Sashe 9
Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
babu tarbiya babu karatu sai talla.maza kuwa daga kwandasto sai kwasan bola,sai karamin su mai sayar da rake.ka ji bayanin da yaya amina ta yi min. mahamud ya ce,tabdijan kuma ka ji ka gani?lsmail ya ce,to yaya zan yi?ba ni da zabin da ya wuce aurenta.buri na shine in ta zama tawa zan tsaya mata ta yi karatu duka biyu.mahamud ya ce,ALLAH ya taimake ka. bayan sallar lsha suka yi sallama da mahamud kan cewa sai gobe in sun hadu, kafin lsmail din ya tafi gida, gidan yaya amina ya nufa, a tsakar gida ya same su ita da yara suna cin abinci. nan yaran suka shiga yi masa sannu da zuwa.ya ciro naira dari ya ba sadam babban,je ka sayo maku biskit,ya ruga da gudu yana murna,yaya amina ta ce,ba ka gajiya ne?haba dai.ta ce aisha dauko ma kawunku tabarma.bayan sun gaisa sai yake sanar da ita batun tafiyarsa abuja.ta ce, gaskiya na yi murna.ALLAH ya sa alheri ne ya kira ka abujan.lsmail ya ce,amin yaya ina son in na dawo in tura gidan su zainab.yaya ta ce,umm!kai dai kana son wannan zainb din yayi dan murmushi,ku taya ni da addua ALLAH ya sa haka shine mafi alhari.ta ce.umm to amin,sun jima suna hira sannan suka yi bankwana ya tafi.yana shiga gida ya kunna wayarsa ya shiga soro su ya ciro makulli dakin ya bude.ya dubi makunnin wutar ya kunna haske ya wadace dakin ya shiga.ya dauki buta ya fita zuwa cikin gida don zagawa ban daki.a tsakiyar gidan matan yayyin sa ne da 'ya'yansu suke ta hira,ya yi sallama suka amsa yayi masu sannunku ya wuce.don shi dama tsakaninsu bai wuce haka ba,sai da ya fito bandakin sannan ya nufi dakin inna,ya yi sallama tana ta gyangyadi.sallamar shi ce ta tashe ta,ya shiga ya gaida ta,ta amsa tare da cewa kananan?ya ce eh na shigo da safe ki na bandaki. ta ce,haka dai ka ce,indai nina haife ka ai don ina bandaki ka jira ni.yayi dan murmushi, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (35)Zuwa yanzun ya saba da halin inna.ya daina jin haushin maganganun da take fada masa marasa dadi.dama zan sanar da ke ne gobe in ALLAH ya kaimu zan tafi abuja.ta ce habuja?kai ko me zaka yi a habuja?ya ce,koyarwa na samu a wani gida zan dinga koyar da yaran gidan ta tashi tsaye,can kuma ka kutsa,lallai ba shakka,ya mike,ya jima da sanin inna zai yi wuya tayi masa adduar ALLAH ya sa alheri. ya fito yasa takalmi tare da daukar butarsa.tun kafin ya bar tsakar gida yana jinta tana cewa kunji mutan gidan nan,samail ya samu koyarwa a habuja,ya fadawa mazajenku?fatu ce ta soma magana,lallai ba shakka,ya fadawa mazajenmu su a su wa?ke ma don kar a ce dai bai fada bane,kala bai ce ba ya wuce dakinsa. Da safe sai da ya shirya tsaf,sannan yayi wa yayyansa maza sallama,su kam sun yi masa ALLAH ya sa a dace.gidan su mahamud ya nufa.yayi sallama da malam aminu mahaifin mahamud sannan suka nufi gidan hajiya sauda.mahamud ya goya shi a mashin,kuma sun yi shawara a kan mahamud zai ci gaba da koyar da su hussaina. A waya ya kira hajiya ya fadi mata ya iso,ta sa ya shigo,kar ya damu ai shima tamkar shi dan gida ne.suka shigo falon baki nan ta same su,ya gabatar mata da mahamud,bayan sun gaisa