Sashe 36
Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Duk da ya nuna abin bai dameshi ba, amma jikin
nasa ya qara rikicewa, ynxun dai ya samu varci,
bayan likita ya gama dubashi. Na’ima cikin sauri tace
“sis mimi din ce tayi hadari momy? ” tace eh itace,
sake guduwa wai tayi, ita d wanda takeso din, sunyi
mummunan hatsari, shi wanda take so din ya mutu.
Na’ima tace innalillahi wa inna ilaihi raji’un! To
ynxun tana ina? Amma da sauqi ko? Momy tace,
dalla can, duk kin wani rude, ni ina zan sani? Dadyn
ku ya hana zuwa. Hamisu direban yara yace, tana jin
jiki. Na’ima tace Allah sarki sis mimi!
To shi daddy ya haqura mana, momy tace karma ya
haqura, su qarata can, kedai ki samu kija ra’ayin
mijinki, yadda zaki samu hanklin mahifinku ya dawo
kanki. Ni araina ma cewa nayi dama itace ta mutu,
Na’ima tace a’a momy kar ta mutu, tunda dai mun
samu ta barmin abbas din ba shikenan ba. Ki tayani
in shawo kansa, baki ga irin wulaqancin da yayi min
ba, tace shikenan zanzo da safe. Na’ima tace Yauwa
gara ma kizo kiyi masa magana, tace to shikenan sai
nazo din, sukayi saida safe.
Zainabu tana kwance akan gadonta, sai juyi takeyi,
cikinta banda hautsinawa babu abinda yake yi, amai
kawai take ji, amma ta kasa yi, ga zazza6i data kwana
dashi. Da qyar tayi sallah. Budo qofarta da akayi ne
yasa ta tashi a firgice, tasan Alhaji ne, kullum sai ya
shigo dakinta daidai wannan lokacin, yayi buqatarsa
da ita, kuma babu ruwansa ko da dakin wa yake
cikinsu, ya cire rigarsa ya rataye, tace don Allah kayi
haquri yau banida lfy, yace ruwa na da ciwonki?
Nima yau sauri nake yi, ba ddewa zanyi ba. Ya fado
kan gadon. Ji tayi aman da takeson yi tun jiya ya
taho. Nan kuwa tayi ta sheqo masa shi a jiki har kan
gadon, ji tayi turarensa dada hankado mata aman,
da sauri ya tashi ya wanka mata wani wawan mari.
Yana ta surfa mata ashariya. Ita dai amai take ta
wankawa, har saida ta amayar da duk abinda taci,
sannan ta kwanta tana maida numfashi. Shi kam da
zage-zage ya fita har xuwa dakinsa, ya wanke ya fito
ya nufi gurin wacce zainabu take bi mata don kai
buqatarsa can tace, sai yau kasan dani? Tunda kayi
amarya ka daina shigowa da safe, yace ai tsiyarki
kenan mita. Ita wancan har mace ce da har zaki
damu kanki? Yarinyar da kullum saina dake ta ko na
zage ta sannan zan samu buqatata. Wai ahakan ne ta
kama amaye amaye, in dai ciki ne zanci mutuncinta,
sbd ban mori kudina ba. To bata sonka kai kuma ka
nace, in bata sona ai tanason kudina ko? Ba sai a
faranta min na kudina ba, sisina bazai yi ciwo ba.in
ba zata zauna ta faranta min rai ba, to zasu bani ‘yan
kudina.
Uwar ta ga roqon tsiya, ko jiya saida ta aiko wai in
bata dubu goma. Kuma kabata? Ta katseshi. Yace
dan iska ne ni, dari biyar na bada aka kai mata. Wane
farin ciki nake samu gurin ‘yarta da har zan dinga
bata kudi? Tace inace ka bata ne,nima ince akai wa
uwata.
Yace ke har kinyi magana? Ko wata uku ba’ayi ba,
tsohonki ya dage saida na sai masa mashin, tace eh
amma kayimin gori yafi sau dari akan mashin
dinnan, kai matsalar ka kenan gori duk wanda kaba
abinka to ya tabbata zaisha gori, yace eh amma su
kuma iyayen naku rokonsu yayi yawa. Ni muje kinji,
sauri nake zan fita.
Alhaji lawal kenan, sam bai damu dayin al’amuransa
bisa tsarin addinnin musulunci ba bare bin doka.
Rayuwar gdansa yana tafiyar da ita bisa son zuciya,
shi ganinsa, kudi za suyi masa maganin komai, bai
qara bi takan zainabu ba ya fito. Shirun da uwar gd
maman bushira taji, yasa ta leqa dakin tana cewa,
amai kkyi haka? Kai ta daga, alamun eh, maman
bushira tace anxo gurin kenan. Ta kama ta, tashi in
taimaka miki, ban daki takai ta tace ta wanke jikinta.
Ita kuma ta koma tana kwashe kayan gadon, saida ta
gyara ta, sannan tasa aka kawo mata abin kari. Da
qyar ma tadan kur6i ruwan kunu.
Ta kalli uwar gdn, maman bushira me yasa kk ce
anzo gurin? Uwar gd tace alamu sun nuna cewa
kinada ciki ko? Zainabu ta zaro ido, nima ban sani ba.
