← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 89

Sashe 53

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

banyi muku qorafin cikina da kuka zubar ba, to ku
bani matata kawai mu tafi. Inna tace, au tanan ka
biyo? To ai inason ka sani, tuni muka samu labarin
baka son haihuwa, bare kayi wata barazanar banza.
Ba zata koma ko ina ba, sai ka canke kudin mutane.
Yace, haka kk ce? To kuwa ku shirya cin wani bashin
don zaku amsa sammaci, kotu zamu shiga.
Ya ciro wayarsa, iroro dake gefe yace, Alhaji ai sai ka
kira lauyannan naka tukun, domin duk wanda baisan
mutunci ba, gara ayi masa abinda yafi sani. Wato
rashin mutuncin ba. Inna tace, ku kira alqali, ba
lauya ba. Kai kuma dan kanzagi makwadaici kabi a
sannu. Kaje ka nemi sana’a ba maula ba. Iroro yace,
ai indai wannan ne sunanmu daya dake, wato ‘yan
maula. Kwadayinki kuwa ya ninka nawa. Tunda kk
miqa ‘yarki ga wanda bashi ta za6a ba. Alhaji yace, ko
ba haka bama Iroro, ai baka kaita roqo ba, kullum
dan aike yana hanya. Tace, kodai me zaku fada, ku
fada.
Lokacin ne layin ya shiga wanda yake nema. Alhaji
yace, yauwa Barista audu kaji ko? Daga can suka ji
murya tace, eh ina jinka Alhaji lawal. Iroro yace,
Yauwa Alhaji ai gara kasashi a speaker taji. Alhaji
game da zancen da mukayi ne na matata. Ynxun
haka ina gidan uwarta ta hanani matata, don haka
zanzo mu shigar da qara. Daga can sukaji muryar
barista yace, qarar kisan kai zamu shigar, tunda basu
da mutunci. Ina ga ko dan gidan da suka mallaka, sai
sun daida ba tare da kuma sun kare kansu ba. Don
haka kar ka damu. Alhaji yace, shikenan nagode. Ya
kalli inna yayi murmushin mugunta, sai mun hadu a
kotu. Iroro ya sheqe da dariya. Dana sani tanata
bibiyarki. Har sun juya tace, Alhaji ya tsaya. Sannan
ya waiwayo.
Lafiya? Tace, bari in turo ta ku tafi. Kudin mutane
dana aro kuma idan nayi maka Allah ya isa fa? Tare
suka sheqe da dariya, Iroro da Alhaji. Iroro yace,
shegiya wuya! Alhaji yace, inna ai dama Allah
ishasshe ne. Cikin jin haushi, inna tace, ni ba innarka
bace don na tabbata ni kaina ka girmeni. Ta juya
cikin takaici, suna tayi mata dariya. Zainabu tana
kuka, tana komai, ta fito tabi Alhaji, tabar innarta
cikin takaici. Wani qarin abin haushi a lokacin suna
isa gida, saida yayi buqatarsa ya fita, ya barta tana
kuka.
Kishiyoyin suka shigo sunayi mata sannu tare da bata
haqurin rashin zuwansu. Ko kawo mata abinci sunce
Alhaji ne ya hana. Haka Zainabu taci gaba da
Rayuwar gidan Alhaji mai cike da matsi da takura,
gami da wahala, duk ta qara kodewa, ta fige ta lalace.
Kuma ya hana innarta zuwa, kamar yadda itama
yace ta daina zuwa gidansu. Innar Zainabu tasha

kuka tare da takaici da kuma da na sanin hada
Zainabu da Alhaji lawal.
Alhaji bashir ya dauki wayarsa ya soma neman layin
Abba. A ringing na biyu Abba ya dauka, ya kara a
kunne yana fadin dad ina kwana? Bayan sun gaisa
Alhajin yace, inason kazo yau ka tafi dani katsina.
Abba yace, amma lfy dai ko dad? Alhaji yace, lfy lau,
inason ganin mahaifiyarku ne, gashi har ynxun bana
jin dadin jikina. Abba yace, shikenan daddy, sai nazo.
Qarfe biyu Abba ya sauka garin Abuja. Tuni daddy ya
turo direba yana jiransa. Suka nufi maitama. Momy
Nafisa batasan da batun ba, saidai taga Abba. Ya
gaisheta tare da tambayar jikin daddyn, tace da
sauqi. Lokacin data shiga don sanarda Alhajin zuwan
Abba, sai yace ta hada masa wasu kayansa na ciki da
kuma wasu takardunsa. Tace, ina zaka Alhaji? Yace
katsina, nine nace wa Abba yazo ya tafi dani. Tace, ba
zaka bari kadan qara samun sauqi ba? Yace, karki
damu, can ma zanci gaba da ganin likita.
Shida daidai suka sauka a filin jirgin sama. Sun samu
direba na jiransu, domin kafin su taso daga Abuja,
Alhaji yasa Abba ya kira direban hajiya sauda,
batasan da zuwan Alhajin ba tana zaune a falo tana
ba Zainab magani, don yau kwananta uku babu lfy,
kullum suna hanyar asibiti. Sai kurum taji Sallamar
su. Bata zaci Alhaji bane, don muryar Abba irin ta
Alhajin ce. Saida taji yaran suna Oyoyo daddy. Da
sauri dago tace, sannu da zuwa Alhaji. Ta miqe cikin
sauri bayan ta kwantar da Zainab, tace, Alhaji baka
sanar dani cewa kana tafe ba. Yace karki damu tu
tunda mun iso lfy. Sun gaisa da Abba sannan ya nufi
gidansa.
Hajiya kuwa ta dauki jakarsa kuma ya bita zuwa daki.
Sannan ta dawo kusa dashi. Ya kamata kayi wanka
ko? Ya kalleta, zan yi wankannan kuwa? Barci nakeji
kuma inajin sanyi, sai inga kamar in nayi wankannan
zazza6i zai iya rufeni. Ta cire masa riga, sai singileti.
Ya kwanta akan gado, ta zauna bakin gadon. Kasha
magungunan ka kuwa? Yace, nasha, sai dai akwai na
ynxun qarfe shida, amma sai zan kwanta sannan zan
sha. Tace, a’a nidai kasha ynxun, yana da kyau kabi
dokar likita.
Ynxun tashi zakayi in taimaka maka kayi wanka,
kasha magani kayi sallah don kaga magriba ta kusa.
Ya tsura mata ido, “sauda nayi miki laifi ko? Ta kama
hannunsa, ni baka min laifi ba, to muje kayi? Yace, to
sauda muje. Kafin yayi sallah har ta shiga kicin da
kanta tayi masa tuwon alkama miyar alayyaho. Yana
zaune kan sallayarsa yana istigfari. Can qasan
zuciyarsa kuwa tunanin mimi takeyi.
Zuwa ynxun ya gama tabbatar ma kansa cewa, son
da yake wa mimi ya zarta tunaninsa, kuma ba zai

