Sashe 16
Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya roke shi don ALLAH ya kaima zainabu wayarsa, don yana son su gaisa yaji muryarta,mahmud ya ce,shi fa ba ya son yaje ne a raina mishi wayo.lsmail yayi ta rokon shi,da kyar ya yarda,ya ce,zai je da yamma.suna gama waya ya mike ya debi takardu don zuwa cikin gida koyar da 'yar mulki,sunan da ya fi kiran ta kenan in zai yi maganar ta da hamisu direba. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (69)Ta fi minti talatin sannan ta fito,tunda ya ga hakan ya san yau akwai matsalar da ta fi ta kullum. ALKUR'ANI da ma yake karantawa tun kafin ta zo, ta kalli inda yake,ta ja tsaki ta zauna,ya kai aya sannan ya dube ta barka da shigowa fatan kina lafiya? ta zaro ido,ba ruwanka da lafiya ta,ko kai likita ne? bai ce komai ba,amma idanunsa suna kallon ta,ta ja tsaki tare da fadin aikin banza shishigi kawai.ya ce, ki na ji na ko?yau ba neman fada nike yi ba,don ALLAH ki tsaya mu yi karatun nan shine ya kawo ni garin nan,ni na roke ki kin ji?ta ce bazan yi ba,ya ce, to zan kira mahaifiyarki in fada mata gaskiyar komai, sannan ni kuma in tafi abina,na soma gajiya da zama haka.ta ce,zan so haka,na fi kowa son ka tafi don na tsani kallon fuskar ka,amma bai kamata in barka ka tafi haka nan ba,ya kamata ni ma in yi maka abinda ba zaka mance ba.kamar yanda kaine mutum na farko da ka soma cusa min bakin cikin da bazan manta da shi ba.ba a taba bata min rai ba tunda ni ke sai kai,ya yi shiru,don shi ya gaji da wannan wasan kwaikwayon,ya ce,to in na baki hakuri fa?ta ce,ka rike kar ka bani don bazan karba ba,ka barni in rama. ya ce,ba laifi,daga nan yayi banza da ita,sai kuma ya mike tare da kwasar littafansa,ta ce,na sallame ka ne?lokacin ka bai cika ba,ya ce,ba amfanin zaman,tunda ba karatun zaayi ba ya ta fi abinsa. yana zuwa dakin shi ya kira hajiya sauda da nufin ya fada mata komai,suna gaisuwa sai ta soma yi masa godiya har ya kasa fada mata,suka yi sallama, ya kwanta yana tunanin abin yi.haka suka yi ta yi har ranar lahadi,wacce ta kasance ranar da alhaji bishir zai amshi bakuncin sabon abokinsa,ministan man fetur.karfe takwas zai zo,amma tun shida an hana kowa sakat a gidan.girki an yi shi yafi kala goma,ban da nau'in kayan sha na kanti,ga busassu tun daga kan goro dabino,kayan marmari ma gasu na kala-kala.takwas zai iso gidan, don haja zuwa lokacin kowa na ta shiri.ya kira alhaji bishir ya ce,alhajin ALLAH zan zo fa da nawa iyalan ne. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (70)Alhaji bishir ya ce,na yi murna sosai,ina yi maku maraba. Ya fito daga dakinsa yana kiran nafisa,ta fito cikin sauri tana cewa,sun iso ne?ya ce,aa da iyalansa zai zo,ta ce,ALLAH ya kawo su lafiya.cikin azama ta shiga dakin na'ima ta same ta tana yin kwalliya, sai ta ce,yawwa na'ima ki yi gayu sosai,da iyalansa zai zo,inda namiji kiyi kokari ki ja raayin shi,ta haka ne za ki samu shiga gurin dadinku.zai so ki fiye da MIMI,na'ima ta ce,ya fada ne?mommy nafisa ta ce,aa ba ya fada bane,kin san yana son zama kut-da-kut shi da minista,in surukanta ta shiga tsakanin su yaya kike gani?na'ima cikin murna ta ce,zan yi kokari, amma in shi kanshi ne mommy ai yayi tsufa. ALLAH