← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 89

Sashe 11

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba zanyi sallamar ba,ba zan rufe jikin ba.ln baka sani ba,barin in fada maka,na sa a kawo ka nan gidan ne saboda in tozarta ka,in nuna maka kai kaskantacce ne.ya ce,don na miki wane laifi?ta ce,kai ne mutum na farko dana taba yin sa-in-sa da shi.wanda ya taba kallon cikin ido na ya fada min magana,kuma ina son ka zama na karshe,wannan shine laifin ka.lsmail ya ce, yanzu dai za ki yi karatun ko a'a?ta ce,na ce ba zanyi ba,ya mike tare da kwashe takardunsa.ta ce,ban sallame ka ba,yayi tafiyarsa ya bar ta zaune. MIMI ta bi shi da kallo cikin mamaki,shi wannan dame yake takama,har da baya jin shakka ta,kamar yadda sauran jamaa suke ji?ya san wace ce ni kuwa?ya san wane ne ubana? Ba wani ba ne uban MIMI fa ce alhaji bashir,dan asalin masari ne,karamar hukumar kafur jihar katsina. mahaifiyarsa 'yar dabai ce,su shabiyu ta haifa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (43)Amma yanzu saura su biyar,bakwai sun rasu,mahaifiyarsu ta rasu lokacin ya kammala sakandire,yayyin shi. mata uku ne,sai namiji daya dake bin shi,rakiya da basira a malumfashi suke aure, saratu kuma tana cikin kafur,malam aliyu mahaifinsu ya sake yin aure. inda matar ta kasance mai son kanta game da son zuciyarta.wannan yasa ya bar masari,ya soma shiga cikin garin katsina don neman abin kanshi, maimakon noma da suke taya mahaifinsu,shi da shafi'u kaninsa. ya yi sana'o'i kala-kala, tun daga kan kwandastan mota har zuwa dako,daga bisani ya soma bin wasu abokansa guda biyu da suka kama shago daya su uku,da lsa mani da kabiru naalla suna harkan dabbobi. tun yana karba yana saidawa ya cire ribarsa,har ya zo ya samu jarin kansa. sannu a hankali suka yi zangonsu na dabbobi, lokaci bayan lokaci yana zuwa masari ziyartar danginsa da mahaifinsa kuma yana yi masu alheri. kaninsa shafiu har yayi aure matarsa ta haihu,don haka mahaifinsa da yayyansa kullun burinsu yayi aure.wani zuwa da yayi har mahaifinsa yana cewa,ga 'ya'yan 'yan'uwansa ya zo ya auri daya daga cikinsu,sai bishir din ya ce,yayi hakuri,shi ba ya shaawar auren zumunta,amma duk lokacin da ya ga wanda ta yi masa,to zai yi aure,amma a yanzu neman kudinsa ya sa a gaba. ranar wata jumaa lsa mani ya tare shi yana sauri za shi masallaci ya ce masa,bashir ga wadansu shanu can zaa saida su a rugar fulani nan mashi.bashir ya ce,har mashi?gaskiya da kyar zan je,lsa mani ya ce,za ka samu alheri mutumi na,don jiya na dawo tafiya,ka sani da na saye su,amma ka daure mu je in ka dawo masallaci.hardon gar ne ke son zuwa aikin hajji,shine zai cikon kudi.bashir ya ce,ni dai masallaci na nufa ga shi ina jinjina zuwa mashin nan,lsa ya ce,mu je dai masallacin nan tare ma kawai,da zanje na karfe biyu ne,in ya so daga can sai mu wuce.a masallaci suka hadu da kabiru na'allah,inda suka nufi mashi dukkan su. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (44)Sun je rugar fulani,inda suka shiga garke shanu don duba shanu.ya nuna masu,aka shiga ciniki, an daidaita kuma bashir yayi alwashin kawo kudi gobe,saboda kudi suna banki.suna cikin sallama ne idon bashir suka kai kan wasu 'yan kwailoli guda biyu,sun dawo daga tallar nono,dayar ya kure da ido, 'yar similmila ta yi masa kyau,sai da ta bace ma idanunsa,ya bar kallonta.har lsa mani ya gane,bayan sun bar gurin ya ce,bashir kana ta kallon 'yar mutane saboda me?kar dai ka ce min son wata kake yi daga cikinsu?bashir ya ce laifi ne yin hakan?lsa ya ce,aa ban ce ba,sai dai ka bani dariya kawai,duk 'yan matan da ke cikin garin katsina? ka rasa wanda za ka zaba sai wadanan 'yan ruga mitsi-mitsi da su?kabiru na'allah ya ce,in dai fulanin nan nema,ba su son baiwa bare 'ya'yaansu.bashir ya ce,ku yi min addua in rabo na ce za su bani,don gaskiya na ga wacce nake so.suka sa mishi dariya. Abin ya wuce da tunanin bashir,domin ranar da tunanin 'yar fulani ya kwana,ya kosa ya je su kai kudin shanu,don haka tun tara ya shirya ya nufi banki ya ciro kudi,daga nan suka nufi mashi. ko da suka isa burinsa ya ga yarinyar da ta hana rayuwarsa sakat, har suka bayar da kudin shanun suna kokarin zuba su a mota,amma bai ga giccin wani da ba.ya kama mota zai hau sai ya hango ta tana kada nono cikin dan kuttunsu da suke cire mai,da sauri ya fasa shiga motar ya nufi gurinta. sallama yayi mata ta dago a firgice ta ji abin kamar daga sama,ganin mutum sai ta amsa cikin dariya. ya ce,'yan mata ya ya sunanki? ta kalle shi ta ce, suna na?ta kau da kai,ta ci gaba da abinda ta keyi.lsa ya kwada masa kira daga nesa,bashir ka zo mu tafi mana,bashir gani ya ke idan fa ya tafi ya bar damarsa,ya ma rasa ta kenan,shi damuwa.don haka da ya ga abinda zai dame shi,nan da nan zai yi maganin abin,in har zai iya, musamman in na kudi ne, tunda yanzu ba laifi yana samu. sake komawa yayi ya sa aka yi masa sallama da ardo,wanda ya tafi don ya adana kudinsa.kabir yazo gurinsa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (45)Zo mu je in ya so mu sake dawo wa,bashir ya ce,ba a haka da ni,ka san ni in ina son abu,zan yi duk abinda zan iya in kuna sauri kuyi gaba zan zo.kabiru ya gane fusata ta sa bashir fadin haka,sai yayi dariya,ya yafito lsa mani da hannu, suka zosu ukun suna jiran fitowar ardo. ya ce,da muna daki daya da ku,duk ku kayi aure ku ka barni,dole ku yi min dariya.duk yadda suka dauki lamarin da zafi gurin ardo,maana ba sauki sai suka ga akasin haka.ardo yana da ilimin addini,ya fahimce su,kuma yayi masu bayanin cewa lallai sun yi dace,domin har an bayar da ita,sai wanda aka baiwa din ALLAH yayi masa rasuwa wata biyu kenan. ya kara da cewa,in yana son ta ta amince ya nemi soyayyarta,in ta amince gurin shi babu wata matsala.kwana biyu tsakani bashir ya sake yi wa rugar fulanin tsinke,cikin ado aljihu dam da kudi.lsa mani yasa shi yin tsarabar sarka da 'yan kunne,wai mutanan ruga suna son abin ado mai kyalkyali.bai samu ardo a gida ba sai babban dansa jabiru.sun gaisa inda yayi masa bayanin cewa,ardo ya je cikin gari maganar tafiyarsa aikin hajji.sai dai yayi wa jabiru alheri,ya ce, masa yana son ganin bengel,kamar yadda ya ji ardo ya ambata rannan. sai jabiru ya ce,oh!sauda? ai saudatu sunanta,ardo kadai ke fada mata bengel, na gode bari in turo ta,domin yanzu zasu fita tallar nono.yana tsugune sauda ta isko shi,tana sanye da koriyar atamfa da kuma farin mayafi mai kyalli.duk da fuskarta babu walwala farin ciki gurin bashir ba ya misaltuwa.ta tsuguna can nesa da shi,ta gaishe shi,ba tare da wata kwana-kwana ba ya ce, saudatu kina so na?rufe fuska ta yi da gefen mayafinta