← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 89

Sashe 23

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sha.ya bar ta yashe ba kulawa bare tausayawa,ya nufi dakinsa. haka ta kwanta babu barci sai kuka take yi.ya fita da wuri,don haka hajiya lndo ce uwargidansa ta zo ta duba ta,ta dafa ruwan zafi ta taimaka mata,ta ba ta abin kari.tsawon sati guda da yayi a dakinta bai raga mata ko sassauta mata ba.haike mata kurum yake yi.don haka ta sha azaba.tsoronsa da tsanarsa sun dasu cikin zuciyarta. khalil ya yi nasarar goge dan imanin MIMI da dan tauhidin da lsma'il ya soma cusa mata.ya zuwa 'yan kwanakin da suka biyo baya,sun yi nisa cikin tsarin yadda za su gudu.ko yanzu da suke yin waya fada mata yake yi,ta nuna cewa ta amince sai daf da auren sai su gudu.suna da bukatar kudi kafin ranar.ya ce,zan dauki sarkar mamana in kai kasuwa in sai da,sbd dad dinmu ba shi da kudi a gida sbd siyasarsa din nan.MIMI ta ce,kai baka da naka kudin ne?ya ce,account dina babu kudi,bai fi dubu ashirin ba.dad baya zuba mana kudi. [01/10 9:45 pm] Abdul: (2)Dad baya zuba mana kudi sosai yanzu saboda siyasa.ta ce,ka bar shi,ina da kudi a cikin karamin account dina.kamar nawa za mu rike?ya ce,muna bukatar kudi sosai,sbd za mu kama guri mai kyau ne a wani state din wanda ba za su yi tunanin za mu je ba.MIMI ta ce,ok,ka samo,ni ma zan samo,sai mu hada.ya ce,shi ke nan sai mun yi waya. bayan sun yi bankwana ta soma tunanin yadda za ta kwashe duk wani abu nata mai amfani.matsalarta daya.kudinta masu yawa suna cikin babban account dinta.ln kuma ta taba dole ne mahaifinta ya ji alat. Momy nafisa an dawo daga dubai,'yan gidansu abbas sun kawo kayan lefe.ran hajiya sauda ya baci da yadda alhaji ya nuna mata.matsayinta na wadda ta haifi MIMI ya kyautu a bata hakkinta ko da na shawara ne,amma alhai yayi mata dif,tunda ta ce baza ta shiga lamarinsa da MIMI ba,ita 'yar ba da shawara ce.bata fadi hakan da wata manufa ba, sai dai nuna ma alhaji kurensa,amma ya dauka da zafi,don haka ta lashi takobi ita da yaranta babu inda za su je,domin auren abba a nan katsina aka yi shi,na MIMI in baza a kawo nan ba,to su je can su yi kayansu. biki saura kwana goma MIMI ta yi wanka,ciki sauri ta zura doguwar rigarta atamfa,sai dan bakin karamin mayafi. takalmi mara tudu ta saka,ta kwashi katinta na ATM daga jakarta da take zuwa banki,ta zuba su cikin jakarta da takan je saloom,ta ra aya takar.ta kwashi wayoyinta.tana sauka kasa,momy zata hawo saman ta ce,aa sai ina haka MIMI? ta ce,za ta je saloon.na'ima ta ce yayi wuri sis.saura kwana goma biki fa?MIMI ta tabe baki,ke kika san da wani biki,ni kam ban san da shi ba. momy nafisa ta ce,ki zo ga tela,zai gan ki sbd dinkunan kayan biki,kin ki zuwa ki ga kayan ki.MIMI ta ce.momy har da ke a wannan maganar bayan kin san komai?ni fa ba son shi nake yi ba.momy ta sassauta murya,yanzun dai ki bi ni kawai.ln lokacin da za ki ce wa alhaji baki son abbas yayi,zan sanar da ke ki tubure kawai.a ran MIMI ta ce,ke ma baki san namu shirin ba.a fili ta ce, [01/10 9:45 pm] Abdul: (3)A fili ta ce,shi ke nan momy.tela ya gwada MIMI sosai.kafin ta fice,makullin motar momy ta dauka ta fita.lta