Sashe 1
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[11/19, 10:00 AM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ
*🪻HAƊIYAR GATARI🪻*
1
©ï¸
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*
Alhamdulillah!!, Ina Ƙara Miƙa Godiyata ga Allah Maɗaukakin Sarki. Yadda na fara rubuta wannan sabon Littafi Lafiya, ina roƙon Allah ya bani ikon kammala shi Lafiya.
Bayan *SAWUN KEKE* Ga wani Sabon Salo, Sabon Tsari, Ina Fatan za ku bi ni a sannu domin jin Abinda ke Ƙunshe a cikin wannan Littafi Me Suna *HAƊIYAR GATARI* Kai tsaye Ba lallai ku fahimci me Sunan yake nufi ba, amma indai kun yi haƙurin Bibiya Za ku Fahimta.
Ina Gaisuwa🫶ðŸ½
Takun nan ce dai *INDO*......
Marubuciyar
WATA HANYA
DOGON YARO
IDO HUÆŠU
SAWUN KEKE
TAJMAHAAL
A JINI ÆŠAYA
SIRRIN ƘETA
AAMINAT (Bazawara)
Da sauransu.......................
10/11/2023
Bismillahirrahmanirrahim.
Sassanyar waƙa gami da hayaniya da iface-ifacen Ƴan Matasan Samari gami da Shewar Ƴan Mata ga kuma Surutan MC ke tashi ta ko'ina a cikin Ɗan Madaidaicin Hall ɗin, wanda ya sha Ado da kwalliya da ƙawa ta ko'ina. Duk da ƙarami ne amma sai Masu abin ne kaɗai ke iya yin shagali a cikinsa. Kai tsaye dai za a iya sanya shi cikin Jerin Abubuwan da ake kira SAI KA KAI SHEGE.......
Casu gami da shaye-shayen Lemuka da ciye-ciye iri daban-daban ake yi. Kusan kowane Saurayi da Budurwarsa a wajen, in ma bai zo da tashi ba zai samu Abokiya.
Cikin farin ciki da kwanciyar hankali Kowa ke gudanar da shagalinsa.
Ihun MC ne ya karaɗe Kunnuwan duk ilahirin Mutanen dake wajen, cike da karaɗi da ƙarawa al'amari Ƙawa yake cewa "Don Allah duk wanda ya san ya zo Taya Irfan Mohammad Murna ne ya yi shiru kuma ya zubawa Ƙofar shigowa wannan haɗaɗɗen wuri ido, domin ganin Da wane Salo Babban Abokin Birthday Boy zai shigo!!!!!, sannan Duk wanda yake son jin kowanene Wannan Babban Aboki da muke ta jiran Shigowarsa ya ɗaga hannu." Cikin sauri gami da shauki mafi rinjaye Mutanen wurin suka ɗaga hannu.
MC ya sa dariya yana cewa "Wallahi Sai kun biya wani abu zan gaya muku!!, in ba haka ba kuma zan hana Abokin Birthday Boy ɗin shigowa, Ina son a kece raini tsakanin Mata da Maza don haka ga inda Mata za su juye Jakarsu ga Inda Maza za su juye tasu." ya faɗa yana nuna masa wasu Ƴan ƙananun Tebura dake kusa da inda yake tsaye yana zubo maganar.
Shiru ba wanda ya fara zuwa hakan ya sa MC ƙara cewa "Yau dai za mu gani Mata ne Jaruman ko Maza; Maza kar ku bari Mata su kayar da ku don wallahi suna fara fitowa kun faɗi warwas!!!!" ya ƙarasa maganar yana dariyar shakiyanci da Yaudara.
Jin haka ya sa aka fara tsere tare da gudun wuce tsara a tsakankaninsu, cikin Lokaci kaɗan suka tara masa kuɗaɗe Mazan kuwa sabida Burga har da masu ajiye watch ɗinsu kuma suka ce in Matan sun isa su saka, Su ma Matan da yake sun ƙagara su ga shigowarsa wasu tuni suka cire layukansu suka ajiye wayoyinsu.
Kasancewar Mafi yawancinsu Ƴaƴan Masu Kuɗi ne ko damuwa akan hakan ba su yi ba.