ta ce,ardo ba za ya bada ni ga wanda ba bafulatani ba.ta yi magana cikin hausar da bata goge ba.ya ce,kar ki damu ardo ya san da zuwa na,ya amince in nemi soyayarki. saudatu yarinya ce ba za ta wuce sha uku-sha hudu ba,sai kyau tamkar balarabiya.ta ce,in na amince me zai faru?ya ce, aure ne zai faru,ya fada cikin kwaikwayon muryarta, ya lura akwai kuruciya, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (46)Gurin yarinyar.ta ce,kamar ya ya?yanzu da na amince sai a kama aure? ya yi dariya,to me za a jira?zan turo iyaye na su gana da naki,zan bayar da sadaki da duk abinda kuke yi na al'ada,sai a daura mana aure.ta sake kallon shi,sai me daga nan?ya ce, a kai ki gida na,ta ce,ina?ya ce,cikin gari,ta ce daga nan sai me?kuma me zanyi a gidanka?ko kaima kana da shanun ne da zan dinga tatsar nono ina kaiwa kasuwarku.ya ce,aa abinci kawai za ki dafa min,sai in kin haifa min yara ki kula min da su.ta rufe fuska,zan tafi ya ce,haba da sauri haka muna hira mai dadi? ya ce,saada ce ke jira na za mu je talla.ya ce,wace ce saade?ta ce,'yar'uwa ta ce, kanmu daya,ya ce,tare zaayi maku aure?ta ce,ni kan zan tafi ta fada tare da rufe fuskarta.ya ce, ba na son tallar nan,ta ce,ni kan ina son zuwa talla,don naga kasuwa,kai kam,me ya sa baka so?ya ce,ina tsoron kar wani ya kwace min ke.ya ciro tsarabar sarka cikin gidanta ya ce,ga wannan,ta amsa da murna. tana godiya.ya sake fiddo da sabbin kudi 'yan naira goma-goma ta yi ta godiya ya ce,mata zai dawo jummaa ta ce,sai ka zo,cikin abinda bai fi wata daya ba ya mallaki zuciyar 'yar fullo.lyaye sun shiga, inda aka tsayar da rana,sai ardo ya dawo daga aikin hajji.su biyu aka hada bikinsu da saade,ita an kai ta wata rugar fulani da ke kusa da su.lta kuma saudatu can masari aka yi da ita,inda mahaifinsu ya ba su daki. satinsa guda ya koma katsina,a nan tudun wada ya nemi daki,ya koma ya dauko ta,ya saka ta lslamiyya saboda ya lura tana da karancin ilimin addini.ta kasa fahimtar cewa shi din fa mijinta ne,fa di take,yadikko,ta ce, ka da ta bari namiji ya taba ta,balle ma jikinta,ita kan ba 'yar iska ba ce. sai da ya lura ta saka hankalinta a karatu,kuma tana fahimta,sai ya samu malamin ya sanar da shi matsalarsu,nan malamin ya cire minti biyar kullum yana yin nasiha ga dukkan dalibansa don akwai me irin matsalar addini bai rufe komai ba,don haka bayani filla-filla ya dinga yi masu ya yin. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (47)Nasihar.sauda ta fahimci komai,kuma ta mika wuya ga mijinta game da neman gafarar sa,lokacin watannin su goma da aure, shi kam yayi ta ji da ita tare da kara son ta tamkar ya ba ta kamshi. sunyi shekara uku,kafin ta samu cikin farko,ta sauka lafiya danta namiji, ya ce,sunan mahaifinsa aliyu,suna kiran sa abba, kullum kara son saude ya ke yi,saboda biyayyanta da ladabi.a wannan lokacin mahaifinta ardo ajalinsa ya sauka,sun shiga tashin hankali,domin damuwarta ta tayar da hankalinsu sosai.tana nan a rugarsu har ta yi sati biyu da kyar ya lallabe ta suka dawo. Bayan iyayensu sun fita takaba,sai aka yi masu rabon gado,sauda ta samu shanu tara da raguna, saboda su biyu ne a gurin ardo,bashir ya ce,ta ba shi aronsu ya saida,zai fadada kasuwancinsa,in komai ya daidaita zai maido mata da shannunta ko kuma kudinsu.
Chapter 11 · 0% Book details