← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 89

Sashe 43

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

dai iyakacinsu banki don bazai yiwu suje zariya yau
ba, sai gobe, Daga nan yaje ya sai magungunan da
likitan ya rubuta masa wadanda bai samu acikin
asibiti ba. Sannan ya koma gida yayi wanka, ya
shanza kayansa zuwa farar jallabiya qal da hula ‘yar
fakistan. Ya fesa turaruka, sannan ya fito. Ya rufe
qofar zai fita saiga su inna zasu shigo. Ya tsaya suka
gaisa, sannan yace, daga unguwa kuke ne? Suka ce,
daga asibiti muke. Ai mun samu Amina. Yace to mun
gode, Allah ya saka. Sukace Ameen.
Fatu tace, umm. Wannan abu yaban mamaki Inna.
Me ya janyo wannan hadarin? Inna ta kalleshi, “ina
zan san abin da ya janyo. Kai sama’ila yaya abin ya
faru ne? Yace, tsautsayi ne kurum. Fatu tayi
murmushi. Zancen dake yawo a gari haka ne kenan.
Guduwa zatayi sbd bata sonshi. Ta kalleshi, kaima
kayi wauta Ismail. Dubi wannan Yarinyar, kallo daya
zaka san ta saba da hutu, amma ka cusa kanka. Da
ido kawai Ismail yake binsu. Kuma bai shirya ce
musu komai ba. Yasa kai ya fita. Tsaki Inna taja
“Mtsss” sannan tace, aishi tsiyar sa kenan. Qarya ne
kaji cikinsa.
Shidai ya sani. Inji rashida, daya matar wan nasa.
Matar musa ce kurum bata ce, komai ba don bata
cika shiga shirginsu ba. Sai da ya fita titi, sannan ya
kira Mahmud yake fada masa cewa, gashi zai koma
asibiti. Mahmud yace, to sai sun shigo Anjima shi da
rabi’a. Ya tare dan acha6a zuwa asibiti. Suna cikin
tafiya ne yana kalle-kallen sa, idanun sa suka sauka
akan wani super market. Yace ma dan acha6an don
Allah dan dakata in duba nan. Dan acha6an yace,
amma ba dadewa zakayi ba ko?
Daidai lokacin da ya tsaya, A’a insha Allahu bazan
jima ba, Ismail ya bashi amsa bayan ya sauka daga
mashin din. Ya shiga tafkeken super market din
tunaninsa kawai ya sayi abinda mimi zata iya ci ko
sha. Da makilin ya soma cin karo, gasu nan kala kala,
ko wanne da kudinsa manne a jiki. Sai ya dauki mai
tsadar ciki, ya sai brush da sabulun dettol na wanka.
Sannan ya koma gurin kayan sha. Ya rasa wanne irin
drink take sha. A qarshe sai ya dauki maltina a nasa
tunanin kowa yanasha. Ya sai katan din ruwan gora
guda biyu, sai kayan tea na manyan gwangwani. Suga
na kwali. Ya sai flask din ruwan zafi. Daya fito wajen
gurin ne kuma ya isa gurin masu saida kayan
marmari, ya sayi Apple, lemon zaqi, sai kankana da
abarba. Dan acha6a yace, gsky malam za fa kaimin
qarin kudi. Ismail yace, babu komai, Allah dai ya
kaimu lfy.
Da kaya niqi-niqi ya hau samansu, gabansa har
faduwa yake yi daya tunkaro asibiti. Haka dai ya nufi
dakinsu, tunaninsa a wane hali zai samu mimin aciki?

Don yasan zaiyi wuya in bata farka ba. Ya tura qofar
cikin sallama, k idanunsa suna kan gadon. Yaya
Amina ta amsa Sallamar tana kishingide a dayan
gadon. Yace sannu yaya na barki ko? Ta sauko tana
tana fadin, banyi zatonka a wannan lokacin ba, ko
har kunje zariyan? Ya nufi gadon mimi yana cewa,
mun bari sai gobe, sbd yau yamma tayi. Bata farka
bane? Yaya Amina ta iso gaba gadon.
Tace, ta farka, ko ido bata bude ba, kuka kawai take
yi. Don nima nishin kukan ta yasa nasan ta farka.
Tsaki yaja cikin damuwa yace, nidai Allah ya sani
wannan kukan yana damuna. Yasa yatsansa ya debe
mata gashin kanta daya watso kusa da idonta, ya
maida mata shi bayan kunnenta. Ya tsura ma
fuskarta ido, wadda tayi jajur don kuka. Idanunta
kuwa sun kumbura sunyi luhu-luhu. Ya dora tafin
hannunsa akan goshinta. A fusace ta bude idanunta,
qwayoyin idon sunyi jajur. Ta zuba masa harara,
sannan ta girgiza kanta, alamun ya cire mata
hannunsa daga goshinta. Yace bakisan in dafa miki
goshi ne?
To na cire. Amma ynxun ki tashi kici wani abu. Ya
rusuna ya soma ciro abubuwan daya siyo daga cikin
ledar. Yaya Amina tace, Yauwa yanada kyau ta wanke
baki kuwa, ga makilin da brush. Amma ka manta
baka siyo roba ‘yar mai fadi ba, da FO sbd fitsari, don
kaga tana varcin nan duk ta fitsare kayan jikinta da
na kwanciyr. Gashi Kaje gida amma baka dauko
mata kayan sawa ba. Ismail yace, fitsari kuma? Ya
dago ya kalli mimi, fitsarin lfy? Sabon kuka mimi ta
saka. Domin farkawar da tayi taji ta sharkaf cikin
fitsari ya tada mata hankali.
Wai ita mimi ce haka? Mimin daddy mai shanawa.
Sam bata son ta bude ido ta kalli asibitin bare malam
Ismail, wanda ta tsana fiye da kowa. Ta tuna lokacin
da tayi wani zazza6in mura, waje suka fita, can
England aka duba lafiyarta. Tunda ta taso, duk bayan
wata uku dad yake kaita a duba lafiyarta a qasar
Misra. Amma yau gata a wani qazamin asibiti kwance
cikin fitsari. Ina ma dai mutuwa tazo ta dauke ta. Da
ma da sukayi hadarinnan itama ta mutu da yafi mata
wannan Rayuwar.
Ismail yace, ba zaki yi magana a saki ba mimi? Yaya
Amina tace, haba Ismail, Kalli yadda take mana
qafafu a sagale taya za’a sata tayi fitsari? Yace hakane.
To ynxun sai dai ta dinga yi a kwance? Yaya Amina
tace, dole a samu robar fitsari, amma mu nemi
Shawarar likitan. Ismail yace, to zan sameshi. Amma
ynxun ya kk ganin za’ayi gurin cire mata kayan? Ko
inje in fara dauko mata wasu in dawo?
Yaya Amina tace, to kayi sauri don inason inje gida
sbd abincin dare. Insha Allahu yanxun zan dawo.

