← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 89

Sashe 33

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

yi ta tafi?na yiwa mahaifiyarta alkawari. mahmud ya ce,zo mu dauki mai gulf din can ya bisu.sun nufi gurin sai suka ga hamisu direba ana sa masa fasinjan abuja.lsmail ya ce,aa me kuma ka tsaya yi?ya ce,lodin abuja zan yi,in dan kara na mai,ln samu na batarwa.lsmail ya ce,sauke sumu bi su MIMI,ta gudu ga su can sun dauki hanyar kaduna. [01/10 10:35 pm] Abdul: (50)Nan da nan hamisu ya sauke su,lsmail ya shiga gaba,mahmud ya shiga baya.duk da halin da lsmail yake ciki bai hana shi ya yi wa hamisu direba nasiha ba.ya ce,hamisu tsakani da allah ban zaci kana cikin direbobi masu cin amanar iyayengidansu ba.sam bai dace ka yi lodi ba tare da izinin maigidanka ba.haramun ka ci.ai gara ka ce min in kara maka na mai.amma wannan cin amana ne.ya baka amana ne fa.ko ya san kana yi?hamisu ya ce,wai!ln alhaji ya ji ai na shiga uku. lsmail ya ce,ka gani ko?yana biyan ka hakkinka.hamisu ya ce, lnsha allah na daina.daga yanzun ba zan kara ba. Da yake hamisu gudu yake yi,sun hango su,har sun kusa zuwa daf da jun. MIMI ce ta gane motar gidansu.ta ce,ana bin mu. waccan motar gidanmu ce. nan suka kara gudu.gudun nasu yayi yawa.allah dai ya tsare...karan da suka ji shi ne ya tabbatar musu da cewa taya ce ta fashe ta su MIMI. daga inda suke suna hangen yadda motar take tuntsira gudi-gudi a kan titi.gaba dayansu suka hau salati.hamisu na cewa taya ta fashe shi. kuma ya taka burki.hankalin lsmail ya yi mugun tashi.suna isa gurin,motar tana tsayawa bayan ta tokari bishiya.suka fito suka nufi gurin.motoci suka tsaitsaya ana ta kokarin ciro su.duk jikin lsmail bari yake yi.wasu na cewa tun dana ga tukin da yaron nan yake yi na san zai yi wuya basu fadi ba. Nan zan dan huta.sai mun hadu a kashi na uku don jin shin su MIMI za su rayu?ln sun rayu,yaya zamansu zai kasance?wai na'ima ta ci nasara da ta hau saman abbas?mene ne labarin zainabu? Taku Halimarku K Mashi. sai na ji ku a 08081165107. lna jiran shawara ko korafi. CANJIN RAYUWA 3 Halima K mashi Littafi na Uku Hausaebooks Shuraih 99% Daga:- http://keffiansonline.cf
Chapter 33 · 0% Book details