ya sa yana da yara maza mommy,nafisa ta ce,ina ruwanki da tsufansa?daura shi zaki yi a wuya?kudin muke bukata, ballantana a ce kin haihu,randa duk ba shi mu sha gado,ga gata gurin dadinku,na'ima ta ce,lnsha ALLAH za ta yi hakan. MIMI tana daki tana shirin ta,ita ba gwanar shafa abubuwa rakwacan ba ce,amma man ta da hodar ta zuwa turare tsadarsu ta isa.jambaki kurum ta shafa pink ta saka riga da wando damammu bakake a sama ta dora pink din shimin kayan ta zo mata gwiwa,ta tattare gashin kanta zuwa gefe ta kama shi da pink din ribom kasa-kasa,ta fesa turaranta na yau da kullum,don ta fi son turarukan arabia,takalmin ta flat baki mai ratsin pink. ta dauki wayarta daidai lokacin da wayar ta soma ringin,ta daga dad ya ce, uwata sauko sun iso,ta ce to daddy.lokacin da ta sauko falon kasan babu kowa,sun tafi tarbo bakin, bata bisu ba,sai ta samu kujera ta kame.suka shigo da sallama,ta tashi ta nufe su,matar minista ce suka shigo tare da mommy nafisa,sannan su alhaji bishir din,sai wani saurayi sannan na'ima da wata budurwa saar MIMI,sannan kananan suka shigo tare da su ahmad.kan kujerun fakon alhaji suka zauna,sun gaisa inda suka gabatar da junansu,ko in ce alhaji akilu ya gabatar da iyalansa.ya nuna uwar,ga madam dina hajiya bilkisu,sai yaro na na farko abbas. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (71)Ga shi nan ina ta fama ya yi aure yaki.ya gama karatunsa,yanzun yana aiki da central bank ne,alhaji bishir ya ce,ya kamata kam a yi aure.abba zai shekara talatin ko?alhaji akilu ya ce,talatin din ce kuwa,alhaji bishir ya ce,saan abba kenan dana na fari.shi kam yayi aure har sun yi min takwara, alhaji akilu ya ce,ka gani ko abinda ni ke buri kenan in ga 'ya'yan.alhaji bishir ya ce,ka kokarta ka ji dana? abba cikin murumushi ya ce,lnsha ALLAHU. ya nuna ta mace,waccen kuma aisha ce tana shekarar ta ta farko a jami'a ta kasar ghana,sai samira da azima da jamil duk 'yan primary ne da j.s.s. alhaji bishir ya ce,masha ALLAH,ALLAH yayi masu albarka.kai ba su da yawa ni yara na ishirin da biyu, mata na uku,alhaji akilu yayi 'yar dariya,ku manya ne, amma hakan yayi kyau, dama ka yi kokari ka cike, suka dariya,alhaji bishir ya ce,mu yi tare,kai ta biyu sai a yi rana daya.suka kalli matan wadanda suma dariyar suke har suna hada baki gurin fadin ku yi ta yi mana,ga dai yaranku nan,sun girma.bayan sun gama gabatar da iyalansu sun dan yi wasa da dariya, sai kuma mommy nafisa ta ce,ya kamata mu je dining, nan fa aka hau kan teburin cin abincin. MIMI ta kalli na'ima cikin maganar nan ta ta a hankali ta ce,ki lura tun daga kan aisha zuwa kasa ni zan ji da su daddies, mommies da brother abbas.yanda tayi maganar, iyayen suka sa dariya,haka ta yi ta zuba masu sai da kowa ya ce,yayi,ita ma na'ima ta kula da na ta gefen.bayan an kammala aka koma kan kujeru, MIMI da ba son hayaniya take yi ba,sai ta kama hannun aisha zo mu je sama na.haka yayi wa mommy nafisa dadi,har ma ta dauki wayarta ta tura ma na'ima messege,inda ta ce,ga dama nan ta samu,ki lura da abbas kuma ki ja hankalinsa.a sama,aisha sai santin falon MIMI take yi, MIMI ta kai ta ko'ina a saman ta,ta ce,gaskiya MIMI kin ji dadi,ke kam 'yar gata ce,duk nan ke daya?a ina ki ke karatu?MIMI ta ce,dubai,ai in fada maki aisha dad yana ji da ni fiye da zaton ki,duk abinda ni ke son. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (72)A sama,aisha sai santin falon MIMI ta kai ta ko'ina a saman ta,ta ce, gaskiya MIMI kin ji dadi,ke kam 'yar gata ce,duk nan ke daya?a ina kike karatu? MIMI ta ce,dubai,ai in fada maki aisha dad yana ji dani fiye da zaton ki,duk abinda ni ke so yana yi min.can kasa kuwa mommy nafisa ta ja hajiya bilkisu zuwa dakinta,alhazan su ma tasu hirar suke yi,kananan kuma sun bar falon alhajin sun nufi na su,suna gaban damfareriyar talabijin din falon suna buga game, Na'ima ta koma kusa da abbas wanda ke ta latsa wayar shi ta ce bros ya kokari,ya kalle ta, alhamdulillah,ya makaranta? ta ce,ai yanzu ina gida ne ban fara zuwa makaranta ba,ina son in je wajen ni ma,amma dadinmu ya ce, ko abuja ba zan bari ba.ya ce,kila kina rawar kai ne,ta ce,aa raayinsa ne haka,sai kuma ta canza maganar da cewa in ga phone din ka bros,ya mika mata ga shi. ta yi ta shiga nan fita nan ta dinga kallon hotunan shi lokacin yana karatu a waje, ya birge ta sosai.ta ce,ka hade fa bros,ya ce,na gode,ta saka lambar wayarta ta ce.ga lamba ta nan,in maka saving din ta, ya ce,eh,ta ce,kana da me irin suna na?ya ce,aa ta saka sunan,ta yi saving din ta shi.kamar daga sama sai taji ya ce,sa min ta sister din ki,mene ne sunanta na gaskiya?ta ce,khadija,ya ce,ok sa min lambarta,da ta tashi,sai ta canza lamba daya ta mi shi saving ta ce,in kun tafi sai yaushe?ya ce,ku ya kamata ku kawo mana ziyara ai,ta ce,haka ne,za mu zo,muryar alhaji akilu bala ta katse su. Goma tayi ku tashi mu tafi,alhaji bishir ya ce,tun yanzu?to sai mun zo muma, alhaji akilu ya ce,abinda zance kenan muna jiran zuwan ku,amma da rana za ku zo mana ko?alhaji bishir ya ce,in ka samu lokaci ka sanar da ni sai muzo,ya kalli na'ima,je gurin mominku ki ce su fito, alhaji akilu ya ce,ka san mata da kus-kus.sun fito inda mommy nafisa ta cika hajiya bilkisu da kayan mata,alhaji bishir ya cika yaran da kudi,na'ima kuwa abbas tayi wa kyautar turaruka masu kamshi,ita kuma MIMI kawarta aisha ta yi ma kyautar irin kaya jikinta. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (73)Da takalmi da kuma turare,sannan suka yi canjen number,alhaji bishir ne ya kira MIMI ya ce,su sauko,abbas ya kosa ya sake ganin MIMI don komai na ta yayi masa,kuma ita ce yake ganin zai zaba ta zama matarsa,tunda suka fito yake sake kallonta zuciyarsa tana kara kuranta ta.sun raka su har bakin mota katuwa jeep, direba yana ciki yana jiransu,aisha ta rungume MIMI sis sai naji ki,MIMI ta ce,yawwa sis aisha sai kin ji ni. Tunda suka koma gida, abbas ke kiran layin da na'ima ta sa mi shi na MIMI, wani ke dagawa,duk ya damu sai kai kawo yake yi a gefen nasa,ji yake yi tamkar ya nufi gidan su MIMI ya fada mata ya na sonta. a gidan alhaji bishir kuwa bayan sun yi bankwana da juna kowa ya shiga makwancinsa, dad da momi sun shiga nasu makwancin,sai take ce masa,alhaji na ga kamar na'ima da abbas sun aminta da juna,ya ajiye rigarsa da ya dauka da niyyar sawa ta bacci ya ce,haba!!ta ce,(cikin dariya) da gaske kuwa,har canjin number ta ce min sunyi.ya kamo hannunta