Sashe 29
Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hawaye.na'ima ta kai yar albarka.allah ya bata zama lafiya a gidana,ke kuma sai ki zauna mu gani,wanda kika bijire mawa din kika watsa masa kasa a ido,kika so ki kunyata shi zai ci gaba da jiyar dake dadi,gami da nuna miki kauna kamar da. Daidai lokacin alhaji ya shigo yana cewa,ba ta da mazauni a gidana.ta zo ta fita ta ko inda ta fito.na sallamawa duniya ita!hajiya binta ta ce,haba alhaji wannan ma ai ba mai yiwuwa ba ne.ka yi mata afuwa,ta yi kuskure.alhaji ya isa gabanta,ke khadija!na ce ki zo ki bar gidana!sunan uwata kika ci,ni uwata ta dade da mutuwa.don haka yadda kika yi min abin da ba zan manta ba.haka nan ke ma zan yi miki abin da ba za ki manta ba.MIMI ta mike ta zo gabansa tana kuka a tsugune,dad don allah ka yafe min.wallahi dad na yarda na dawo,zan auri duk wanda kake so.dad ya ce,me abbas zai yi da ke a halin yanzun?kin je kin kwana da wani ki zo ki ce kin yarda!cikin tashin hankali MIMI ta ce,wallahi ban kwana da wani ba.na rantse maka dad! hajiya sauda duk dauriyarta ba ta san lokacin da ta soma zubar da hawaye ba.su usaina suka je jikinta suna bata hakuri. abba ya ce,daddy to kawai ka daura mata aure da shi wanda ta bi din mana.dad ya sake daga murya,har abada wallahi!ba zata aure shi ba.yadda bata yi min abin da nake so ba,ita ma har abada ba zan taba yi mata wanda take so ba. momy nafisa ta shigo tana kuka,tana ba alhaji hakuri. ya ce,na yi rantsuwa,yau dole yarinyar nan ta bar gidana,ko da ita kadai na haifa.yarana ashiri da biyu. don na rasa ita kadai bana jin cewa nayi asara. Hajiya binta ta ce shi ke nan za mu wuce da ita gidana can malumfashi.ya ce,gidanki ko gidana?can ma gidana ne,don haka ba ta ba shi.ta gama cin arzikina,don ko gidan mahaifiyarta na yi mata tsakani da shi.abba ya lumshe ido,yana tunanin dad ya tsaurara da yawa.don haka ya ce, [01/10 10:34 pm] Abdul: (31)Dad shi ke nan bari mu wuce da ita,in tafi da ita gidana.alhaji bishir ya girgiza kai,ban lamunta ba.ln kuma ka yi hakan ba zan yafe maka ba.ka sa min idanu kaga irin hukucin da zan yi mata.hajiya binta ta ce,don allah alhaji ni dai kar ka ce zaka kore ta a gidanka,ka ji?momy nafisa ta shigo cikin kuka tana cewa,don allah alhaji kayi hakuri,ka yafe mata,tunda na'ima ta riga ta auri abbas din sai a bar zancen.MIMI ta zo tayi shirin komawa makaranta.cikin zafin rai,ya waiwayo,wace makarantar?nafisa za ki sa in tafka miki ashariya!ya nuna MIMI,wannan yarinya don ubanta ta gama boko a gidana,ta je tayi zaman aure.yau din nan zan aurar da ita ko ma ga uban wane ne.bana son kowa ya ce,min uffan.a kalle ni da hukuncin da zan yanke duk inda na bada ta da sunan aure.na gindaya allah ya isa ga duk wani ahalina da ya je,ko na sani ko ban sani ba.sai lokacin hajiya sauda ta daga ido ta kalle shi,duk da halin MIMI,amma da da mahaifi sai allah.ta ce,alhaji kana ganim wannan hukuncin bai yi tsauri ba?a fusace ya kalle ta,bana bukatar ki sa bakinki a cikin lamari,kamar yadda tun farko kika ce ba ruwanki ke yar shawara ce.to don allah ina son shawarar ma ki bar ta.kina da kima sosai a idona bana son mu