ta ja motar zuwa bankinta na karamin asusunta,inda ta kwashe kudinta kaf.ta nufi babban asusun da ke wani bankin daban,ta dibi dubu dari biyu.za ta kara sai kiran dad ya shigo.ta daga ya ce,MIMI kina ina ne?ta ce, ina banki ne.dad ya ce,yaya kika taba wannan account din MIMI?ta ce,dad ba ni da kudi ne,kuma zan yi gyaran jikina ne.ya kalli alhaji akilu,ya ce,shi ke nan ya isa,ki bari zan ba ki kudi. kar ki kuma cira daga wannan account din,ina son yi miki wani tsari ne da kudin.za ki yi kasuwanci kina daga gida,kuma na manyan kudi kin gane?MIMI ta ce,eh dad ba zan kara cirewa ba.ya ce,shi ke nan. alhaji bishir cikin dariya ya ce,ka ji 'yar kwal uba? wai tana fadin bata so,amma ta zo tana dibar kudi wai za ta yi gyaran jiki.suka sa dariya.alhaji akilu ya ce,me na fada maka?kiyayyar mata ba ta zuwa ko'ina.amma shi ma abbas din ai shi ya dace ya ba ta kudin gyaran jikin. alhaji bishir ya ce,ai ita da shi duk daya ne.ka rabu da shi,zan ba ta.alhaji akilu ya kira layin abbas.bayan ya dauka,ya ce abbas ya baka bai wa amaryarka kudin gyaran jiki ba?abbas ya ce,dad ta ki ba ni damar in san abin da take bukata ne.amma zan ba ta anjima. ya ce,shi ke nan ka je ka ba ta.ka lallabe ta,ka san yarinya ce.abbas ya ce, insha allah dad. MIMI gida ta wuce ta adana kudinta da duk abin da ya kamata ta tafi da su,amma banda kaya. lsma'il ya dangana har zuwa ranar ashirin da tara da alhaji bishir ya yi musu albashi.duk da kin karatun da MIMI ta yi,bai sa alhaji canzawa daga dubu darin da ya alkawarta zai ba shi ba.lsma'il yayi ta juya kudin a cikin dakinsa,yana farin ciki.sam bai taba rika su ba a hannunsa ko na wani ma bare nasa.lalle goben nan sai katsina,ya je ya biya kudin gaisuwa,ya hada kayan sa rana,ya sai ma zainabu waya,yayi alheri,yayi sabbin dinkuna,yana ta baje burinsa.nan ya kira mahmud ya sanar da shi cewa gobe yana tafe. [01/10 9:45 pm] Abdul: (4)Tun dare yake ta shirin sa,washegari ya kira hajiya sauda ya fada mata cewa yau yana son zuwa gida ya ga 'yan uwa.ta ce ba laifi,sai ka iso.ln ka zo kuma don allah ina neman ka.ya ce babu matsala.sai dai ina son don allah ki sanar da alhaji sbd ban san lokacin da zai fito ba.ta ce,ya ba ka albashi dai ko?ya ce, wallahi ya ba ni.ki yi min godiya.ta ce,to zan sanar da shi yanzun nan. ba a yi minti talatin ba, sai ga hamisu direba ya ce lsma'il ya je in ji alhaji.a falo ya same shi.ya zauna,ya gai da alhajin cikin girmamawa.alhaji ya ce, sauda ta kira ni,ta sanar da ni cewa zaka je gida yau. haka ne?ya ce,eh alhaji.lna son in je in ga 'yan uwa ne. alhaji ya ce,da fatan ba mu takura maka ba ko?ina nufin ka ji dadin zama da mu?lsma'il ya ce,na ji dadi sosai.alhaji ya ce,to ina fatan za ka dawo.lsma'il ya ce,eh to,na ji ana cewa za a yi wa wadda na zo in koyar da ita aure,shi ne ban sani ba ko hakan yana nufin ni ma na gama aikina ke nan?alhaji yayi murmushi,ai in na lura ita din bata yin karatun,amma kannenta suna yin karatun. kana yi mana salla.ga yaran nan suna yin karatu sosai,suna yin salla a kan lokaci.wannan ya fi min komai.yanzun ma da ka ce zaka je gida din,na kira ka ne in ji ko kwana nawa za ka yi?lsma'il ya ce,to ina ganin dai zan yi kamar