Sashe 17
Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tin da gari ya waye Momi ta kasa zama sai fakam-fakam take yi wai a dole sai ta haɗa musu abin tarbar Baƙi, ita dai Leelah abin har kunya yake bata don ta san sun fi ƙarfin duk wani abinda Momin za ta yi musu, wai har da Lemon Roba za ta sayo musu kamar ba su taɓa sha ba.
Salim duk wannan rawar jikin da ake yi shi banda shi yana gefe don kuwa fushi yake yi da Leelah akan rashin Mutuncin da ta yiwa Aminiyarsa.
Momi ce ta fito daga Madafa tana karkaɗe zaninta gami da gyara masa zama ta ɗage shi sama, "Salim!!!! Salim!!!!! wai don Ubanka ka zuba min ido kana kallo in ba ka taya ni ba waye zai taya ni?, ka zagaya baya wajen Bishiyar nan ta Gado da Ubanku ya saba zama ka ce masa ya tashi ya je ya nemo Kuɗin da za a sayo Fulawa da mai don yau sai na fita kunya a Gidan nan, ba zan karɓi baƙi haka sakaka kamar Shanu ba dole sai na yi musu tanadi. Murya ciki- ciki ya ce "Uhm aikin banza jefa Agwaga a ruwa, wallahi Momi ban ga abinda za su yi da abinda za ki jagwalgwala ki yi musu ba." "Uban me ka ce???" ta faɗa cikin ɗaga murya, da sauri ya ce "A'a meye na tashin hankali? cewa na yi da sawwaƙewa kanki kika yi don wallahi na san sun fi ƙarfin ɗan abinda za ki yi musu." "To dan Ubanka sai na yi!, sai dai in na basu su ɗauka su zubar ai dai na fita, ba za ka tashi ka je aiken da na yi maka wajen Malalacin Uban naka ba ko?, ba ma dole a haifi Ɗan Daudu ba! Mutum sai lalaci a ce nema ma ba zai iya fita ba?!" Sosai Gorin da Momi take yi masa shi da Babansu yake ɓata masa rai, dan dai Uwa Uwa ce kawai banda haka ba abinda zai hana shi yi mata abinda ko da wasa ba za ta kuma ba, a gefe guda kuwa yana jin haushin Abinda Iyayen nasu Maza ke yi, gasu Talakawa gashi ba sa son nema da Baba Ridwan da Babansu haka suke, shi kuma Baba Jamilu zai nema ɗin sai dai ko ya samu ba zai bawa iyali ba haka zai barsu su yi ta fakam-fakam, Baba Habu ne dai yake tashi tsaye ya nema kuma duk abinda ya samu alla-alla yake ya sauke nauyin da ke kansa.
Yana tafiya yana gunguni da mita, tin kafin ya ƙarasa ya gamu da Baban nasu yana shirin shigowa cikin Gida, isar masa da saƙon kira ya yi kana ya ci gaba da tafiya don ba ya so a yi Tijarar a gabansa.
Shi kansa Baba Usama cike da fargaba ya shiga Gidan.
Ai kuwa tana ganinsa ta yo kansa tana cewa "Gwara da Allah ya shigo da kai!, wai kai ba ka da Zuciya ne? Manyan Mutane ne fa za su zo gidan nan amma ko ruwa me kyau wanda za su sha ba ka ajiye musu ba, haka ake rayuwa?, wannan wace irin Masifa ce Usama? so kake ka jawo mata zagi da Gori a wurin Dangin Miji?" jiki a sanyaye ya ce "To me za mu yi? me muke da shi da za mu iya ba su?" "Ko ba ka da shi sai ka nema, ÆŠan Sarkin kiran babu!, sai ka ce a kanka aka fara yin ta, kuma wallahi ka san da sani sai ka yi duk me yuwuwa ka yi wa Yarinyar nan Kayan ÆŠaki da na Kicin na kece raini, na gaji da wannan abin naka, ba rance ba Allah ya sa sata za ka yo ka saya sai ka sayo su ba fashi, don haka yanzu ma ina jiran KuÉ—in Mai da na Fulawa.
Kamar zai fashe da kuka ya ce "Ni ba ni da su Dije!, ban san ina zan je in samo su ba, gashi rayuwar ta yi tsada....." katse shi ta yi da cewa "Ba ruwana da tsadar rayuwa!, ai ka iya kwantar da Murya ka cuci Mutum, to wallahi ba ka isa ba ka yi kaɗan." Leelah ce ta ƙaraso wajen tana kuka shaɓe-shaɓe, cike da damuwa ta ce "Don Allah Momi ki yi haƙuri, tinda ba mu da shi ba yadda za mu yi sai haƙuri, ni ina da ɗan sauran Kuɗi a wajena sai a Sayo iya ruwa kawai a bar wani soye-soye, don Allah ki bar zancen haka, Abba don Allah ka yi haƙuri."