fara abin da bamu yi a da ba.za ta yi magana.abdulkarim yayi mata alama da hannu wai ta yi shiru.don haka sai ta kulle bakinta.shi kuma alhajin ya fita yana fadin zata gane ba ta da wayo. Hajiya sauda ta kalli MIMI maganinki ke nan!hajiya binta ta ce,ni fa ina zargin cewa MIMI shigo-shigo ba zurfi aka yi mata. momy nafisa ta ce,me kike nufi?ke nan ni na sata bijirewa mahaifinta?hajiya binta ta ce,komai zai iya faruwa.yaran da suka tashi a karkashin tarbiyyarki me zai sa na'ima ta lankwasu, amma MIMI ta kasa lankwasuwa?hajiya sauda ta ce,ku bar zance nan.laifi dai duk na MIMI ne.ban ji haushin alhaji ba,duk hukuncin da ya yanke mata.da ta tsaya a kan bata so,sai ya fi mata a kan gudun da tayi.wa ya san abin da ya faru a gudun da ta yi?MIMI ta ce,hajiya ku yarda da abin da zan ce [01/10 10:34 pm] Abdul: (32)Na rantse muku babu wani abu da ya faru da ni.ni kadai na kwana a dakin da na sauka.abba ya ce,kin dai cuci kanki da kika sa kafa kika bar gidan mahaifinki,kika bi wani kato. kuma duk sunan da aka kira ki da shi dole ki amsa. abdulkarim ya ce.alhakinmu ne yasa ta yi wa alhajin haka.don haka ni duk mai zai mata ba zan ji haushi ba.usaina bata ce,yaya ni kuma a nawa ganin tunda wannan ne karo na farko da sis MIMI ta soma saba masa da ya yafe mata,sai in ta kara.momy nafisa ta ce,yawwa usaina,abin da ni ma nake so ke nan. shi kuwa alhaji ya fita ne da niyyar ba ta duk wanda ya ci karo da shi.babu abin da ta fi tsana a duniya kamar talaka,don haka za ta dandana rayuwar talauci.har zai fita gate,sai idanunsa suka hango lsmail yana alawala,tamkar an tsai da shi ne,ya tsaya cak, yana kallon lsmail.sai ya tuna ta taba furta masa cewa ta tsani lsmail. murmushin takaici ya yi,ya ce,malam lsmail yana kan wanke kafafu,ya dago da azama ya karasa,ya mike cikin girmamawa yake cewa,alhaji barka da arziki.na ga MIMI ta dawo.alhaji yayi yake,tare da cewa,barka ka dai.wato malam lsmail kamar kai ne kake fada min an aurawa budurwarka wani ko?lsmail sam baya ko son tuna lamarin don haka sai ya ce,ni ne alhaji,amma na dangana.haka allah ya hukunta.alhaji ya ce,wane ne wakilinka wanda zai amsar maka aure?gaban lsmail ya fadi,cikin in-ina ya ce,alhaji ban gane ba.ka ce mene ne?ya ce,kar ka damu,in mu i sallar laasar ka samu ko baba maigadi ne ka wakita shi ya amsar maka aure.kar ka ji mamaki hausawa suna cewa wani hani ga allah baiwa ne.sai kawai alhaji ya wuce ya bar lsmail tsaye,zuciyarsa cike da tambayoyi,amma bai san wa zai amsa su ba. Maigadi da hamisu suka nufo lsmail suna cewa, malam lokaci fa,baka yi kiran salla ba.maigadi ya ce,kodayake alhaji ne ya tsai da shi ko?lsmail ya ce,ku ji alhaji wai in samu wanda zan wakilta ya amsar min aure,wai ko kai. su ma suka cika da mamaki.hamisu ya ce,ko cikin yan aikin gidan ne tunda ya san kayi rashin budurwarka? [01/10 10:34 pm] Abdul: (33)Isma'il ya ce,ni don na riga nayi fushi da soyayya, don ma kar in ce na daina yin ta ne,a ce na dauka da zafi.hamisu ya ce,tunda ya zabe ka zai yi maka alkhairi kar ka ce aa,ka yi shiru.lsmail ya ce,ba zan iya musu da shi ba,dana yi tun tuni.ku taya ni adduar allah yasa in ci