← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 89

Sashe 28

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

an gama daure aure za mu koma gida.ta ce,shi ke nan sai na iso.ta kalli khalil,ina za ka tsaya?ya ce zan je har gaba mahaifinki, yayi yadda ya ga dama da ni.amma na gama hango mutuwata,in har na rasa ki. ta kalli agogo,yanzu sha biyu da wani abu,kana ganin har za mu je abuja ba a daura da na'ima ba?ya ce zan fi kowa so in hakan ta kasance.ki yi adduar allah ya sa ni ne mijinki.daya saura alhaji ya shigo gidan don shirin zuwa masallaci ko kuma in ce gurin daurin aure.daidai lokacin ne kuma hajiya binta ta shigo,ita da yaranta. mamakinta da tunaninta alhaji ya rasu ne?ko an ga amaryar ana ci gaba da biki,shi yana asibiti?ta ga harabar gida an zuba kujeri da rumfuna,ga mutane da yara.suka shiga falo.nan ma duk jamaa.dakin nafisa hajiya bintar ta nufa.cike da manyan kawayenta,tana zaune a gaban madubi,ta yo wanka ana yi mata kwalliya.hajiya binta ta ce,nafisa wai biki ake yi ne?ta mike da sauri,sannun ku da zuwa kun iso?eh,kin san tafiyar mota,tun bakwai muka fito.ban gane ba,wai bikin ake yi ne?eh bikin na'ima.cikin mamaki, hajiya binta ta ce,na'ima kuma?momy nafisa ta karaso gurin ta cikin murmushi,eh,kin san MIMI ta gudu.shi ne na'ima ta zabi ta fitar da mahaifinta kunya. hajiya binta ta ce,to shi alhajin wane asibiti yake?ta ce,ya shigo yana gefensa,zai yi wanka. [01/10 10:34 pm] Abdul: (26)Tun jiya aka sallamo shi.yana jin na'ima ta yi wannan furucin,sai ya gyare.wata daga cikin matan da ke zaune a kan gadon ta ce,yarinya ai ta share wa ubanta hawaye. wata ta ce,ai ko ta yi saa jiya maigidana ke ba ni labarin irin gudummawar da abokan kasuwancin alhaji suka yi ta ba amarya. babban dan kasuwan nan wanda yafi kowa shahara a afrika an ce zunzurutun kudi miliyan ashiri ya ba da, banda motoci.hajiya binta dai ta ce,bari in duba alhaji. momy nafisa ta ce,to ki duba shi.yawwa hajiya sauda ma suna saman MIMI to kawai hajiya binta ta ce, ta nufi sasan alhajin,cikin al'ajabi.gani take yi momy nafisa murna take yi da aure ya juye a kan 'yarta. Ta kalli yaranta ku hau saman sis MIMI,hajiya sauda tana nan.da farko har za su noke,don suna tsoron MIMI,tunda bata kula su.amma jin cewa sauda tana nan,sai suka nufi saman cikin murna.suna son hajiya don in sun zo hutu ba sa son tafiya.ta iya tafiyar da yara sosai. Ta samu alhaji ya fito wanka,ya ce,aa ku ma kun iso?ta ce,eh,alhamdulillah sam ban zaci zan samu jikinka haka ba.na ji an ce sugar,mene ne mene ne.ya ce,da sauki.da ma karin damuwar kunyar da MIMI ta so ta ba ni ce,sai kuma na'ima ta zo ta tare matsalar.yanzu dai burina a daura auren nan.zan koma asibiti,likita ya duba ni yadda ya kamata.ta ce allah ya sawwake.to,yanzu mene ne labarin MIMI? ya kalle ta.bayan ya gama saka wando,yana tura singiletinsa,ba ni da labarinta, kuma bana bukatar in sani.hajiya sauda sun zo da su abba.lna zaton suna saman.hajiya binta ta ce,to bari in ji gurinsu.ta samu su abba za su fito.nan suka tsaya suka gaisa.suka ce bari su fita su yi salla.ln an daura aure za su wuce.hajiya binta ta ce,wai ni hajiya yaya lamarin ya zama haka?ba kya tunanin cewa nafisa ta san komai a kan gudun MIMI ko