← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 89

Sashe 42

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

mai innar tace ba, sbd lokacin sun dan gota shi, ya
hau sama yana tunanin, to wa suka kawo asibiti? Sai
dai babu mai bashi amsa.
Ya samu har an sawa mimi jinin, har lokacin tana
varci. Likitan ya tambayeshi inda yaje? Yace ya raka
wansa ne. Ya tambayi likitan ko babu matsala a irin
wannan varcin da takeyi? Likitan yace, babu komai
karka damu. Fitar likitan da nurse dinnesai ya kira
malam Aminu suka gaisa. Malam ya tambayi mai
jikin, Ismail yace, da sauqi, sannan yace, dama
mahaifiyar tace take son in tura mata account
number na, nace mata banida shi, amma zan turo
mata na makaranta. Shine nake neman izini. Malam
Aminu yace, babu komai, ko baka fadamin ba zaka
iya amfani dashi. Ismael yace, nagode malam, Allah
ya saka da alkhairi. Malam yace, haba babu komai,
Allah dai ya bata lfy. Ismail yace, Ameen. Suka yi
sallama.
A take ba tare da 6ata lokaci ba, Ismail ya turawa
hajiya Account number din, bada jimawa ba ta
kirashi tace masa zaiga saqo zuwa gobe. Yayi mata
godia, sannan sukayi sallama. Lokacin da zai tafi
sallar magriba, yanason sai yayi isha’i zai dawo don
haka yaje ya fadama nurses din da suke kula da
dakin na musamman dake sama cewa, zaije sallah
koda za tayi motsi tunda suna daf da dakin ne sukace
to, amma yayi sauri don sun kusa tashi, masu
shifting din dare suke jira. Bayan an idar da sallar
isha’i sai yadan kishingida, dan varci yana da fizgarshi
don akwai bashin varcin akansa na tsawon lokaci.
Tun ranar da ya rasa Zainabu baya varcin kirki, har
zuwa shigowar wannan matsalar.
Can sai yaji vibration din wayarsa don ya sa ta a
silent, lokacin da ya shigo masallaci. Ya duba yaga
ashe Mahmud ne. Don haka, sai ya tashi ya fita daga
masallacin, sannan ya daga wayar. Mahmud yace,
nazo baka nan, ina kaje? Gashi ma ta farka. Cikin
sauri Ismail yace, ta farka? Cikin wane hali take?
Mahmud yace, kana inane kai? Ismail yace, ganinan
zuwa, sallah naje. Ya kai qarshen maganar tare da
kashe wayar, take yaji varcin ya sakeshi. Cikin
hanzari ya nufi saman. A bakin qofa ya samu
Mahmud, ya miqa masa hannu sukayi musabaha. A
maimakon gaisuwa, sai Ismail yace, ta farka fa
kacemin Mahmud?
Mahmud yace, eh ta farka sadda nazo. Ban ganka ba,
sai na tambayi nurse tace, kaje sallah. Shine na tsaya
jikin window. Can na leqa sai naga alamun tana
motsi, shine na kira nurse din. Da sauri Ismail ya
bude dakin ya shiga. Nurse daya ce a kanta tana
lallashinta. A tsakiyar dakin Ismail ya tsaya yana
tunanin ta inda zai fara lallashinta. Yana jinsu da

nurse din tana ce mata ya isa mana, ki daina wannan
kukan haka. Nurse dince ta waiwayo ta dubeshi.
Yauwa kazo ka lallasheta. Yace, ko zaki kiramin likita?
Tace, ya tafi, kuma mai shifting din dare baizo ba.
Ya isa bakin gadon ya daura hannunsa saman
goshinta, sannan ya rusuna saitin kunnenta. Mimi
kiyi haquri da wannan kukan. Ba magani bane, khalil
ynxu babu abinda yake buqata agareki sai Addu’a, ki
roqa masa yafiyar Allah, yafi miki wannan kukan.
Batayi magana ba, kuma bata daina kuka ba. Haka da
Mahmud yana tayi mata sannu, sam bata san ma
yanayi ba. Duk wani lallashi da ya kamata, Ismail yayi
mata, amma sam bata ma san yana yi ba. Don haka
ya miqe daga kusa da ita, ya nufi waje ya zauna akan
benci tare da riqe kansa mai sarawa. Mahmud ya
biyo shi ya dafa shi, sannan ya zauna kusa dashi.
Ismail Yace, Mahmud yadda kasan in fasa kuka haka
nakeji. Yarinya sai kace wata jaririya, bata jin lallashi.
Nifa in ta qure ni, sai in tafi in barta. Domin yadda
bata sona, nima bafa yimin tayi ba. Gashi sai wani
uban kuka takeyi, ban san yaya zanyi mata ba.
Mahmud ya dafa shi, kar ka damu Abokina, kayi
haquri. Ka jure, ka jajirce, in ka tafi to ka barta da
wa? Kada ka manta matarka ce, wadda take a
matsayin ba tada kowa, sai kai. Kayi iyakar yinka, ka
hada da Addu’a. Zamu taya ka, wata rana sai labari,
ka jure, karka sare, Ismail ya sauke ajiyar zuciya, tare
da cewa, abin ne ya fara isata. Mahmud yadan girgiza
kafadarsa kadan, alamun lallashi, kar ka damu akwai
Allah. Ya sake sauke ajiyar zuciya. Allah ya taimake
mu. Mahmud yace, Ameen, sannan ya miqe, bari in
tafi, gidansu rabi’a zanje.
Insha Allahu gobe zamu zo da ita. Ismail ya kalle shi
da dan murmushi, kace ina gaishe ta. Sai kunzo. Ya
miqe ya taka masa zuwa gurin matattakalar benen.
Har ya juya zai tafi, Mahmud yace, Ismail kaga na
manta ko? Ismail ya waiwayo. Yaya akayi? Mahmud
yace, na zo ne in fada maka anyi admission fa. Haba?
Inji Ismail. Mahmud yace, sosai ma kuwa. Ya kamata
muje mu duba. Ismail yace, bari mu gani ko zuwa
gobe ne, in wannan rigimammiyar ta dangana, sai
yaya Amina ta zauna da ita muje, Mahmud yace,
shikenan Allah ya kaimu goben.!
Yadda mimi taga rana haka taga dare, kuka kawai
take, babu qaqqautawa har mutyarta ta dishe. Tun
Ismail yana lallashin ta, har ya gaji ya fice yayi alwala
don yin shafa’i da wutirinsa tare da da addu’o’insa
daya saba. Haka suka kwana har asuba tayi ya tafi
sallah. Gurin qarfe taran safe aka shigo aka soma yi
mata shirin yin aiki, wato dori. Goma saura aka shiga
da ita. Lokacin ne malam Aminu ya kira Ismail yana
sanar dashi cewa, yaga alert. Ya duba yaga an turo