Uwar gd tace gsky ina zaton ciki gareki. Yaushe
rabonki da al’ada? Zainabu ta sunkuyar da kai, fashin
sallah kuma? Eh, inji maman bushira. Tun ana saura
kwana biyar bikina. Maman bushira tace tabbas ciki
ne dake, abinda yasa nace haka, sbd Alhaji baya son
haihuwa. Zaki fuskanci wulaqanci sosai.
Zainabu tace, banda wannan wulaqancin, har akwai
wani kala da zai min? Maman bushira tace sosai ma
kuwa! Amma Shawarar dazan baki, in ya tambayeki
cewa kina da ciki ne? Kice masa a’a shawara ke
damunki, Zainabu tace sbd me to? Tacesbd zai baki
maganin zubar da ciki. Zainabu tace zaifi murna, in
har cikin ya zube, maman bushira tace ai ba wannan
ne matsalar ba. Matsalar zaije ya kawo miki magani,
kuma ba wai zai kaiki asibiti bane. Akwai wata
yarinya daya ta6a aure, haka akayi qarshe Yarinyar
rasuwa tayi, sbd jini ne ya 6alle mata.
Tace to in na 6oye masa, kuma yasa aka kaini asibiti
aka gano cewa inada ciki fa? Maman bushira tace
bazai gane ba. Don ba zai kaiki asibiti ba, don kuwa
baya daga cikin mazajen da suka damu da lafiyar
iyalinsu, don ko panadol sai dai ki saya. Zainabu ta
soma kuka tana fadin dole zai sani, tunda cikin zaiyi
girma, maman bushira tace kafin cikin naki yayi
girma, da ace zaki iya sakin jiki dashi kema ki sauko,
ki tarairaye shi, to da kin yagi na xuwa asibiti, dana
kayan jariri. Zainabu tace, nayi ta qoqarin in
kwatanta tun kwanaki da kk fadamun, amma na kasa
sakin jiki dashi, don inada wanda nake so, kuma yake
sona. Tace shikenan zako kiyi zaman wulaqanci, duk
ranar daya gano akwai wannan cikin, sabulun wanka
sai kin rasa. Zainabu tace zan kwatanta in gani ko zan
iya. Maman bushira tace da dai yafi miki. Ranar
Zainabu wuni tayi sheqa amai da kuka. Ta galabaita
sosai, da magriba ya shigo ya ganta kwance. Ya dube
ta a wulaqance, ke kuma kukan me kkyi? Tace
shawara ce, dama ko a gd inayi, yace oho’ to kina
shan wani magani ne in ya tashi? Tace eh, amma
banida kudi ban sayi na asibiti ba, sannan ina kuma
shan na hausa. Yace to ina kumazaki samu kudin na
siyen maganin, tunda ni dazan baki kin mai dani
kamar wani dodo?
Ta kalleshi, ai na bari, yace da gske? Ta sunkuyar da
kai, sannan tace eh. Yace kinyi alqawari? Ta daga kai,
alamun eh. Cikin yace to shikenan vari inzo in nemo
miki magani. Ko ke fa? Ynxun zaki san kinyi aure.
Amma zan vari yau ki huta tunda baki jin dadi,
amma gobe da safe zanzo ko? Tace eh, yana fita ta
nufi ban daki ta dinga kakarin amai, don gsky shi
kansa wari kawai yake yi mata.
Washe gari yana shigowa, haka tayi qoqarin yi masa
duk abinda yake so, tare da maida masa martanin
duk abinda yayi mata. Tasha wahala matuqa, amma
haka ta jure ta nuna masa tana tare dashi, yaji dadi
matuq a. Dazai fita ya kawo dubu biyar ya bata. Ya ce
ki jirani da daddare, gabanta ya fadi, tace a ranta na
shiga uku, a fili tace ai yau ba’a dakina kk ba, yace ina
ruwana da wani inda nake, karki damu, abinda kawai
na sani dukkanku matana ne, kuma zan shiga gurin
duk wacce raina ya biyamin ko kina da ja?
Cikin sauri tace, A’a haka ya fita ya barta tana
mamaki, tare da tambayar kanta wai daman haka
auren yake, ayi ta abu sai kace cin tuwo, kuma ba
gajiya? Ita kam ta gaji wlh. Ta dinga juya kudin a
hannunta, sannan ta bude akwati nta ta saka, tana
yin wanka, sai kuma zazza6i ya rufe ta, ta qudundu
ne akan gado cikin bargo. Bata san tsawon lokacin
data dauka ba akan gadon nata. Can kamar daga
sama sai taji muryar su innarta suna salalla ma.
Da sauri ta tashi suka shigo, itace da aminiyarta inna
yelwa. Suka iso bakin gadon suka zauna. Inna tace
lafiya na ganki cikin bargo haka? Zainabu tace banida
lfy ne inna, tace me kuma ke damunki? Ta sunkuyar
dakai, tace wai uwar gdnsa ce tace ciki ne dani, shi
kuma gashi baya son haihuwa, inna tace to ynxun
daya ji kina da cikin me yace?