bijirewarta?ba na tunani,in ji hajiya sauda.ba na zargi a kan abin da ban ji ban gani ba.abin da na sani kawai alhaji shi ne silar komai.haka nan kullum ina cikin adduar allah ya shirya MIMI.ya bata miji na gari. [01/10 10:34 pm] Abdul: (27)Ban yi fushi ba ko da aurenta bai kasance da dan gidan minista ba.kila ba alherinta.hajiya binta ta ce, haka ne allah zai amshi adduarki,domin bakin mahaifiya yana da karfi a kan yara.hajiya sauda ta kalli usaina wadda ke dube-dube a kan kwamfutar MIMI,ta ce,ku sa wa yaran nan abinci ga shi nan.hasana ta sa wa hajiya binta.hajiya binta ta ce,ni duk damuwata ta a ba na jin yunwa.sauda ta ce,damuwar me,bayan ga jikin mijinmu da sauki? hajiya binta ta ce,batan MIMI ai abin tunani ne.ko kusa,in ji hajiya sauda,guduwa ta yi,ba bata ta yi ba.kin ga kwanukan da su abba da abdulkarim suka ci?cewa suka yi tunda jikin dadynsu da sauki a sa musu abinci su ci.ni ce ma ban riga na ci ba.na fi son abu mai ruwa da safe,mai kuma dumi kamar shayi.hajiya binta ta ce,ya fi dadi ai hasana sa min wainar allah ya rufa asiri.suka ce amin. Duk da gudun da motar da su MIMI suka shiga take yi,gani take yi kamar ba gudu ba.ba ta taba shiga motar haya ba tunda aka haife ta sai yau.bugu da kari bata taba shan wahala ba a rayuwarta tunda take kamar wannan lokacin da ta bar gidan iyayenta.shiru da ta yi daga zaune abubuwan da take lissafawa ke nan.duk da tsananin son da take yi wa khalil ba ta jin za ta sake barin gida,ba tare da yardar mahaifinta ba.abin nufi ba tare da sun yi mata aure ba.cikin haka ne ta ji mutanen cikin motar suna salati,wadansu kuma wadanda ba musulmi ba suna ambatar abin da suka yi lmani da shi.ta zaro idanu,lokacin da ta ga motar ta su ta saki hanya, sosai ta firgita,ta soma fadin wayyo allah!daf da wani rami motar tasu ta tsaya cak.wai ashe taya ce ta fashe,tana duniyar tunani,bata ji kara ba.babu wanda ya zaci motar nan za ta tsaya.motoci suka tsaya ana ta yi musu allah ya kyauta.hankalin MIMI ya sake tashi.har aka canza taya jikinta bai daina bari ba.haka nan duk lallashin da khalil ke yi mata bata daina kuka ba.shi kansa yayi dana sani sosai na tahowa da ita.da kyar ma ta yarda ta sake shiga motar suka nufi hanya.karfe biyu daidai aka daura auren. [01/10 10:34 pm] Abdul: (28)Karfe biyu daidai,aka daura auren na'ima da abbas.daurin auren mai dimbin tarihi irin manyan mutanen da suka halarci gurin.babbar matsalar angon yaki halartar daurin auren,yana gida kwance,lta kuwa na'ima suna can gidan yayar mommy nafisa suna cashewa da makadan da suka dauko.sun koma can ne wai kar a ce suna murna da auren ya koma kan na'ima.wani karin abin aushin ma na'ima ita da abbas din ba su taba yin magana ko da ta waya ba. kuma daga momy har na'ima ba su taba tunanin cewa wannan wata matsala mai zaman kanta ba ce.uku saura tasi din da suka dauka shata ta karyo kwanar layinsu.kasancewar layin baya fita,sai ta tsargu da ganin motocin da aka ajiye a layin,ga mutane ta ce,me ke faruwa?ba dai dady ya mutu ba?dan tasi din ya ce,gaskiya ina zaton ba mutuwa ba ce,sai dai biki.ta ga nisan su karasa har kofar gidan,don haka ta ce,tsaya ina zuwa.yana tsayawa ta dauki jakarta,ta zura da gudu.kofar gidansu duk jamaa.gate dinsu a