Duk akwatunanta ya chaje su tsaf, babu riga da zani,
mafi yawa daga cikin kayanta ‘yan kanti ne, riga da
wando, sai dogayen riguna. Na atamfan ma daga
doguwar riga sai riga da siket. Tsaki yayi, cikin haushi
ya bude qaramar Jakarta, wadda ta dauko zata gudu
da ita. A ciki yaga Jakarta wadda ta zuba kudadenta
data debo sbd guduwar su.
Ya ciro jakar yaje ya daga can qasan katifarsa ya sata
cikin tsohuwar malum-malum. Ya daga ledar tsakar
daki, ta qasan katifar ya saka, sannan ya maida
katifar. Yayi hakane sbd tsoron 6arayi, tunda shi ba
wai yana kwana a gidan bane, kar a zo a bude dakin.
Ya dawo ya bude akwatin da yaga kayanta na ciki.
Aciki ya ciro siket da dan kanfenta, sai best. Baisan
meyasa ya zuba ma rigar mamanta ido ba, qila kyau
tayi masa, amma duk da haka bai dauka ba.
Qamshin turarenta kayan sukeyi, sai ya dauki ‘yan
shirt guda uku, tunda babu zannuwa. Yace zaibi ta
bakin kasuwa ya sai turmin zani ya tsaga su gida uku.
Ya dauki bargon rufarsa da zanin gado, sannan ya
nufi kasuwa, daga can ya wuce asibitin. Yauma ya
hangi innar su Zainabu acan baya gurin wanki.
Yauma haka ya hau sama yana tambayar kansa wai
wa take jinya? Ya samu yaya Amina da taimakon
nurse din dake aiki a wannan lokacin suna cire mata
kaya. Ido hudu sukayi da ita, lokacin daya shiga an
cire mata riga. Cak ya tsaya, domin idanunsa sun
kalli abinda bai ta6a gani a fili ba
Runtse idanunsa da yayi, sunzo daidai da ihun data
yi. Yaya Amina tace, “mun yi miki fami ko? ” Malam
Ismail ku rufemin jikina. Tun farfadowarta, sai ynxun
tayi magana. Ismail ya ajiye kayan hannunsa a gurin.
Idanunsa a Runtse ya juya. Sannan ya bude idanun.
Abin daya gani suna yi masa gizo. Ya fita kan benci,
ya zauna tare da tura hular kansa baya. Sannan yasa
hannunsa ya shafe fuskarsa. Wani yanayi ya samu
kansa a ciki, wanda ba zai iya tantance shi ba. Wata
zuciyar tace, ba fa haramun ka gani ba, duk ka rude
haka, matar kace.
A cikin dakin kuwa, yaya Amina ce ta zo ta dauki
kayan da uwanta ya ajiye taje kan daya gadon ta
zazzage su tana dubawa tare da cewa, shikenan
tunda ya fita sai kiyi haquri. Nurse tace, wane haquri,
ba kunce mijinta bane? Yayan tace ai bata ta re bane
shiyasa. Nurse tace, to kuwa kina da aiki. Mimi dai sai
kukanta takeyi, saboda baqin cikin qirjinta da malam
Ismail ya gani, har suka gama kintsa ta bata daina
kuka ba, sunce zasu sa mata robar fitsari, tace ita dai
bata so, Nurse din ce taba yaya Amina Shawarar su
sai mata pampers na manya. Shi sai dai kawai a cire
a yar, ayi mata tsaki, yaya Amina tayi mata brush,
taqi cin komai, sai ruwan data sha kusan rabin gora.
Chapter 43 · 0% Book details