ta kuma kara rokonsa a kan ya tsaya mata sosai a kan MIMI,duk lokacin data yi yunkuri ko barazanar koran shi,to ya kira ta.ta ce nasan aiki ne na baka mai wahala,amma kamar jihadi ne,ya ce,na yi miki alkawarin zan tsaya a kanta kamar kanwa ta,zan jure saboda ALLAH da kuma halaccin da ki kai mun.ya'u direba ne zai kai shi,sai da motar ta tashi sannan mahamud ya buga mashin cikin kewa.suna tafe suna labari shi da ya'u cewa yayi,gaskiya ina yi maka jajena kan wannan aiki,gara in yi aikin kwasar kashi don na tsani wulakanci,lsmail ya ce,hmm ni fa gani nake kamar wata kaddar tasa zan je koyar da yarinyar nan. wata zuciya kuma tana fada mini ALLAH zai taimake ka.ina tunawa ni NAMIJI ne,sai inga to wai meye ne abin tsoro. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (36)Ya'u ya ce,ba za ka gane ba,ai ubanta zata sa ya tozarta ka.ga zagin wulakanci,lsmail ya ce, ALLAH ta zage ni sai na mare ta.ya'u don dariya sai da motar tayi kamar zata sullube masa.ya ce gaskiya kar kayi wannan kuskuren, lsmail ya ce,nanne kaduna? ya'u ya ce,eh amma ba garin kaduna ba ce zariya ce,nan dama baka taba zuwa ba?kai ni ina zaton sokoto kawai muka taba zuwa yin gasar karatu lokacin ina SS1.ya'u ya ce gaskiya ni ban zata ba,in na kalle ka sai ka ce ka taba fita kasashen duniya. lsmail ya ce,ni kifin rijiya ne ban san ko in ba.in mun zo kaduna ka nuna min ina jin labarin garin ina son zuwa. ya'u ya ce,shike nan za nuna maka,tun daga na yake nuna masa garuruwa har suka isa kaduna.ya ce, bari in bi da kai ta cikin garin maimakon by pass tunda kana son ganin garin. shikenan lsmail sai kalle-kalle ya ke yi.ya ce,garin ya birge ni.amma duk a zato na ya fi haka,yadda sunan kaduna ya cika ko ina.ya'u ya ce,zaman garin yana da dadi saboda ba su shiga harkan abinda bai shafe su ba.lsmail ya ce,wani ya taba bani labarin garin 'yan karya ne ko?ya'u ya ce eh, to ni ma dai haka na ji ana cewa,to muna da 'yan'uwa. suna zuwa katsina gurin innarmu,mu ma mukan zo,ba wasu masu karfi ba ne,amma komai za su yi sai inga suna son yin wanda yafi karfinsu,ni ma sai na amince 'yan karya ne.amma daga baya lokacin ina yin tuki a nan kaduna a wata unguwa wai ita unguwa rimi sai na gane ba wai karyace da su ba,yin hakan a jinin 'yan kaduna ne yake.ka gane malam lsmail? su mutane ne masu son yin komai me kyau,kuma basu da kyashin sayan duk abinda ransu ke so,ko da kudinsu kenan idan za a aje maka dan kaduna mai dubu dari biyar,da dan wani gari mai milyan biyar,za ka ce dan kadunan ne mai milyan biyar,wancan mai dubu dari biyar.lsmail ya ce na gane,in ko haka ne sun burgeni.saboda ni mai irin raayi na kenan,arziki na ALLAH ne,in na samu zanyi abinda nake so da halas di na.haka suka yi ta labarin 'yan kaduna har suka kai abuja garin manya. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (37)Shi kam a ranshi 'yan kaduna sun yi mashi, yana son mutane masu test,wadanda ba komai ne ya yi masu ba. Tafkeken gida ne na gani na fada,tunda suka doshi gidan lsmail ke mamaki sai ka ce fadar shugaban kasa,duk yadda yake kisima gidan a rashi ya wuce nan,tun kafin su shiga ma kenan.su na shiga sai ya ga ma kamar wata sabuwar duniya ce,wannan mutumin wane irin kudi ya mallaka?lsmail ke tambayar kanshi. dama tun kafin su kara so ya kira hajiya ya fada mata cewa sun iso unguwar,ita kuma ta kira momi nafisa ta sanar da ita.lsmail ya na jingine jikin mota,wani matashi ya iso wurinsa ya ce,wai wanene malam lsmail?ya ce,ni ne. ya ce,to zo mu je,ya kalli ya'u direba zo muje, ya ce,a'a,ni dama aiki na shine na kawo ka,kuma na kawo ka,yanzu zan juya.lsmail ya bashi hannu suka yi sallama bayan gidan suka nufa inda suka nufa gefen yara, suka je ya bude wani daki, an ce ka shiga nan.lsmail ya kalle shi,ba mu gaisa ba?ya mika masa hannu suka gaisa.ya ce,suna na lsmail,kai fa?ya ce hamisu, kuma nine direban yaran gidan nan.ga daki na nan kusa da na ka,mu biyu ne a cikin dakin,ni da me share-share,game da kula da fulawoyi.lsmail ya ce, ALLAH ya sa mu amfani juna,hamisu ya ce,amin. lsmail ya shiga yana kallon dakin tamkar ba dakin masu aiki ba,hamisu ya ce,ai kurar dakin ba ta yi yawa ba,don kanin momi bai yi sati da tafiya ba,da cikin dakin yake.lsmail ya ce,kurar ba tada yawa ma kenan,amma duk da haka bari in dan kakkabe,ya shiga ciki sosai,hamisu ya ce,in zaka yi sallah ga bandaki nan.lsmail ya ce,tunda muka taso,duk inda sallah ta same mu,sai mu tsaya muyi ta.ya ce, shikenan baka da wani nauyi a kan ka.lsmail ya gyara daki mai dauke da katifa katuwa,sai duruwar ajiye kaya,sai kuma dan teburi a gefan katifar. hamisu ya ce,bari in sa a sanar da momi cewa ka iso,kuma naba ka masauki, yanzu saura abinci. kusan minti ta latin da fitar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (37)Kusan minti ta latin da fatar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa,sannan ya ce,ga abincin ka.shi ma nan haka lsmail din ya sake gabatar masa da kansa, suna na lsmail kai fa?ya ce, suna na jabiru,kuma nine mai dafa abincin rana da dare,lsmail ya bashi hannu suka gaisa.bayan fitan sa ne ya bude plate din abincin, dafa dukan shinkafa ne,ta ji kifi da alayyahu,ya ci ya koshi,ya sha ruwa ya koshi.daga nan barci ya sace shi, saboda gajiya bai taba yin doguwar tafiya kamar haka ba daga katsina zuwa abuja. can da ya farka ya kalli agogo,sai ya ga lokacin sallah ya karato,nan da nan ya tashi yayi alwala,ya fito waje bakin gate don ya ga karamin masallaci a gurin. hamisu yana zaune kusa da maigadi suna hira,yayi masu sallama,suka amsa. ya ce,hamisu ina ladani ya kira mana sallah lokaci yayi, hamisu ya ce,ba a fa kiran sallah a masallacin nan,sai dai kawai kowa yayi alwalarsa ya shiga yayi sallah.lsmail ya ce,saboda me?hamisu ya ce,ni dai haka na tarar suna yi,to ai duka-duka mu uku ne ke yin sallar,ni da maigadi da mai shara.ko maigidan ba kullun yake sallah a cikin masallacin ba,ya fi yi a cikin gida.yaron sa namiji daya. ya kai shekara shabiyu, amma ko shi ba a turo shi. lsmail ya ce,ko ku uku za ku iya jam'i,don haka ni kam zan kira sallah. lsmail ya shiga ya ga da abin magana da komai,yana kwada kiran sallah daidai lokacin motar alhaji bashir tana kunno kai ko da direban ya tsaya bai fito ba,sai da ya ji karshen kiran sallah,muryar tamkar balaraben