← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 89

Sashe 40

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

da gske? Kai inajin wasa yakeyi, zalayarki kawai yake.
Kin ta6a ganin mai aikata irin wadannan qazaman
laifukan sannan ya fada ma matarsa kai tsaye? Dole
zaiji shakka. Ki barshi bari yazo.
Na’ima tace, ai yace, ba zaizo ba, shi yana aiki. Momy
ta yi shiru tana ta kallon Na’ima cikin matuqar
mamaki, sannan ta miqe. Muje gurin nasa, mara
mutunci kawai. Na’ima ta kalleta. Da kin barshi kawai
momy, tace muje kawai, bazan dauki raini ba, gara
in taka masa birki.
Ta tasa Na’ima suka nufi saman. Yana latse latsensa a
computer, yaji shugowarsu, amma sai ya dauke kai,
yayi kamar baiji shugowarsu ba. Saida momy tace,
bakaji Sallamar mu bane? Sannan ya waiwayo,
fuskarsa babu annuri, yace, naji. Ina jinku, aiki
nikeyi, ina kwana? Duk da baice su zauna ba saida
momy Nafisa ta zauna, sannan tace “lfy” shine wato
Abbas nace kazo, amma kacemin kana aiki ko? Ya
nuna computer da hannuwansa guda biyu, ba gashi
ba kina gani? Ya juya yaci gaba da aikinsa. Tace, to
zaka iya bani ‘yan mintuna muyi magana? Ya hada
tafukan hannuwansa wuri daya ya murza tamkar
mai jin sanyi, sannan yace, kamar minti nawa? Ta
zaro ido cikin mamaki. Abbas ni kk tambaya? Ashe
baka da mutunci har haka? Da sauri ya juyar da
kansa gefe yana kuma dannar zuciyarsa, don kar ya
nuna mata ainihin kalarsa. Taci gaba da cewa, to
zuwa nayi inji laifin da Na’ima tayi maka da har zaka
soma wulaqanta ta daga kawo ta.
Har na qaryata ta, sai kuma gashi nima ka gwadamin.
Ya kalli Na’ima, me nayi miki harda zaki kai qara ta?
Tace, ko Yanxun dana shigo ba na sameka kanayin
magana da wata bane? Ya daga murya cikin zafin rai
yace, me ya dameki don kin sameni ina waya da
wata? Meye naki a ciki? Ya kalli momi, tunda taxo
gidannan ban ta6a shiga harkarta ba sbd banason
matsala. Tayi harkarta inyi tawa.
Momy tace wannan kuwa ba zai yiwu ba kana
mijinta. Sannan kace, kowa yayi harkarsa? Ko kuwa
dama baka amince da auren bane? Ya miqe tsaye
yana kallon momy tare da cewa, “au dama baku sani
ba? Ya girgiza kai, ni gsky mimi na gani nace inaso.
Momy tayi shiru tana kallon sa, gabanta ke faduwa,
damuwa ta bayyana qarara akan fuskar ta. Ta sauke
ajiyar zuciya, ta rasa me zata ce, sai ta kalleshi tare
da aje fushinta, to ynxun me kace? ko ince me kk
nufi? Ya kalleta, ban gane ba.
Momy tace, matsayinta. Yayi murmushi, sannan ya
koma ya zauna kan kujerar computer tare da yin
juyi. Ban sani ba gsky. Momy ta miqe tsaye ta sake
daga murya, to me ya hana ka cewa iyayenku baka
sonta tun kafin a daura auren? Yace, momy karki kiji