sati daya.alhaji ya ce,har sati daya?na zaci baza ka wuce kwana uku ko biyu ba.har me zaka yi haka?lsma'il ya ce,eh to ina so dai za a sa ranar aurena ne tukuna.alhaji yayi 'yar dariya,oho haka ne?to ba damuwa.allah yasa alheri.ya laluba aljihunsa,dubu biyar ya kara masa.ga wannan kayi kudin mota.ka amshi lambata gurin sauda.ln ya so in ka tashi kira na.sai ka kira ni kai tsaye,ba sai ka bita gurin hajiya sauda ba.lsma'il ya ce,to na gode sosai. bayanan fitarsa ne momy nafisa ta ce,na lura yaron nan yayi maka ko?alhaji ya ce yana da hankali sosai.lna son mutum haka.har gareji, hamisu direba ya kai lsma'il,bayan yayi sallama da dukkan maaikata gidan. [01/10 9:45 pm] Abdul: (5)Kowa yayi kewarsa, damuwarsu kar ya dade ko ya ma ki dawowa. shida na yamma daidai ya isa gida.matasan da suke zama a gindin bishiyar da ke kofar gidansu suna nan zaune kamar yadda suka saba.hirar ta kwallo ce sai ta siyasa.dukkansu sun juyo suna yi wa lsma'il sannu da isowa,bayan dayansu ya sanar da su cewa ga lsma'il nan ya dawo.ya isa gurinsu ya babba su hannu suka gaisa.suna ta yi masa murna da samu aiki a abuja. wasunsu har suna cewa.ustaz ka ga yadda ka yi kyau kuwa?gaskiya abuja ta amshe ka! shi dai godiya yayi musu,ya shige gida.kai tsaye cikin gidan ya shige.matan gidan suna ta haramar sauke girki, sallamarsa suka ji.fatu ce ta soma ganin sa.cikin irin faraar da bata taba yi masa ba ta ce,ga yan abuja,ga yan abuja!nan dai aka yi ta masa sannu da zuwa.ya amsa cikin jin dadi da mamakin fatu.a wata zuciyar ya ce,kila don dai ta daina ganin sa ne. dakin lnna ya shiga ya gaishe ta,sanan ya mika mata tsarabarsu.ya tashi ya koma dakinsa ya bude,yayi kakkabe-kakkabe a gurguje,sbd lokacin salla ya kusa.ya shimfida katifarsa,ya dauki bokitin ruwa wankansa ya kulle kofar da makulli,ya nufi cikin don yin wanka.da ya dawo,yayi alwala ya zura jallabiyarsa ya sake kulle kofa ya nufi masallacin kusa da su. bayan idar da sallar ya dawo ya zauna ya kasafta kudinsa,ya adana sauran ya canza kaya tare da fesa turarurruka masu kamshi.ya yi kyau matuka cikin shadda mai ruwan toka,ya murza hula.ya kosa ya ga zainabu,ga shi tunda ya shigo garin katsina yake ta neman layin mahmud. cikin nishadi yake takawa,duk da lokaci bayan lokaci gabansa yana faduwa.sam ba ya ganin nisan gidan su zainabu daga nasu gidan.a kafarsa ya taka.har ya je kofar gidan,sai kuma ya tuna bai zo mata da tsaraba ba.don haka ya juya,ya tare dan acaba ya hau,sai wani shago ya je inda ya siyo mata waya ta naira dubu biyar.ya sake komawa kofar gidan.kamar an turo shi,sai ga kanin zainabu.kafin lsma'il yayi masa magana har ya juya da gudu ya koma ciki.a ran lsma'il ya ce, [01/10 9:45 pm] Abdul: (6)Yawwa kira ta,kai ma ka zo ka dan ja wani abu.kwarai idanunsa suka kosa su ga fitowarta.cikin duhun zauren ya ga alamun fitowar mutum.a zatonsa zainabunsa ce,har da gyara tsayuwa. muryar mahaifiyarta ya ji daga sama tana cewa,sannu malam lsma'il da zuwa.cikin faraa ya ce,yawwa lnna. cikin girmamawa ya gai da ta.ta amsa.ta ci gaba da cewa,sai ka samu labarin zainabu ta yi aure ko?ledar wayar da ke hannunsa ta subuce,ta fadi a kasa.cikin
Chapter 23 · 0% Book details