← Book details Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 35

Sashe 29

Haɗiyar Gatari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau ma sai da aka raba dare ana kwasar Shagali.
Salma tana samun sa'ar cafko Maa aka gama abinda za a yi ta samu ta gudu ta kwanta.

Washegari lokacin da ta fito Gidan sai tsirarun Mutane kowa ya san inda dare ya yi masa, abin daɗi ya yi mata duk sai ta ji ta sakayau kamar an cire mata rigar ƙaya.

Bayan Kwana Uku. Ko'ina biki ya tashi kowa ya dawo daga shi sai halinsa.
Su Momi ma sun dawo isu-isu sai dai yanzu salo ya ƙara canjawa don kowacce jin kanta take yi, ita Momi tana taƙamar Ƴar ta ta Auri me Kuɗi, Mama kuma tana tinƙahon Ƴaƴanta sun yi sabon kamu na Ƴaƴan Masu da shi.
Su Sumy kuwa dama abu ne wanda an riga an saba sai dai an ƙara samun ci gaba fiye da Da domin an samu sababbi hanyar nema ta ƙara faɗi.

Leelah Duk in gari ya waye ba ta ƙara sanya Haydar a idanunta sai dare ya kuma yi zai dawo ya kalamance ta. Abin yana ɗan damunta amma ta riga ta sa a ranta kawai yana fita ne sabida jama'arsa da kuma Kasuwanci, don haka ba ta tunanin komai.

Yau haka kawai ta ƙagu da son ganinsa, ta sha kwalliya kamar ba za a mutu ba, ta gama shirya irin tarbar da za ta yi masa.
Tin farkon dare har dare ya miƙa shiru babu shi babu labarinsa, tin ana sha ɗaya shabiya har ɗaya ta yi. In ta kira lambarsa ba ya ɗauka daga baya ma sai ya fara katse kiran, daga ƙarshe sai ya kashe wayar muɗis. Abin ya yi mata ciwon da ta kasa jurewa sai da ta sha kuka sannan bacci ya kwasheta Zuciyarta cike da tunane-tunane masu yawan gaske.

