiya na sa a raina zan koyar da ita Darasin rayuwa, tayuwu ta dalilina za ta zamo me nutsuwa da hankali kuma kamila; Jiya lokacin da muka iso wajen ta sameni......" labarin yadda suka yi da ita ya bashi tsaf.... bayan ya kammala Irfan ya sauke gwauron numfashi sannan ya ce "Kana da gaskiya hasashen da ka yi mata ni ma shi nake yi mata musamman yanzu da na ƙara ji, kuma da alamu ita ɗin fa Ƴar Malam Shehu ce amma take wannan Fasa kan; ɗazu Imran yake buɗe kyaututtukan da aka ba ni jiya, wai ka san me ta ba ni kuwa?? ashe takarda ce a ciki wadda aka shaƙareta da kalaman soyayya, ni sai ta ba ni dariya ma, ni wallahi ta yi min kaɗan Roshan amma kar ka ji haushina!" ya ƙarasa faɗe yana dariya.

Da ƙarfi ta banko ƙofar Office ɗin ta shigo cikin sauri buzur-buzur...... zumbur Irfan ya miƙe yana binta da idanu ƙirjinsa na dukan shalugude, ganinta a burkice ya fi komai jefashi cikin firgici da tsoron abinda zai biyo baya. Roshan ma zuba mata idanun ya yi Zuciyarsa na wani mugun tsalle..... ba ta zame ko'ina ba sai...............

*Samu Ƴancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal,☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632*
Chapter 5 · 0% Book details