← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 89

Sashe 15

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

banza zaa ba ka dubu dari?ya ce,in na fasa koyarwar fa?ta ce,ka rasa,zan fin son ma ka ce ka fasa,don ni dole idanu na suke kallon fuskar ka,kuma bana son in kore ka saboda hajiya zata yi min fada,amma in ka tafi da kan ka shikenan. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (64)Ya ce,yanzun zan kira hajiyar in fada mata komai,gabanta ya fadi,ta yi shiru cikin fargaba. ya ce,zan fada mata komai don kar ta zarge ni,ta ce,bari in riga ka fada mata,ga mamakinsa sai ya ga ta saka wayarta a handsfree ta kuma kira layin hajiyar,ba ta jima tana ringing ba ta daga.sun gaisa ta ce,ya ya kuwa karatun ki na yi?ta ce eh! hajiya yanzu haka ina kan yin karatun,na kira ne nayi miki godiya,ki yi wa malamin godiya in kun yi waya,don ina fahimtar karatunsa,ta ce,ai lsmail yana da himma ALLAH ya taimaka,ta ce amin,suka yi sallama. ta kalle shi,ka gane nufi na?na san yanzun dai za ka ji nauyin ce mata bana karatu,tunda na ce ina fahimtarka,ka ga kenan sai ka nemi dalilin ka na kin koyar da ni da zaka yi,yayi banza da ita ya ci gaba da kallo agogo minti goma da suka rage sun yi mishi nisa,sai da ya ga saura minti biyu,ya kalle ta, tana ta chatin,ya ce,ki yi amfani da lokacin ki tun kina da kuruciyarki,ki nemi sanin addininki sannan ki bauta ma ubangijinki kafin lokaci ya kure miki.ta ce,kai har ka samu sake da yawa irin haka ne?ganin ka ka kai ka dinga fada min magana son ranka ne?ya yi murmushi,in kin gaji da kallon kyakyawar fuskata zan tafi,don lokaci ya cika, kin san lokaci baya jira. Ta mike tsaye,shima ya mike tare da kwasar littafansa,ta ce,har wani kyau ne da kai? [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (65)Dube ka,ya ce, sosai kuwa,don na san nafi ki nesa ba kusa ba.ta ce, karya kake yi,na sha jin mutane suna gulmar kyau na,ban da wadanda suke fada a gabana.ya yi 'yar dariya,da son ya cusa mata takaici,sanna ya ce,ina zaton suna tsoron ki ne,ko jin nauyin ki,ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau su fada maki tsakani da ALLAH.ya kalli agogo,kash har na kara minti biyu,ya face,kafin ta kai ga cewa wani abu, ranshi kar,ya san cewa ya guma mata.don ya san mata ko basu da kyau,sun tsani a fada,shi kuma yayi ne kawai don shakar da ita,bai yi nisa ba,ya ji ta saka kuka,sauri ya kara ya fice daga gefen na su. Mommy nafisa ta fito da sauri jin kukan MIMI, abinda ta dade bata ji ba, ta ce, mene ne?MIMI ta ce, mommy kalle ni sosai da gaske bani da kyau? mommy ta ce,in ji wane makahon?MIMI cikin shagwaba ta ce,wancan talakan malamin mana, mommy nafisa ta ce,barshi kawai karya yake,MIMI ta ce,bari dad ya dawo dole ne malamin nan yayi kwanan cell,mommy ta ce,ki share shi ne kawai, hajiya sauda ba za ta ji dadi ba,in har ki ka kai shi gurin 'yan sanda. MIMI ta yi samanta cikin matsananciyar damuwa,kai tsaye dakin ta ta wuce,sai gaban madubin ta na jikin sif dinta,don shine zai nuna mata siffarta tun daga sama har kasa,ta dinga juya kowane gefen ta tana kallo,zantukan malamin suna yi mata yawo a cikin kai.ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau,su fada maki tsakani da ALLAH,wadannan kalaman sun sa ta a cikin rudani,ta dauki wayarta,ta kira layin na'ima,bayan ta daga ta ce, ki je ki ce ma hamisu direba zamu fita,na'ima ta ce to sis,ni ma zan bi ki,cikin tsawa ta ta ce,aa ki je aike na kawai. gidan su amina dakingari ta nufa,mina ta yi mamakin ganin MIMI ba ko sanarwa,bayan sun shiga daki,MIMI cikin kuka ta ce, mina don ALLAH ki fada mun gaskiya tsakani da ALLAH.mina ta dafe kirji,me ya faru MIMI?MIMI ta ce,ni dai ki fada min,ina da kyau?,mina ta ce,ko makaho ya shafa,MIMI ya san kina da kyau sosai ma. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (66)Wai duk me ya kawo wannan tambayar? MIMI ta ce,hum!wannan malamin ne talakan banza nan dai,MIMI ta sanar da ita yanda suka yi.mina ta yi tsaki,na zata ma wani na kirki ne ya ce miki haka,ya fada ne kawai don ya baki haushi.ke to me zai dame ki tunda ba khalil ba ne ya ce baki da kyau!ln duniya za a taru a ce baki da kyau, na tabbata khalil ba zai ce ba. MIMI ta sauke ajiyar zuciya,ta isa gaban madubin mina tana kallon kanta,ta ce,mina cewa fa yayi kawai ana dai jin tsoro na ne ake cewa ina da kyau,mina ta zo ta dafata, kar ki ruda kanki MIMI,dube ki fa doguwa fara sal ga gashi har baya,idanuwanki masu haske.MIMI hatta hakoranki abin birgewa ne, so kar ki damu kanki.MIMI ta dauko wayarta ta soma kiran layin khalil,ta zauna daidai lokacin da ya daga ta ce,zan tambayeka wani abu,ka fada min gaskiya.ya ce,ina jin ki,ta ce,kana so na?ya tausasa murya,haba khadija wannan tambayar ai kin dade da sanin amsarta,amma in kina son in sake maimaita mi ke ne, sai in ce ina sonki,ina sonki sosai fiye da yanda ni ke son kaina,ta ce,saboda me kake so na khalil?ya ce, abubuwa da dama khadija, amma daga ciki akwai halinki da kuma kyawunki, MIMI ta ce,hali na kuma? khalil ko dai gaskiya ne mutane basa son fada min gaskiya?ban taba jin wanda ya yabi hali na ba, daga daddy na sai mommy nafisa,sai kai yanzun,ta kashe wayar,hawaye na zuba mata. Mina ta ce,MIMI kin cika son sama kanki damuwa, wani banza talala ya rikitaki duk ki damu kanki,ki dawo hankalinki mana? wayarta ta soma ringing ta duba ta ga khalil ne ta jefar da wayar.mina ta ce,shi kuma me ya shafe shi? MIMI ta ce,tsakanin da ALLAH mina kin taba jin wanda ya ce,ina da hali mai kyau?hatta mahaifiyata kullum fada take yi min in gyara hali na. ke ma in na yi wani abu,kina ce min irin hakin nan ba shi da kyau,amma yanzu khalik yana min wai yana sona don hali na. maganar malamin nan ta zama gaskiya,kenan masu cewa ina da kyau basu fada min gaskiya. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (67)Mina ta ce,oh my god,don ALLAH ki daga wayar khalil,in kowa zai ce halinki ba kyau,khalil ba zai gani ba,don so yana hana ganin laifi,ka da ki dama ma kanki lissafi,shawara ta ki kori malamin nan ki huta mana.MIMI ta ce,kina nufin khalil iyaka gaskiyar shi ya fada min?mina ta ce kina dai karatun englis novel na soyayya dama baki fahimtar komai?MIMI ta yi shiru tana nazari,can ta yi ajiyar zuciya,ta dauko wayarta daidai lokacin khalil ya sake kira.wanda ba ta san ko kira nawa kenan ba.ta daga