Sai da MC ya ce ya dakatar sannan suka dena Wasan kece raini.... "Dariya ya saka yana cewa ba shakka wannan Babban baƙo namu me farin jini ne domin kuwa Mata sun yi da gaske sun kayar da Maza sabida son ganinsa!!!" Tafi akasa gami da shewa tuni wurin ya ƙara karaɗewa, Wasu daga cikin Mazan suna cewa an yi musu maguɗi, shi kuwa MC hakan ƙara ziga shi ya yi, sabida Magana Tamkar zai tashi sama.
"To!!! to!!!! DJ yana Godiya yana ƙarawa!!; yanzu dai kowa ya saurara domin jin sunan haɗaɗɗen Abokin wannan Chocolate ɗin Birthday Boy namu!!" sai da surutan nasu ya lafa sannan ya ci gaba da cewa "1 - 2 - 3 ALIYU ALMUSTAPA NAIRA!!!!! Muna yi maka Barka da zuwa wannan waje!!!!" Tafi suka sake sanyawa gami da ihu, lokaci guda Salon wajen ya ƙara canjawa, da yawa daga cikin Ƴan Mata iyayi da kwainanensu sai da ya canja, duk suka zubawa Hanya ido cike da Ƙaguwa, kowacce ta ƙwallafa rai akan jan ra'ayinsa.
Sanye take cikin wata fitinanniyar Gown wadda ta kama jikinta tsam-tsam, ta sha Make-up kamar ba gobe, ta yi bala'in kyau, duk wanda ya kalleta sai ya ƙara, ga eyelashes ɗinnan zaya-zaya sun ƙara mata kyau da armashi, ta baya kuwa haɗaɗɗen kitson Ƙarinta ya bazu akan bayanta zuwa kafaɗunta.
Waige-waige take yi tamkar me neman wani abun, karaf idanunta suka sauka akan wani da ke tsugunne gaban wata Haɗaɗɗiyar Mota me Numfashi yana ɗan tattaɓa tayoyinta.
Da sauri ta ƙarasa wajen gami da yi masa sallama tare da Addu'ar Allah ya sa Direba ne, da sauri ya juyo yana tsitstsilla ido kamar Munafuki, cikin yanayinta na jijji da kai da ɗagawa ta ƙare masa kallo sama da ƙasa sannan ta ce "Daga ina do Allah??, wannan Motar Me gidanka ce??" Jin tambayar tata ta sa shi washe baki sannan ya bata amsa, "A'a Hajjaju, daga wata Unguwa nake wai ita Ɗorayi." "To gayyatarka aka yi wajen Birthday ɗin??" da sauri ya girgiza kai yana cewa "Wace ni??, a'a kawai dai na ga an yi posting ne a Facebook ana gayyatar kowa shine na garzayo in sha 5 alive in tafi, Allah ya sa ma sun yi mana Ƴar garau-garau ɗin da zamu afa." dogon tsaki ta ja gami da binsa da wani kallo wanda ya fi kama da na ƙyama sannan ta ce "Menene garau-garau kuma??" tuntsirewa ya yi da dariya yana cewa "Ai Hajjaju ku manya ne ba lallai ku santa ba, wani Abinci ne namu na Hausawa." Tsaki ta ƙara yi a karo na ba adadi sannan ta ce "Kai nan har wani Bahaushe ne?? ni ai kama kake yi mini da irin Fataken nan, yaya ake kiran Yarensu ma??, irin waɗanda za ka ga suna aikin Gadi a Manyan Gidaje" cikin sauri ya ce "Buzaye?? yo ai Ranki-yadaɗe baki faɗi ba, na ji an ce Kakan Kakana asalinsa Buzu ne, amma dai tinda ban iya kowane Yare ba barni a Bahaushen kawai." ɗan numfashi ta ja kafin ta ce "Za ka yi min aiki in biyaka??" Da sauri ya ce "Haba Hajiya indai za ki bani na cin Taliyar Yara ai ba matsala zan yi." Murmushin samun nasara ta yi kafin ta ce "Dama PA ɗina ne na aikeshi wani wajen, to ba na son Yawo ni kaɗai shine nake so ka tsaya a matsayin PA ɗina a wannan wajen, Bayan Mun fito zan biyaka, amma fa za ka dinga yi mini ladabi sosai sannan kai za ka riƙe mini jakata." leƙewa ya yi ya ƙara gano Jakar tata, ba laifi da ɗan girmanta, jinjina kai ya yi yana ƙara faɗaɗa fara'arsa ya ce "Na Amince Ranki-yadaɗe, Muje kawai kina tafiya ina take miki baya, ba ki da matsala." ta yi wani yauƙi gami da cewa "Okay, amma in ba ka yi abinda ya kamata ba ba zan biya da yawa ba ko kuma ka rasa ko ficika." "Me zai hana yin aiki tuƙuru ma Hajiya ai kin wuce nan a wajena, ni a kullum ma in za ki mayar da ni Ɗan Aikinki indai za ki biya na Amince." Murmusawa ta yi kana ta miƙa masa jakar tana cewa "Yaya sunanka ne??" "Ali Haidara" ya faɗa yana ƙara washe haƙora kamar me tallan makilin, yana karɓa ta yi gaba ba tare da ta ce komai akan sunan nashi ba; da sauri ya dakatar da ita da cewa "Hajjaju don Allah jirani, kin san mu Buzaye sai da rawani." gaba ta yi tana cewa "Ina ɗan can wurin maza ka zo ka sameni."
