← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 89

Sashe 48

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

daya.
Ta fito tana tunanin ina zata nufa. Tafe take sannu sannu tana ‘yan waige-waige. Daga baya ta yanke
shawarar tambayar dakin ‘yan hadari. Dan haka sai
ta tun kari wata nurse. Tayi mata sannu, ta amsa.
Sannan tace, don Allah inane dakin ‘yan hadari?
Nurse din tace, mata ko maza? Zainabun tace “mata.”
Nurse din ta nuna mata. Zainabu ta nufi gurin a cikin
zullumi kala-kala. Shin zata gashi ko ba zata ganshi
ba? Matar tashi ta fi ta ko bata kaita ba? Ta shiga,
dogon falo ne kamar nasu, kwakkwance da marasa
lfy gado-gado. Tabi tana yi musu sannu, tare da
tambayar matar Ismail, amma har ta gama dubawa
bata ganota ba.
Ta fito ta tafi tana waigen dakin. Yinin ranar cikin
damuwa tayi shi, don ko ‘yar shinkafa da waken da
innarta kan siyo mata taci, yau kam kasa ci tayi. Da
magriba, innarta ta nufi dan lungun da sukan
shinfida tabarma suyi sallah. Ita kuma zainabu ta fito
ta sake zuwa dakinnan na ‘yan hadari. Bata shiga ta
qofa ba, window qarshe ta nufa, ta dafa windon tana
leqen mara lafiyar dake kwance a gadon. Zuciyarta
ce ke zargin cewa, lallai wadda ke kwance a Gadon
nan ita ce matar masoyinta. Bisa dalilinta na ganin
cewa, kaf dakin itace yarinya qarama. Sannan da safe
da tazo babu mai jinyar ta a gurin gadon su, sannan
da tace mata kece matar malam Ismail?
Kai kurum ta girgiza alamun a’a. Ita kuma sai take
qara dogara da cewa, batason sa shiyasa shine dalilin
da yasa tace a’a. Fatanta ace Ismael yana gurin ta
samu ta dan ganshi ko zataji sanyi. Sai dai tana
leqawa taga wata gyatuma zaune kusa da Yarinyar.
Tayi ta leqe-leqe kusan minti biyar. Ko mai kama da
Ismail bata gani ba. Taja silifas dinta zata tafi dakin.
Daidai kwanar da zata kaita babban daki, inda suke
kwance, sai ta hango Mahmud shida rabi’a,
budurwarsa, don ta san ta, itama ‘yar islamiyyarsu
ce, sai dai ita, ‘yar babban aji ce, ajin da Ismail ke
koyarwa.
Da sauri ta shiga kwanarsu ta juya baya, sam su basu
ganta ba suka wuce. Ta fito ta bisu da kallo, yana riqe
d kula ita kuma da leda mai dauke da lemu da ayaba.
Wata zuciyar tace, ki bisu mana, kinsan dai babu
gurin wanda zasu, sai gurin masoyinki. Da sauri tabi
bayansu, sai taga sun nufi wata matattakala. Itama
sai ta bisu har suka hau saman. Wata qofa suka
shiga, dan tsayawa tayi kamar mai tsoron binsu don
batasan yaya cikin qofar da suka shiga take ba. Sai
kuma taga ashe dogon guri ne mai dauke da dakuna.
Can ta hango su sun kusa kai qarshen dakunan. Don
haka ta shiga itama cikin azama. A tsorace take tafiya
har takai gurin da Nurses masu kula da wannan