bude.tana shiga da malam lsma'il ta soma yin ido hudu. mutane ba su gane ta sosai ba,saboda ita ba maabociyar saka hijabi ba ce.lsma'il ya ce,daga ina kike?ta ce,me ake yi a nan gidan?ya ce,auren na'ima ta zaro ido,an daura da na'ima?ya ce,tabbas!sai ta juya,yana cewa ke!za ta fita ke nan su abba da abdulkarim za su shigo don yin sallama da hajiya sauda don basu so su kai wannan lokacin ba a abuja.dad ne ya tsare su,wai sai an gama daurin aure.yana ta nuna su ga abokansa, wadanda a da MIMI suka sani,basu san ma yana da wasu yaran ba.sai abokansa na tun farko irin su alhaji lsa.abdulkarim ne ya gane ta,don abba ne a gaba,amma bai kalli fuskarta ba,kuma hijabin da ta sa ya kara boye ta.da karfi abdulkarim ya rike hijabinta,har ta dan gota shi.ya jawo ta ya falla mata mari.sai da ta ga wani haske,ya ce,gidan uban wa za ki koma?ta tsala ihu,wanda ya janyo hankalin duk mutanen da suke harabar gidan.lsmail ya iso gurin yana cewa a yi mata hakuri.abba ya ce, haka shi ne daidai da ita. suka iza keyarta tana kuka, suna rankwashin ta,gami da zagi. [01/10 10:34 pm] Abdul: (29)Momy nafisa ta fito da gudu,domin wata kawarta ce zata tafi gida,sun yi sallama.amma tana fitowa ta ga MIMI a hannun su abba.sai ta koma da gudu ta sanarwa momy nafisa cewa ga fa MIMI.da farko momy nafisa idanu ta zaro,tana cewa,na shiga uku!me zai sa yarinyar nan ta dawo yanzu?sai yarta ta ce,kar ki damu tayi ta dawowa.an riga an daura aure.momy nafisa ta ce, kuma fa haka ne.bari in fita in ga yadda wannan fim din zai kare.suka sa dariya gami da shewa,ita da kawayenta.ta kalli wata hajiya nana,ba ni wayata!ga ta nan kusa da ke in sanar da ubanta.ln ya zo fim din zai fi dadi kallo. shine nan ta fito da gudu.a daf da hawa sama ne ta iso ta rungume MIMI ta fashe da kukan karya.lna kika shiga ne yata?me ya sa kika yi haka?abdulkarim ya ce,momy sake ta mu je sama.sake komawa za ta yi.abba cikin fushi ya ce,ki wuce mu je mana!don shi yana jin haushin momy nafisa ta taimaka gurin lalacewar MIMI.momy nafisa ta sake ta suka iza keyarta zuwa sama. abdulkarim yana rike da jakarta.momy nafisa cikin kukan ta kira alhajin ya ce? tana sheshekar karya ta ce,ka zo gida,ga MIMI nan ta dawo su abba suna ta dukan ta ya ce,haka shi ne daidai.na gode musu.ya kashe wayarsa. hajiya sauda tana inda take zaune ba ta tashi ba tunda ta yi sallar azahar sai ko ga MIMI ta shigo da gudu.a gaban hajiya sauda suka yi mata duka.dama kowannensu yana da haushinta.hajiya binta ce ta kwace ta.ko kallo bata ishi hajiya sauda ba,bare ta yi magana.hasana da usaina sun yi jungum-jungum cikin tausaya mata ta rakube gefen kujera tana ta kuka. abba ya ce,wawiya mara hankali kin bata sunanki a duniya.kin zubar da mutuncin kaki.abdulkarim ya ce,sosai kuwa,duk yarinyar da ta gudu ta bar gidan iyayenta,ai sunanta yar lska.hajiya binta ta ce, gaskiya baki kyauta ma kanki ba MIMI.ba ki yi wa mahaifinki adalci ba lrin son da alhaji ya nuna miki,ln kina da hankali,ko wuta ya hura ya ce MIMI shiga,ba za ki yi tsalle ki shiga ba,bare aure? [01/10 10:34 pm] Abdul: (30)Sai lokacin hajiya sauda ta yi magana,ta ce. ai shi yasa haihuwa ma da yawa take da dadi.ln wani ya saka kuka wani sai ya share maka
Chapter 28 · 0% Book details