Zazzafar iska ya furzar yana bin bayanta da kallo.
Sai da ya naÉ—e fuskarsa da kansa ya rage sai idanunsa kaÉ—ai a waje sannan ya bi bayanta.
A tare suka shiga É—agwas-É—agwas tana tafe yana binta a baya kamar wani Mijin Ta ce.
Sai suka zama abin kallo kuma abin sha'awa ga Mutane, shi kansa MC sai da ya bata yabo da jinjina da girmamawa, hakan ya sa kanta ya ƙara huruwa Kamar Balo.
Tinda suka shigo Irfan Mohammad ya zuba musu, ba kowa yake kalla ba face na bayan nata ita kuwa sam bai ganeta ba ma.
Sai da ta ƙaraso inda yake suka gaisa sannan ta yi masa bayanin itace Leelah Facebook Friend ɗinsa, na bayanta kuma Body guard ɗinta ne. Tarbar Mutunci da Mutuntawa ya yi mata gami da yi mata godiya a bisa kyautar da ta bashi, sannan ya sa a rakata waje na Musamman a kula da ita.
Har zuwa lokacin hankalinsa ya fi karkata kan Body gourd ÆŠin nata, hakan kuwa ya sosa mata rai don so take ta ja ra'ayinsa akan Soyayyarta amma shi yana can yana kallon wani Gardin Namiji ÆŠan Uwansa.
Duk wanda ta haÉ—u da shi bayan gabatar da kai sai ta gabatar da Body Guard É—inta.
Bayan sun zauna Ya dubeta kafin ya ce "Amma Hajjaju za ki ƙara min Kuɗi ko??, na ga da farko PA kika ce mini yanzu kuma kin mayar da ni Body Guard!" tattaɓe baki ta yi a yanƙwane ta ce "Ka fiye azarɓaɓi, na gaya maka indai kuɗi ne ba ka da matsalarsu." Laƙwas ya yi yana zazzare ƴan idanunsa a cikin Naɗi.
Shagali aka ci gaba da yi yayin da MC ke ta ɓaɓatun Kiran Abokin Birthday Boy amma shiru wasu har sun far tunanin ko raina Musu hankali yake yi.
Kallo ne ya koma sama lokacin da wata Ƴar Budurwa me Halittun Indiawa ta doso ciki, sanye take cikin wata Shegiyar Doguwar riga blous fara tass!!, daga ƙasan rigar a buɗe yake buzur!! sai sharar ƙasa take yi daga baya, duk da Ɗan Mayafin da ta naɗe kanta da shi sai da Dogon gashinta dake ta sheƙi da walwali ya bayyana.
Cikin nutsuwa da kamala gami da jin kai take takawa, tana yi tana sama da ƙasa da dara-daran idanunta wanda Allah ya ƙawata mata su da dogayen gargasa. A bayanta Kuwa wasu daka-daka Ƙartai ne hannayensu riƙe da award wanda ya sha ado irin na Indiawa.
Duk wanda ya kalleta sai ya ƙara ba ma kamar Maza, Manyan Abokan Irfan ne kawai suka Ganeta ciki kuwa har da shi.