sashen suke zama. Yadda take tafe tana waige-waige
ne yasa wata nurse tace, ke ina zakije? Nan Zainabu
ta daburce, ta soma inda-inda, “am zan..zanje can
ne. Yin me? Nurse din ta katse ta. Duba mara lafiya
zanyi. “ya sunan wadda zaki duba? Zainabu ta sake
rudewa, ni ban..bansan sunanta ba. Nurse din tace,
daga ina kk? ynxun bama yarda da mutane, sbd
rashin gsky yayi yawa, don ko jiya an saci Jariri a
dakin ‘yan tiyata. Zainabu ta firgita. Nima nan nake,
can dakin ‘yan 6ari aka bani gado. Dan uwana ne
matarsa take nan tayi hadari. Shi sunansa Ismail.
Nurse tace, ok na gane shi, wani ustaz haka ko?
Zainabu tace eh, shine. Ta nuna mata, ga dakin can
na qarshe. Zainabu tace, nagode sannan ta sauke
ajiyar zuciya.
Cikin fargaba ta doshi dakin. Zuciyar ta tana
tambayar ta me zata ce, in ta shiga? Ta kalli jikinta,
dube ni sai kace wata tsohuwa. Gabanta yana
tsananin faduwa, don haka sai ta fasa shiga, ta
window taje ta leqa. Tana iya hango Mahmud da
Ismail suna zaune bakin wani gado. Rabi’a kuma ta
zauna kan kujera ta kare fuskar mara lafiyar. Sai dai
tana ita kallon qafafun mara lafiyar akan gado.
Zuciyar ta ta tsananta da bugu, sakamakon Ismail
data gani, hawaye suka soma sharara akan
kumatunta. Can kuma sai taga Ismail din ya bude
kular da ta gani ahannun Mahmud ya zuba acikin
plate. Bata dai san ko menene ba. Tana kallo, yazo ya
dagata ya jingina. Tana ta son taga fuskarta, amma
gashin kanta mai tsawo ya bazu ya tare. Rabi’a ta
tashi, shi kuma ya zauna yana bata a baki kan bencin
dake gurin.
Ta koma ta zauna kuka sosai takeyi. Daga bisani ta
miqe, ta tafi tana kuka. Bata damu da mutanen da
suke kallonta ba. Wasu a zatonsu ko mutuwa akayi
mata, sai suce, “Allah sarki! Allah ya jiqan rai. Tana
saukowa taci karo da innarta tana nemanta. Tace ke
ina kk shiga ne, inata nemanki? Zainabu bata kulata
ba, ta wuce. Tsakiyar gadon ta zauna tare da dora
kanta akan gwiwoyinta. Matar kusa dasu tace, wai
Zainabu lafiya kk wannan kukan? Yau tun safe kk
cikin damuwa. Innarsu ta qaraso. Wai Zainabu daga
ina kk da kuka? Cikin kukan take cewa, an cuce ni an
hadani da namijin da baisan darajata ba. Tunda nazo
asibiti ko sau daya bai leqo ba.
Innar taja tsaki, tare da ce mata, sai ki tona ma kanki
asiri kowa yaji. Ai duk laifinki ne tun farko da kk qi
nuna masa so. Zainabu tace, to ni bana sonshi, kuma
bazan koma gidansa ba. Inna tace, sai kiyi tayi. Ga
faten doya nan da mai
wancan gadon ta sammiki. Cikin takaici tace, bana ci.
Innar tace bari inci, dama ba qoshi nayi da tuwon da

wannan ta kusa damu din ta bani Zainabu ta zame ta
kwanta, idanunta na qara hasko mata Ismail dinta ke
baiwa matarsa abinci a baki. Ta tabbatar da irin son
da Ismail yake yi mata, da ace ita ce, qila ma sai ya
tauna a bakinsa zai bata. Tuno durowar da ake dora
abubuwan ci na dakin dasu Ismail din suke tayi
shaqe da abubuwan ci. Gashi a daki na
musamman. Su kuwa abincin da zasu ci ma sun rasa
mai kawo musu, sai dai maqotansu na kwanciya su
sam musu. Da wannan takaici Zainabu tayi varci mai
cike da mafarkan masoyinta Ismail. Mahmoud ya
kalli rabi’a kinyi qoqari domin mara lafiyar nan bata
ci komai ba tunda tazo asibitinnan sai yau da kika
kawo mata. Azaton Mahmud Ismail baijishi ba
yanayin jinjina ne ga masoyiyarsa. Sai kurum yaji
Ismail ya cafe da cewa, ni kaina na jinjina miki rabi’a
domin a tarihin mami abincinki ta fara ci. Sai dai
abinda basu sani ba mimi mayyar kifin ruwa ce,
kuma farfesunshi rabi’a tayo da alayyahu.
Haka nan ta dai yo ne don batasan me zata yi ta
kawo ba. Yayanta masunci ne, in yayo fatsa yana
saida ma masu suyar kifi. Shine tace ya dan sam
mata zata girkawa mara lafiya. Sai gashi ta kawo a
daidai. Mimi dai tana jinsu bata ce komai ba, sai data
qoshi sannan tace, ya bata ruwa. Tasha sannan tace
zata kwanta. Tun lokacin da likitan ya taimaka masa
suka shawo kanta bata qara yi masa gaddama ba sai
dai kuka. Sannan bata magana sai in tana da
buqata. Ko da suka tafi zariya shi da Mahmud ya
barta tare da yaya Amina da suka dawo ta fada masa
cewa, batayi kuka ba hakanan ta yini shan ruwa,
kuma sun saka mata pampers ita da wata nurse.
Harma mimin tace, su sake canza mata rigarta. Yaji
dadin sannan ya dawo da murna sun samu
admission islamic ya nema. Mahmud kuma sai suka
bashi English baiso ba amma hakanan ya haqura.
Mahmud sun kai kusan qarfe goma sannan suka fito,
Ismail ya rakosu, saida suka hau mashin din
Mahmud sannan ya dawo. Sannu yayi ma wadannan
Nurses din na gefensu da zai wuce, sai dayar take
tambayarsa dazun wata ‘yaruwarka ta gane gurin ku
ko?
Ismail yace, da yau she kenan? Tace dazun nan kuma
nice nayi mata kwatancen dakinku. Ismail yayi shiru
kodai rabi’a ta gani da Mahmud. Yace ita da Abokina
dinnan ko? Nurse tace, a’a ita daya ce tace, tana nan
asibitin ne dakin masu 6ari. Ismail ya girgiza kai.
Gsky babu wanda yazo. Dayar nurse din tace, naga
lokacin data dawo tana kuka, sai nayi zaton tana
tausaya ma wadda ba lfy dinne. Ismail ya sake
dawowa kusa dasu. Tace kuma mu take nema?
Nurses din Sukace, sunanka ma ta kira. Yace to gsky
Chapter 48 · 0% Book details