jarabawar don ina cikin gwaji.suka ce,amin allah ya sa ka ci. bayan sun idar da salla,alhaji ma ba a nan yayi sallar ba.kamar minti goma,sai ga alhaji da abokansa hudu da kuma kaninsa kawu shafiu wanda daki lsmail yake kwana tunda suka zo bikin.nan alhaji ya ciro naira dubu talatin,ya mika wa maigadi.sadakin malam lsmail ne.ga wanda zai ba da auren nan,ya nuna kaninsa cikin masallaci suka koma,inda aka daura auren KHADIJA DA ISMA'iI duk ba su yi saurin dago wace ce khadija ba,saboda sunan MIMI ya boye.sun fito suna tambayar juna,alhaji kuma da kaninsa suka shiga gida. daki lsmail ya shiga yana kai-komo a fili ya ce,kaddara ta kawo ni abuja.ya dauko wayarsa yana ta zufa,ya kira mahmud ya sanar da shi komai.cikin murna ya ce, allah ya sanya alherh.lsmail ya ce,ba na son wulakanci jaje ya kamata ka yi min ba murna ba.mahmud ya ce bari in sanar da malam, in kuma je gida yaya amina in fada mata.lsmail ya ce,ni damuwata ko daki ban kama haya ba ban san ma yaya zan yi ba.amma komai ake ciki zamu yi waya.alhaji kam da ya shiga ciki,shi da dan uwansa kai tsaye suka wuce saman MIMI,inda su hajiya sauda suke.alhaji ya ce,mika wa binta sadakin, duk suka zura ido,hajiya sauda salla take yi,amma sai da ta ji kamar ta fadi.momy nafisa da ke biye da su alhajin don tana falon kasa da baki suka shigo,ta ce,wane ne mijin alhaji?ya ce,zai shigo ai lna take MIMI?hasana ta ce,ta shiga cikin tana wanka.ya ce,to in ta gama ku fada mata ta shirya maza-maza alhajin ya sake sauka ya bar su nan cirko-cirko shi ma dan uwan ya basu kudin,ya fice. [01/10 10:34 pm] Abdul: (34)MIMI tana fitowa wanka,hasana tana shiga dakin ta ce,in ji dad ya ce ki shirya.MIMI ta zaro idanu, zuwa ina?hasana dai ta ce,haka dai ya ce,amma ban sani ba.riga doguwa ta zura ta zauna bakin gado tare da yin tagumi.hajiya sauda ta idar da salla ta zabga tagumi,tana hawaye,lalle alhaji.jim kadan ya sake hawowa, wai ina su abba ne?usaina ce ta iya cewa,sun tafi tun dazun.sun ce za su je suyi salla su wuce.ya sake sauka ya fita.hamisu ya samu a bakin gate,ya ce, malam hamisu ga shi ka je ka cika tankin motarka.don allah ka zo ka kai amaryar katsina.lna shi lsmail din yake ne?hamisu ya ce,yana dakinsa.ya ce,to ka je ka ce masa na ce ya shirya kayansa,ya zo ina nemansa.yan kayansa da ma basu da yawa,ya tattara su,ya zuba a jaka,ya fito ya tsaya a wajen su maigadi,shi kuma hamisu ya tafi siyan mai. Alhaji ya sake fitowa ya yafito lsma'il da hannu. lsmail ya nufi alhaji cikin faduwar gaba yana cewa,kaddara da ta same ni,allah ka duba min.ya isa gurin alhajin.ya ce,biyo ni. suka ratsa falon.har yanzu da mutane,amma sun ragu ba kamar dazun ba. matakala alhaji ya soma takawa,shi ma ya bi shi.ya waiwayo ya yi masa alama da kai. suna shiga alhaji ya kalli usaina, kira min MIMI.hajiya binta ta ce,alhaji wai me kake nufi ne?momy nafisa ta ce,kana nufin wannan ne mijin? usaina ta shiga ta same su da hasana ta ce,sis MIMI dad yana kira.da sauri ta mike,kanta babu dan kwali,ta fito a firgice.duk zatonta zai ce ta koma gidan mamanta ko gidan hajiya binta.tana fito ta kalle shi,ga ni dad.ya ce,ki shirya ga mijinki nan za ku