muryarta tana rawa ya ce,khadija fada min gaskiya nayi miki wani laifi ne?ta ce,aa na i ka ce kana so na don hali na,ni kuma kullum kowa ce min yake ba ni da hali,fada min gaskiya.ya ce,ni halayen ki sun mini,ko da ba su yi ma kowa a duniya ba,zan iya yin komai a kan sonki,ki yi min izini in zo abuja mu yi magana a cikin tsanaki.ta ce,na fada maka dad dina bazai so ya ga ina hira da saurayi bai san lokacin da muka hadu ba,ka bari na bashi labarin ka,sai ka zo ku gana.ya ce,ko wani guri daban sai mu je, in na zo sai mu yi maganar kin ji?don ALLAH dama ina son ganin ki,ta yi shiru.can ta ce shikenan,gobe ka zo, amma zan turo maka address din gidan su mina sai mu hadu a can,ya ce, shikenan sai kin turo,ki kwantar da hankalin ki kin ji?ta ce,babu komai. mina ta riko mata hannu, kar ki damu da sauraran shi,ki kore shi kawai.MIMI ta ce,bani da damar yin haka, don dazun na kara daure kaina na fada ma hajiya cewa ina jin dadin karatunsa ina fahimta,in na ce a kore shi bisa ga wane dalili?mina ta ce,kin hadu da alakakai,ta tashi,bari in je gida,duk da haka zan nemi shawarar mommy nafisa a kan shi.lokacin da ta iso gidan mommy nafisa, mommy nafisa suna dakin na'ima suna tattaunawa a kan matsalarsu,wato MIMI, mommy ta ce,na'ima ai na ji dadin zuwan malamin nan,saboda na jima ina son in ga ran yarinyar a bace,sai dai ni bani da damar in bata mata.na'ima ta ce,don ALLAH mommy kar ki bari ta kore shi,ai ni ya birgeni da yake mata abinda take yi wa mutane. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (68)Kira da take yi wa mommymomy shine ya sa ta yin sauri ta fito daga daki,ta ce,ya ya ne MIMI,kin dawo?ta ce,eh,ni mommy kina ganin ba zaifi kyau in kori malamin nan ba? mommy ta ce,a'a bana son hajiya sauda ta zarge ni,don haka kiyi hakuri 'ya ta, bari in sa folina ta kira shi,in gargadeshi,don kada ya ci gaba da fada miki magana,ta ce,shikenan, amma ina son a yi mashi fadan a gabana don ya san ni ba sa'ar shi ba ce. Haka kuwa folina 'yar aiki ta kira lsmail,a gaban MIMI tayi mi shi gargadin kar ya kara cewa ba ta da kyau.ya ce,lnsha ALLAHU, ko ba komai dai lsmail ya ji dadin bata mata ran da yayi. A katsina kuma kwana biyu da tafiyar lsmail zainabu ta soma yin tallar ta,kuma a ranar ne ta hadu da wani alhaji,babban mutum ne a shekaru haka kuma a aljihu.direban shi ya tura ya tsaida ita,ya tambayi sunanta da kuma gidansu,ba ta boye ba don mahaifiyarta ta shirya mata cewa,ta saurari duk wanda ya zo,tunda lsmail ba ya gari,a nan ma za su samu kudin siyan mata kayan kicin.zainabu tana son lsmail sosai,don haka ta yarda tana son ta ji ana yin zancan auran su.alhajin ya zo da dare kuma ya tura uwar da kanta ta dinga gyarawa zainabu kwalliya har zaure ta rako ta, tamkar ta bi ta wajen a yi hirar da ita,tunda 'yar ta ba ta labari,ta ji a jikinta cewa irin wanda ta ke so ne ya zo.alhajin yaji dadin fitowar zainabu,don yarinyar ta yi masa,ya ce mata auranta zai yi,shi sunansa alhaji lawal,ta ce,ta yarda,da zai tafi nan ya cika su da kudi masu dama,wanda suka sa mahaifiyar rawa,ta kuma yarda cewa 'yarta ta samu miji. washegari da safe lsmail ya kira mahmud
Chapter 15 · 0% Book details