← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 89

Sashe 44

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Baiji fitowar nurse din ba, sai dai muryarta yaji tana
cewa, kana zaune anan ne? Ya kalleta, kun gama?
Tace eh, ya ce na gode. Tace ba komai, sai kaje kayi
lallashi, don shagwa6ar matarnan taka tayi yawa.
Hannu yasa ya shafa fuskarsa tare da yin guntun
murmushi. Ta wuce gurin aamansu shi kam ya kasa
shiga dakin.\Yaya Amina ta fito, cikin jin nauyi ya
kalleta. “tafiya zakiyi? “Tace, eh, kaga yamma tayi, ga
girki. Ummi ba girki ta iyaba. Nasan dai zata share
min gd tsaf, har ma ta hana su Saddam yimin wasa a
cikin daki. In ba ayi sa’a ba sai yayi ta dukanta.
Ismail yace, ai rigimar sako da sako na gurin saddam
da Ummi, kamar masu ganin hanjin juna. Tayi
dariya. Haka suke, amma in daya baiga daya ba, ayi
ta damuna, mama ina take, ko ina yake? Ismail yace,
haka suke fa. Cikin zaulaya yace to kisa abbansu
saddam ya qaro aure mana. Kin ga kin huta, baki da
tunanin yin wani girki. Tace oho, sakamakona kenan
nayi maka jinyar mata? Cikin dariya yace, yaya laifi
ne? Tace, ban sani ba, ni kaga tafiya ta, sai anjima.
Yace yaya ki vari sai gobe mana. Tunda ma da kayan
tea, sai in sha ruwan zafi. Tace shikenan sai goben.
Yace, zaki zo da wuri ne, sbd inason zamuje zariyar
nan. Tace, zanzo dai kamar qarfe goma. Yace, Allah
ya kaimu. Har gurin matattakalar ya rakata sannan
ya dawo. Tsaye yayi a bakin qofa yana tunanin yadda
zai shiga dakin. Daga bisani yayi ta maza, ya tura
qofar tare da yin sallama. Tana zaune akan gadon, an
cire mata qafafun daga sagalewar da akayi musu.
Sannan an dago gadonta, gurin kwanciyr, ta yadda
zata iya kishingida.
Ya kasa kallon fuskarta. Yace, meyasa bakici komai
ba? Ya isa gurin fridge ya bude, ya ciro gwangwanin
maltina. Kisha maltina mana? Tsakin da ta ja shine
yasa shi kallon fuskarta. Harara take ta zabga masa
da jajayen idanunta. Ya sauke idanunsa, yasan kan
abin da ya kalla dazu ne. Sannan ya sake kallon
fuskarta. “kiyi haquri, dazun bansan ana shiryaki
bane. Kuma ni banga komai ba ma.
Bata dai tanka shi ba. Yace, kisha maltina ko kadan
ne kinji? Tace, ni bana sha. Yace to fadamin kk so
kici? Ta soma kuka. Yace, kinga matsalarki. An ce
miki kuka yana maganin matsala ne? Wannan kukan
sai dai ya qara miki ciwon. Tace, ni da zan mutu sai
nafi murna. Rayuwata ba tada amfani. Yace sbd me?
Tace, khalil ya mutu. Shine kawai ya ragemin a
duniya. Ismail yayi murmushin takaici. Ko zaki bishi
ne? Ta Kalli Ismael a fusace, ai da ace inada izinin
tashi, to da tuni na fada ta wannan windon. Ismail
yace, in kuma Allah baiga dama ba, kk karye, kuma
yaqi daukan ranki, kizo kiyi ta jinya ba. Wai shin ma
in tambayeki, da kk ta burin mutuwa, me kk tanada