ta6a son wani cikin ‘ya’yansa kamarta ba. Amma dole
ya jure sbd ya samu ya ida nufinsa don ta samu
canjin rayuwa. Wasu hawaye suka soma zubo masa.
Sam baiji Sallamar Hajiya sauda ba, har saida ta dafa
shi, sannan ta tsugunna tare da aje abincin dake
hannunta dayan. Duk da saurin da yayi ya share
hawayen sa, saida tace “na shiga ukuna! Alhaji kukan
me kkyi? Cikin sarqaqqiyar murya yace, ba kuka
nake ba. Sauda ta zauna dirshan akan sallayar, cikin
tashin hankali tace, haba Alhaji. Shekarunmu nawa
ban ta6a ganin hawayen ka ba sai yau.
Dole akwai wani babban al’amari. Ta kama
hannunsa. “Na roqeka karka 6oyemin komai.
Idanunta suka cika da hawaye yadan matsa
hannunta, “sauda karki tada hankalinki ba wani abu
bane. Sannan inason don Allah ki yafe min nasan
cewa, na sa6a miki da yawa. “qara firgita tayi, gani
takeyi tamkar Alhajin mutuwa zaiyi ya barta. Sai ta
soma kuka. Jikinsa ya janyo ta.
Haba sauda, mene ne na kuka kuma? Tace Alhaji don
Allah karka tafi ka barni. In kuma wata matsala ce
tasa zubar hawayen, don Allah ka fadamin. Yace,
sauda bazan 6oye miki ba, ina kuka ne sbd mimi.
Saida na rabu da mimi nasan cewa, inayi mata
mugun son da bansan adadinsa ba. Tunanin ta ne ya
hana sugar na sauka, na sani. Ya dago fuskarta mai
dauke da mamaki. Ta kalleshi cikin ido, “sbd mimi kk
cikin wannan tashin hankali? Yace, eh sauda. Tace to
me zai hana ka tashi muje gurinta ynxun a asibiti?
Yace, lokaci baiyi ba.
Sauda ynxun zan sanar dake dalilina na aura wa
mimi talaka. In kince ban kyauta ba, to zanje gurinta
ynxun, in kuma raba auren ta, sannan in fita da ita
wajen qasarnan don nema mata lfy. Hajiya sauda
tace, kafin nan bari in baka abinci da kuma magani.
Tunda munyi sallar isha’i, sai inje in sallami yara na
inzo in saurareka har zuwa asubahi. Yayi guntun
murmushi. Ta janyo tiren, ta zuba tuwon a cikin
plate, tasa a gabansa. “in baka a baki?” yadan
karkatar da kai, “bana tuna shekaru na matsawar ina
gabanki. Ki bani zanci da hannayenki masu albarka.
Ta soma bashi tuwon, bayan yayi bissimillah. Bai iya
tuna lokacin da yaci abinci kamar na yau ba sam.
Tana bashi tana masa hira har yayi qat. Ta bashi
magani, sannan ta jashi da wata hirar, tunda ta gano
maganar Mimi ce damuwarsa.
Batun ‘yan uwanta ta dauko masa na auren ‘ya’yan
sa’ade ‘yar uwarta, da irin gudummuwar da ta basu.
Yace, nima zan bada tawa. Kullum inason in nazo
inje in gaida ya Dikko sai abubuwa susha min kai.
“sauda tace, har na gaji dayi mata qaryar cewa, kana
gaida ta. Kwanaki tazo tayi sati hudu. Har yaya jabiru
Chapter 53 · 0% Book details