← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 89

Sashe 51

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alhmdlh. Lokacin Ismail yana zaune yana 6are wa
mimi lemun zaqi, ya daga ne ya kalli mimi, wadda ta
qosa tasha lemun. Yace, ina zuwa. Ya fita cikin sauri.
Suka gaisa, sannan yace, hajiya kwana biyu? Tace
layin ka baya shiga. Yaya mai jiki? Yace da sauqi sosai
hajiya. Ina tsammanin matsalar ntwk ne, amma
wayata a kunne take, kuma akwai charge. Tace sauqi
na samuwa sosai ko? Ismail yace, tunda tana dai
kar6ar abinci. Hajiya sauda tace, to mun gode Allah,
sannan ina qara jaddada maka amanata, sannan ina
qara baka haquri. Na sani zakaga abubuwa gurin
mimi. Ismael yace, don wannan karki damu hajiya.
Sannan ina godia kan kudin da aka turo. Tace, karka
damu wannan ba wani abu bane. Zan sake turo ma
wasu insha Allahu. Daganan sukayi sallama. Ya dawo
ciki yaci gaba da 6are lemunsa. Sai da ya gama ne, ya
kalli mimi tare da cewa,, qanwatah ga lemun.
Fuskarta daure tace, bana sha. Sbd me? Ya
tambayeta cikin sauri. Tace, saida ka gama yin wayar,
sannan zaka 6are min, alhalin tun tuni nace zansha
lemu. “cikin irin shagwa6arta data zame mata jiki
tayi maganar. Sannan qasa qasa don ita mimi ko
yaushe maganarta qasa-qasa ce. Ya matsa kusa da ita
haba qanwatah waya nayi. Ta harareshi, bana son
ana hada uzuri na dana wasu. Inka gama nawa sai
kayi na kowa. Yayi ‘yar dariya sbd yadda ya lura itafa
iyakar gskyrta take magana. Yace, shikenan ranki ya
dade. Ko wane lokaci uzurinki zansa a gaba. Tashi
kisha lemun to. Tace ya fita raina. Barci nakeso inyi
ynxun. Ya kalli lemun na hannunsa, sannan ya ajiye
ya gyara mata kwanciya, tare da cewa, ayi bacci lfy.
Ismail shida yaya Amina sun tafi Daura sbd maganar
saida filin mahaifiyar su na gado. Hannun Ramatu
Nurse Ismael ya bar mimi. Domin yace, komai dare
aranar zai dawo ba zai kwana ba. Mimi kam ko amsa
shi batayi ba, lokacin da yake yi mata saiya dawo. Ya
gama karantar halin mimi tsaf, dan zaman da sukayi
tare, shirunta na nuna taji haushin tafiyarsa. Bai
damu ba, nasa ganin tafiyar itace zata kawo masa
qarshen tunanin, ina zai samu kudin tafiya jami’atul
madina. Sun samu tarbar mutunci da qauna, kamar
yadda aka san dangin uwa. Sannan sunyi murna
dajin batun tafiyar Ismail qasa mai tsarki don yin
karatu.
Haka nan sun jajanta masa batun hadarin matarsa
da suka basu labari. Sannan sunsha alwashin zuwa su
dubata. Kawunsu yace, shikenan nan ma in za’a zo
sai a taho da kudin tunda yau za’a sata a kasuwa.
Qarfe takwas da rabi Ismail ya iso katsina, yabar
yaya Amina a can zatayi kwana biyu. Ya nufi gida kai
tsaye, yayi wanka yasa jallabiya mai ruwan siminti,
sannan ya nufi asibiti. Sai da yayi mata tsarabar kifi,

sannan ya qarasa asibitin. Kuka sosai ya sameta
tanayi idanunta jajur. A rude yake tambayarta
abinda ya sameta. Bata tanka ba. Yace, to ga
gasasshen kifi na siyo miki, nasan zaki ci. Ya duba
cikin kular da yaya ta dafo mata abinci kafin su
wuce, ashe faten wake ne da kifi, amma bata ci ba.
Ya dawo ya zauna bakin gadon. “Kar dai duk yau
bakici abinci ba? Ta kalleshi idanunta jajur, “yau na
yarda banida kowa, muryarta tana rawa irin na
wanda ya gaji da kuka. Yace me akayi miki khadija da
bana nan? Fadamin. Kuma karki sake cewa, bakida
kowa. Gaki da ni, ga yaya Amina, muma da mu biyu
ne, amma ynxun kinga mun qara mun zama mu
uku. Mun tafi da tunanin ki. Ya warwaro tissue ya
soma share mata hawayen. Sannan ya dauko kifin ya
soma bata a baki sala-sala tare da jajjagaggen kayan
miya. Taci sosai, sannan ya debo ruwa ya kawo mata,
ya taimaka mata ta wanke hannu da kuma baki.
Sannan yace khadija tunda ynxu kina iya zama zaki
iya yin sallah. Ta 6ata rai. Yace wai meyasa duk
lokacin da nayi miki zancen sallah, sai ki 6ata rai?
Tace to yaya zan iyayin sallah a haka? Yace, zaki iya
mana. Shi addinin musulunci sauqi ne dashi, ya nuna
mana yadda zakayi ibada matsawar kana cikin
hankalinka. Ita kuwa sallah sbd muhimmancinta, ko
a filin yaqi anayin ta. Tace, ni ynxun dai ka barni
barci zanyi. Ya ce, kinada yaqinin daga varcinnan zaki
farka?
Tayi shiru, yace bakida yaqinin cewa, zaki farka,
kuma zaki iya farkawa ki ganki a kabari. Tace, oh
Allah na, don Allah kabar zantukannan. Yace assha!
Assha! Ina tsoron kar zuciyarki ta kamu da mugun
ciwo, wanda batason ko kadan taji an ambaci Allah
ko manzonsa, ko wani abu na addini. In hakane
kuwa lallai kin daura qawance da shaidan, kuma yaci
galaba akanki. “Don Allah ka barni mana! Ga
mamakinsa, sai yaga ta soma kuka, shiru yayi, ransa
6ace. Lallai akwai matsala babba, akan zancen addini
mimi ke kuka. A fili yace “akwai aiki!.
Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi
gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba.
Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta
samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon
babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin
kashewa, ynxun dai fada min me za’a yi? Hajiya Nana
tace, tsabar katan qamshi za’a hada masu fizgar
hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa
wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa.
Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya,
lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa,
amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa
daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi

kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. “kai Nana!
Allah ya shiryeki.
Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan
ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy,
yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya
Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin
kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli
kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu
kayan, inda daganan suka nufi gidan Na’ima. Cikin
sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm.
Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume
momy tayi tana kuka.
Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin
gadon Na’imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba
zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, “ke
da Allah natsu! Na’ima ta tsaya tana share hawaye
don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan
ki zauna in karanta miki. Nan ta soma shiryo abinda
suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu
koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta,
karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko
kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da
kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin
gidajenmu.
Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da
kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu
sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka
karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata
shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace,
kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du,
yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija
mana dariyar ‘yan baqin ciki. Da ma gashi jikin
dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda
aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da
hankali, suka fita, suka tafi.
Sha biyu da kusan minti arba’in na dare lokacin ne
Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga
bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa.
Na’ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da
jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa
kiranta. “Na’ima in na shigo sai na ci miki mutunci.
Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da
kallo tun daga qasa zuwa sama. ‘yar mitsilar rigar
varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa
fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi.
Cikin wata kidima ya rungume Na’ima a zaton ta
abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi.
Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta
mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin
dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni.
Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna
qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na’ima tana kukan
Chapter 51 · 0% Book details