na ibada ko na alheri, wanda zaki kare kanki, ko
kuma ince wanda zaki amsa tambayoyi a gaban
Allah? Mimi ta sunkuyar da kai. Yace, inaso kisan
wani abu, fushin iyaye ba qaramin bala’i bane.
Dakin mutu a hadarinnan, kin tafi da fushin iyaye a
gudun da kk yi, kinsan illar dake cikin guduwar ‘ya
mace kuwa? Koda yake kece zaki bada labari tunda
gaki a gadon asibiti. Sannan gudunki na farko ma
nasan kin hadu da wani qalubalen, sai dai in ba zaki
fada ba. Ta daga masa hannunta mai lafiyar, ni bance
maka kaimin wa’azi ba. Da zama da kai a matsayin
miji, gara min mutuwa. Yace sbd me? Tace ni ban
son ka, na tsane ka. Ismail baya varin bashin
magana. Don haka yace, ashe duk daya muke. Nima
mimi bana sonki. Sam bakya cikin tsarin macen da
nake so.
A ra’ayina inason mace mai kyau, mai son addini,
kuma maijin maganar mahaifanta. Kalamansa sunyi
wa mimi zafi. Har ta kasa cewa komai, sai kai data
sunkuyar ta soma kuka. yasa hannu ya daga fuskarta.
Karki damu in kin samu sauqi, zamu san yaya za’ayi
,ta goce kanta da qarfi, kar hannunka ya sake ta6a ni.
Yace, nifa damuwa ta kici wani abu, tace bazan ci ba,
ni ka barni, ya koma bakin dayan gadon ya zauna. Ya
soma shan maltina tare da cewa. Na barki.
Har bayan isha’i tana kukan maganganun da Ismail
ya danqara mata, lokacin kuma likita yazo. Bayan
sun gaisa, ya tambayi jikin nata. Ismail yace, jikin da
sauqi, amma taqi taci komai. Likitan ya kalleta,
khadija! Ta dago ta dubeshi. Yace me zakici?
Cikin wata murya mai ban tausayi tace, ba komai.
Ismail ya ta6e baki, barta likita, cikinta ne zai fada
mata. Sai kuma maganar pampers, dazun wata nurse
ta ba yayata Shawarar mu sa mata pampers sbd
fitsari, tunda taqi a sa mata roba. Likitan ya kalleta, ki
bari mana a sa miki robar fitsari? Tace doctor bana
so. Ta sunkuyar da kai tana tuna zuwansu katsina, ita
da hajiya. Ta matsa wai sai an kai ziyara asibiti da gdn
marayu. Daddy baiso zuwa ba yace zai bada abinda
za’a kai, amma hajiya ta cije tace dashi za’aje. Aka tafi
harda ita, a wani asibiti ne taga marasa lfy an daura
musu ledar fitsari.
Ta tambaya menene wannan? Aka ce mata ledar
fitsari ce, saida tayi rashin lfy sanadin ganin marasa
lafiyan. Sannan ace za’a sa mata. Shikenan ka sai
mata pampers din, amma amma dai zaku sha kudi,
in kuma zaka dinga sata a toilet din da kanka, da sai
yafi muku. Da sauri mimi ta daga kai, Allah ya
tsareni, ko hannuna karka sake ta6a min. Ba mijinki
bane? Ko pampers din waye zaisa miki in ba shi ba?
Duk wahalar da yake miki, yana kashe kudi akanki
shine zaki dinga yi masa haka?

Mimi tasoma kuka,”Ni bana son yasake tabani,na
tsaneshi”. Kuma ai kudina ya dauka yakemin
magani.Ai bashida kudin dazai kashemin.
“Likita kar ka damu da ita,nima inayi mata ne don
Allah,da Lima tausayin halin da take ciki,amma
rashin mutunci halintane ko tayi min bazae dameni
back.Ita ikirarinta bata sona,nima kuma bnga abinso
a gurinta ba”.
Likitan yayi murmushi ,don ya fahimci Isma’il yana
maganar ne don son cusa haushi ga marar lafiyar.
Yace “khadija wae bakya son shi?” Tace “eh”. Saboda
me? Tanuna isma’il da yatsanta,”saboda abubuwa da
yawa. Ina zargin sa da shiga cikin rayuwata. Kuma ya
taemaka gurin shigata wannan halin.
Isma’il yazaro ido yana kallonta,a zuciarsa
yace”sharri zatayi min?” Likitan yaja kujera, yazauna
tare da tattara hankalinsa gareta. Sanar dani
hujjoinki,kila inada taemakon dazanyi miki. Tasoma
kula “Ranar wata asabar nasoma jin lavarinsa a
wurin kannaina. Sunaji dashi a matsayin malaminsu.
Ranar farko Dana dora idanuana a Kansa,ranar ya
raena min wayau,tare dafada min maganganu na
wulaqanci.
Abinda baa taba yi min ba a rayuwa ta. Sannan shi ne
mutum na farko da banyi nasarar rama abinda
yaemin ba, duk da cewa yayi min abin da baa taba
yimin ba. Sannan shine mutum na farko dana taba
kae qaran shi wurin daddyna bae amshi korafina ba.
Tundaga ranar asabar din daya dira gidanmu
Abuja,van qara samun kwanciar hankali ba.A qarshe
shine daddy ya daura min aure dashi a ranar asabar
kuma. Kalli wannan abin doctor,ta yaya zan
yafemasa wannan zunubin?
Salis yayi qoqarin danne dariyar da ke qoqarin kufce
masa,sannan cikin zolaya yacee “gaskia yayi babban
zunubi”. Ismail kam dariyarsa yayi harda
qwalla.sannan yace, “Mimi kenan ,kiyi haquri,don
nifa haka nake, duk inda nashiga sae nayi nasara
akan duk mae ja dani, saboda na dogara ga
Allah.kinsan duk Wanda ya mika lamuransa ga
Allah,to fa Allah ya Isar masa.kinci sa’a ma wannan
guntun labarin naki agaban likita kika fada,ba agaban
alqali ba, da sae ya daureki.Domin babu abinda ya
hada labarin nan da halin dakike ciki.ni na hanaki bin
umurnin mahaefinki? Ni nace miki ki gudu? To, in
baki sani ba kisani,bijirewa mahaifinki da kuma
gudun dakikayi kika bar iyayenki sune silar shigarki
wannan Hamlin. Likita have, wai-wai-wai kin gudu
ne dama? Ta sunkuyar da kai, hawaye ne kawai ke
zuba. Lallai kinyi babban laifi.
Ko dani ba alqali bane. Kamar yadda Ismael yace,
amma na yarda gudunki ne ya jawo miki wannan
Chapter 44 · 0% Book details