kudi naira dubu dari(100,000). Kuma yaga sunan
saudatu bashir.
Ismail yace, eh, saqon da mahaifiyar ta ta turo din
ne. Ynxun haka ma an shiga da ita gurin dori. Zan fito
Anjima sai in amshi katin ATM din in yana gurin
Mahmud. Dama kudin hannuna sun qare kaf. Yace,
kar ka damu, ko nine sai inje in ciro maka tunda
akwai mashin a gurina. Allah dai ya bata lfy. Ameen,
inji Ismail. Sannan sukayi sallama. Ismail ya saukar
da ajiyar zuciya, har ya danji dadi sbd samun
wannan kudin, domin hannunsa babu kudi. Tagumi
yayi yana tuna irin kukan da mimi tayi ta rerawa jiya.
Ko sallolinsa yayi ne dai kawai, amma gunjin kukanta
yana daukar hankalinsa. Cikin wannan tunanin ya
hango yaya Amina. Yaji dadin zuwanta sosai, domin
zamansa shiru ya isheshi.
Ya tare ta, tare da amsar kular hannunta da kuma
ledar ruwan pure water, suka shiga cikin dakin, tace
ina mara lafiyar? Yace, an shiga da ita dakin da za’a yi
mata dori. Ya bude kular, dame kk zo? Tace, alala ce
don nasan kanaso. Yayi dan murmushi, a fili yace,
naka sai naka. Yaya Amina nagode da hidima. Tace,
haba Ismail wa gareni banda kai? Kaima kuma
bakada wadda ta fini. In ban maka ba in ma wa?
Donma Allah yasa ni ba mai hali bace. Yayi dariya,
hakane yaya. Allah ya qara mana zumunci. Tace
Ameen, yaci alalar sosai, yana ci suna hira, har take
bashi labarin cewa, su inna dasu fatu sunce sunanan
zuwa anjima.
Yace, Allah ya kawosu qila ma ke zasu samu yaya.
Sbd jiya Mahmud yace min anyi admission, zamuje
mu gani ko Allah zaisa mu samu. Don kinsan
qasarmu sai Allah. Qiri-qiri zaka ci jamb amma saika
rasa admission. Sai ace baka ci post UTME ba. Mu dai
munce zamuje mu gani. Sannan mahaifiyar mimi ta
turo kudi a account din makaranta zanje in cire.
In kuma malam ya ciro shikenan, don yace koshi sai
yaje ya ciro tunda da mashin a gunsa. Sha daya
saura aka fito da mimi daga dakin da aka yi mata
dori, tamkar wadda akayi wa operation. Nurses suka
kwantar da ita akan gadonta tare da maqale
qafafunta da gadon. Bayan sun gama kintsa ta ne
likitan shima ya shigo, tare da ainihin doctor salis,
likitan dayake kula da ita. Sunyi ma Ismael bayanin
babu matsala, insha Allahu zata samu lfy, cikin zolaya
doctor salis yace ma Ismael, “yar amanarka zata
warware. ” Ismail yace, Allah yasa. Sannan suka
rubuta magunguna suka ce ya siyo kafin ta farka.
Yace musu zata iya cin abinci? Suka ce eh, zata ci
komai in ta farka. Wannan varcin ma da takeyi anyi
mata allura ne sbd ta wahala. Sai azahar Mahmud
yazo, don haka nan yabar yaya Amina suka tafi. Sai
Chapter 42 · 0% Book details