https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx

Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136

Tana zaune a ɗan Madaidaicin Falon dake ɓangaren nasu, ƴar ƙaramar wayarta ce a hannunta tana lallatsawa, a zahiri danne-dannen take yi, a baɗini kuwa ta yi zurfi a tunani. Tinda ta haɗa Alaƙa da Aliyu take wasu irin mafarkai marasa kan gado a kansa da Kuma wasu Mutane wanda a mafarkin kawai ta san Danginsa ne amma ba ta samu damar sanin ko suwaye ba.
Jin an tallafo hamarta ya sa ta zazzaro idanu tare da wangame baki za ta zunduma ihu, karon da aka samu tsakanin nasa idanun da nata ne ya sa ta fasa yin ihun suka shiga yiwa juna kallin ƙunta. "Rufe bakin mana ko cinye ni za ki yi??" da sauri ta rufe shi gami da kawar da kanta gefe a ɗan kunyace.
"Me kike tunani har ya hana ki jin sallamata?"
cikin sanyin murya ta ce "Ba komai!" "FaÉ—a min!, akwai wani abun gaskiya, ko akwai wani abin da bai yi miki ba a Gidan?, ko kuma zaman Gidan ne bai yi miki ba??"
cike da rashin sanin abin yi ta gyaɗa kai sai kuma ta yi saurin cewa "A'a! babu komai fa". "Kin raba min hankali kuma, faɗa min gaskiya. Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na ɗan lokaci sannan Salma ta ce "Am...da....dama.. Abbana ya ce....." kasa ƙarasa maganar ta yi don ba ta san ta inda za ta kamo ta ba.
Zaman dafa'an ya yi a kan Kafet sannan ya kalleta a nutse ya ce "Ina ji! Abba ya ce menene?" bakinta na harɗewa ta ce "Wai..wai fa... Garar nan da ake yi ce, shi ne yace ku yi haƙuri bai samu damar yi ba amma nan gab....." katseta ya yi bayan ya murmusa ya ce "A kan haka ne kike ta gunguni? ko ma shi ya sa ki tunanin?, abu ne fa wanda bai zama dole ba, ki bar zancen kawai don Allah, ba na raina ba ne amma ki ce ba sai an yi komai ba, ai Maa ta yi duk wani abinda ake buƙata idan kuma akwai saura ki faɗa min ko ki faɗa mata". gyaɗa kai ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Zura hannu ya yi a Aljihunsa ya zaro wata tamfatsetsiyar Waya ya miƙa mata yana cewa "Karɓi wannan ki dena fama da wannan Burin Ɗan Ga ruwan. kasa karɓa ta yi don kuwa ba ta taɓa yin tozali da irinta ba ma bare har ta zamo mallakinta, girgiza kai ta yi alamar a'a, dariya ya yi yana cewa "Ni fa wallahi da na fara ganinki na zata Jaruma ce kamar Ƴan Uwanki, ke ashe ma komai tsoronsa kike ji!" Murmusawa ta yi gami da cewa "Wai ni ba Yayarka ba ce kake tsokana ta?" "To Yaya yi haƙuri, amma dai ki karɓa Please" "Ba na jin Turanci kuma ka haɗa da shi a cikin maganar" ta faɗa tare da juyo masa ƙeya, "Tinda kika zo Gidan nan kike sa ni dariya, kina so cikina ya yi bindiga ko?" "Ni ban ce ka yi dariya ba ai, kawai neman tsokana ne yake sa ka yi; Ni fa da gaske nake ba zan iya riƙe Wayar nan ba, wannan ta hannuna ta ishe ni". ya lura abin nata da gaske ne don haka ya tattaro duk nutsuwarsa ya ce "Ni kuma da gaske nake da wannan Wayar za ki yi amfani, tinda Allah ya sa kika zamo Matata fa sai kin jure wasu abubuwan don yanzu ma gani nake ba a yi komai ba akan nan gaba, don Allah ki karɓa kafin na fara yi miki kuka". Nazartar lamarin ta yi kafin ta ce "To ajiye a ƙasa" ba musu ya ajiye mata, ɗauka ta yi tana ƙare mata kallo, tsakaninta da babbar waya sai dai ta hanga a hannun su Leelah su Sumayya, tana da tabbacin wannan ba ma tsarar ta su ba ce, to ta yaya za ta iya amfani da ita?. Tunanin da take yi kenan tana jujjuya wayar.
Ba ta ankara da ya ɗauke ƴar ƙaramar ba sai ta ga ya miƙo mata Layin ciki. Jiki a sanyaye ta karɓa cike da takaici, ta so ya bar mata ita sai ta dinga ajiye babbar tana amfani da ƙaramar.

Zuwa yanzu lamarin Haydar ya gama É—aure wa Leelah jijiyoyin kanta, cikin kwana Uku sau ÆŠaya ta sanya shi a idonta, da ranar Allah ta ga sun fito shi da wata Budurwa sun yi waje, ta tabbata sun ganta su duka amma ko kallonta ba su yi ba.
Ya gama kwankwaÉ—a mata Madarar Mamaki, gashi duk iya nazarinta ta kasa gane abinda yake faruwa, duk ta tsargu sai tufka da warwara take yi.

Yau suna zaune a Babban Falo suna Hira Aliyu ya ce ''Bhaba ina son Gida za mu zauna na É—an lokaci tare da Salma."
Bhaba ya jinjina kai gami da cewa "Me ya sa?" "Kawai na ga kamar ba ta sakewa ne a nan" ya faɗa yana kallonta, da sauri ta ɗago kai tana zaro ido cike da mamaki sharrin da ya lafta mata, kashe mata ido ya yi gami da yi mata gwalo. Harara ta danƙara masa har da cije baki, ji take ina ma za ta iya ta shaƙe shi.
"Ba gasiya ya faɗa ba ne Ƴata?" Maa ta jefa mata tambayar gami da tsare ta da ƙartan idanunta, ƙasa ta yi da kai tuni kunya ta yi mata Hijabi, ji take dama ƙasa zata tsage ta shige ciki, a ranta kuwa ayyana yadda za su kwaso ta da Aliyu take yi don ba ƙaramin takaici ya bata ba.
Chapter 29 · 0% Book details