"Dole ki ce haka dama mana, ni da nake yin komai a kan ki wai kin fi son Ubanki a kaina." cikin matsanancin Kuka Leelah ta ce "Wallahi ba haka ba ne Momi, ni dai na haƙura koda Haydar zai fasa Aurena in ba a yi wannan soye-soyen ba na haƙura; da Dukiyar Halal Allah ya ce kowane Mutum ya ciyar da iyalinsa, in kina haka za ki sa ya fara neman na Haram!" "Ke Buhun Ubanki!! har wani wa'azin ƙarya za ki yi mini?, ai shi kansa ya san muna yi masa ƙoƙari, in banda ina da ke ma ai da yanzu na haukace ko na ɗimauce, shi bai san cin mu ba bai san shan mu ba, gashi na haifi wani Ɗan Daudu shi da yake Namijin wanda ya kamata ya nema to ya zo a Ɗan Daudu kuma ba na shakka kan cewar wannan lalacin na Usama shi ne ya jawo haka".
Ganin Momi ba za ta dena zuba bala'in ba ya sa Leelah ta janye Abba ta fitar da shi waje gami da bashi haƙuri da roƙawa Momin yafiyarsa. Shi dai kawai cewa yake "Ba komai Laila, ai Ƙaddara ce kowa da irin ta shi, uhm! ba komai ai!, ba komai wataran sai labari, uhm! Allah Sarki, ai ba komai!".
Sai da ta ji Momin tana shirin biyo su ƙofar gida ta yi saurin komawa ta ci gaba da rarrashinta sai dai tana yin gabas ita tana yin yamma, in tana ba ta haƙuri kamar ƙara iza wutar take yi.
Haka Momi ta wuni tana bala'i da Masifa, su ma su Inna duk ta kunna su, abu ne wanda kowa yake damunsa su ma suka kafa tasu Masifar akan Mazajensu.
Leelah da Salma har ma da Umma sai aikin Kuka suke yi. Nana kuwa da yake tana bayan Momi É—are-É—are har da ita a faÉ—en maganganu. Salim kuwa tinda ya fice bai dawo ba sai bayan Magrib.
Sai bayan Isha'i Baƙin suka iso. A ƙofar gida aka yi musu shimfiɗar ƙatuwar tabarma sai dai duk ta yamutse ta fara zama ƙashi, ɗan ruwan da Leelah ta bayar a sayo aka zo aka dire musu.
Su Momi da Nana har ma da wasu daga cikin Ƴan gidan suna daga bakin Zaure suna leƙensu.
Momi tana ganin an miƙawa su Baba Kuɗi ta juya cikin gida tana rangaɗa wata muguwar Guɗa, Innayi ta karɓe ta tayata suka ci gaba da yi.
Inna ma shiga ta yi aka fara shewa da ita, Mama kuwa kadaran kadahan, Umma kuwa sai fara'a take yi tana cewa "Alhamdulillahi" abinda dukkansu ba wadda ta yi hankalin faɗe har ita kanta Uwar Ƴar.
Sai da baƙin suka tafi sannan su Baba suka shigo suka sanar da su iyayen Ɗa sun buƙaci a saka ranar Aure Sati uku su kuma sun yarda don ba su da ikon Ja da Manyan Mutane.
Sam Momi ba ta yi tunanin komai ba face ta kusa Aurar da Ƴarta ga Ɗan Masu Kuɗi, ba ta yi tunanin ta ina za su samu Abin yin hidima ba, ita dai kawai ta ci gaba da Murna.
Baba ne ya miƙawa Abba kuɗin da suka bayar yana cewa "To ga wannan, duk ku shaida Kuɗi ne suka kawo na Aure." Abba ya karɓa yana cewa "Ai adana su za a yi sai mu yi wata hidimar da su" "Kan bazawara ba gashi!!!, to dan Ubansu ina Sadaki kuma??, ko suna nufin kuɗi ɗaya za su bayar?, ai kuwa ƙaryarsu, tinda ɗansu ma ya ga Ƴata ya ƙyasa ai kowa ma ya san ba ta wasa ba ce, don haka kamar yadda ake yi wa kowace Ƴa me Daraja sai an yiwa tawa, a biya kuɗin Aure sannan a biya ni Sadaki" Momi ta faɗa a masife.
A sanyaye Abba ya ce "Haba Dije, ai sun ce za su bayar da Sadaƙin in an zo ɗaura Aure, kuma ko ma iya Sadaƙin suka bayar ai ba matsala tinda shi kaɗai Allah ya ce a karɓa". "To ba da ni ba!!, amma tinda sun ce za su bayar shi kenan, na zata mugun halin za su nuna mana su ma, waɗannan kuɗi kuma tattaro su za ka yi ka miƙo min, ni ya kamata in ajiye ba kai ba, in ma so kake ka yi kayan ɗaki da su to ba ka isa ba, sai ka fita ka nemo ka yo kayan ɗakin nan.
Baba Jamilu ya ce "Yo ai ba a ta kayan Ɗaki yanzu, sun ce ba abinda suke buƙata za su yi mana komai."
Zazzaƙar Guɗar da Momi ta tsumbura sai da ta sa wasu toshe kunnuwansu, hakan bai wadatar da ita ba sai da ta tashi ta fara taka rawa.
Yau dai an ga abin mamaki, sai da Momi ta É—aurewa kowa kai.
Haka aka watse kowa da abinda yake faÉ—e.