haushi na. Ko na fada musu ba zasu fahimceni ba a
wannan lokacin tunda suna da burin kansu. Ya nuna
Na’ima, ke kuma ki bani lokaci, in burikan iyayen mu
sun cika, sai in sauwaqa miki. Da sauri momy ta
katse shi da cewa, ha Abbas, ai ko mutuwa tana
kunyar idon mahaifi, inji masu magana.
A gabana kk fadin bakason ‘yata? Yayi guntun
murmushi, momy kenan. Don dai ni ba danki bane,
saiki takura min? Ya kamata kusan cewa, shi so ba’a
masa dole. Ni mimi na gani nace inaso. A tsari na
farar mace nake so. Kinsan kowa da ra’ayinsa. Qila
da fara ce da nayi manage. Momy ta miqe, shikenan
na fahimce ka. Yace, Yauwa nagode da kk fahimceni,
kuma naji dadin haka, don ni mutum ne mara son
takura. Ta kalli Na’ima, tashi muje.
Na’ima wadda ke ta faman kukan takaici, ta miqe
tana cewa, nidai kawai momy ki tafi dani, bazan iya
zama ba. Yace, kin kawo shawara, ku tafi tare kawai
momy, ta dube shi a qufule.
Babu inda zanje da ita, zan kuma sanar da
mahaifiyar ka, daka-duka auren yau kwana biyu,
sannan ace tana gida? Yace, umm, yadda kuka za6a
haka zakuyi. Amma in da zakiji shawara ta, da sai
ince kar ki kai qara ta gurin momy na, sbd itama
irinki ce, tafi son ‘ya’yanta akan na kowa. Ni dai kunji
ra’ayina. Sannan don Allah a daina takura min, a
kuma guji shiga harkata. Basu sake cewa komai ba
suka fice. Shi kuma yaci gaba da aikinsa. Dakin
Na’ima suka koma sukayi jugum-jugum. Na’ima tana
ta faman kuka. Mommy ta kalleta cikin damuwa,
sannan tace, share Hawayenki. Badai farar mace
yakeso ba?
Na’ima tabi ta da kallo. zamu duba mayukan cikin
akwatinki, in babu wanda zaisa kiyi fari, saimu shiga
kanti. Kafin da wata guda, sai kin koma tamkar
baturiya. Daga nan sai ki dinga yin duk wani abu da
zaki ja ra’ayinsa. Na’ima ta dan ta6e baki tallafe kanta
sbd tsabar ciwon da yake yi, tace, hmm mu gwada
mu gani, haka suka sauke kafatanin kayan shafan
dake cikin lefen, amma basu fahimci komai ba,
ma’ana basu gane ko mayukan zasu iya yi mata
bilicin din ba.
Momy ta dafa Na’ima, cikin sigar lallashi, karki damu
Na’ima, zan nemi Shawarar Aminiyata hajiya nana,
domin na ta6a jin suna zancen qwayoyin da suke
saka fari. Na’ima tace, to kafin ta wuce saida ta
tabbatar hankalin ‘yar tata ya kwanta, ta nuna mata
cewa ta zauna tayi haquri, ta zauna kada ta sake
maganar tafiya. Ta kwantar da hankalinta, wata rana
sai abin da tace masa zaiyi.
Momy dai ta tafi cikin takaici, ta bar Na’ima cikin
damuwa. Ta jima sannan ta tashi ta shiga cikin kicin

dinsu masu aikinta ssuna ciki. Dattijuwar tana zaune
tana firar dankali. Yarinyar kuwa tana wanke-wanke.
Daqyar ta amsa gaisuwar da suke mata, wai ita dole
ga matar gida, ta kalli tsohuwar, me za’ayi da wannan
dankalin? ‘Yalla6ai ne yace ayi masa cips da shayi.
Na’ima tayi sororo, cikin muzanta, domin itace ya
dace tayi masa, ko kuma tazo tasa ayi masa, amma
sai ta wayance da cewa, dama har ynxun baku kai
masa ba? Dattijuwar tace, hajiya zuwansa kenan
yazo yai magana. Na’ima tace, ni bance sai kinyi min
lissafi ba. Inason ki gasa min bread da kifi, Na’ima
kenan. Wannan kuma ai cimar mimi ce. Yinin ranar,
Na’ima ta kasa sukuni.
Domin ita gsky tana matuqar son Abbas. Tana jin
lokacin da zai fita wuraren daya saura na rana, ta fita
taje gurin window tana leqensa har ya dau motarsa
ya fice. Qarfe goma da mintuna na dare, taji
tsayuwar motarsa. Cikin sauri ta fito falonta wanda
tasan nan ce kadai hanyar binsa don hawa samansa.
Ta dau gayu cikin riga da wando matsattsu, kanta
babu dan kwali, tayi wankan turaruka har maqaqi
suke mata a wuya.
Sai dai kash! Tayi dana sanin fitowa daga dakinta,
don burge angonta, domin kuwa da wata budurwa
ya shigo, bayan ya buga alarm ta bude, sororo tayi
cikin tsananin kishi, ba tada wata power da zata iya
ce musu wani abu. Kuka ta saka sannan ta juya ta
nufi dakinta. Abbas ya kalli Jenifer, kin gani ko? Har
ynxun babu kamarki, tayi murmushi suka nufi
samansa bayan ta saqalo hannuwanta a qugunsa.
Tana fadin, na yarda honey.
Cikin matsanancin kuka, Na’ima ta kira layin momy,
wadda shugowarsu kenan daga asibiti, ita da daddy.
Jikinsa da dan sauqi, shine ya matsawa likitan ya
sallamesu, don ya tsani zaman asibitin. Momy Nafisa
bata son daddy yaji wannan matsalar, don haka taqi
dagawa, saida ta shiga dakinta. Tana dagawa ta fara
da cewa, meyasa bakida haquri ne? Na’ima ba nace
zanyi shawara bane? Zan kiraki da kaina. Tsaya kiji
momy, da karuwa fa ya shigomin gida. Karuwa??
Momy ta tambayi Na’ima. Ta rantse, sannan ta ci
gaba da cewa, ni bansan yaya zanyi ba ynxun, Momy
tace, ki barshi zuwa gobe zanje gurin uwarsa. Na’ima
ta shiga daki, ta zauna bakin gado cike da nadamar
auren Abbas.
Kuka take sosai, amma babu mai lallashi. Qarfe shida
na yamma, innar su Zainabu ta shigo tare da
Aminiyata, inna yalwa, suka sake dawowa gidan
Zainabu, ta danji dama, tana zaune kofar dakinta. Jin
muryar innar tata yasa gabanta faduwa. Rai a dagule
ta kallesu, sannan ta shiga dakin, suka bi ta ciki,
Aminiyar inna ta kalli Zainabu, meye kika dagule rai?
Chapter 40 · 0% Book details