← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 89

Sashe 13

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta yi,ni haushi na daya,mene ne na kin fada mani,wa zai hana shi aure?kuma da ya ki kawo ta,inda ta ALLAH ta kasance a kanshi ta zo da yara ta ce ita matarsa ce za a yarda cikin sauki? lta kuwa hajiya binta zagewa tayi tana ta tsula rashin mutumci duk da cewa gidan mutuwa ne, karara ta nu na kishinta. Shima duk da yana cikin ciwon mutuwa,ya girgiza da samu nafisa a gidan, sam bai so ba.dole ya hakura ya jure masifar da hajiya binta ta dinga yi masa son ranta,ta fada ma shi maganganu.lta kuma sauda bata ce komai ba,sai rashin yin maganarta yafi daga mashi hankali fiye da masifar da hajiya binta ta keyi.sai da aka yi bakwai sannan kowa ya watse suka koma gidajensu. Daga nan yasa aka maida nafisa abuja,shi ma ya nufi katsina. Har cikin daki ya samu sauda tana shirya yaranta zasu tafi lslamiyya,sai da suka tafi sannan ya zauna kusa da ita ya ce,sauda na san nayi miki laifi,don ALLAH ina son ki yafe min, dama kullum cikin tunanin zuwa wannan ranar nake yi.ta kalle shi laifin me?ya kasa bata amsa,ta tabe baki baka yi min laifin komai ba.ya ce,ai nina san nayi laifi,ki fahimce ni,sam banyi da nufi ba. Tunanin halin da zaki shiga ne ya hana nina fada miki,saboda naga yadda muka yita samun matsala a lokacin auren hajiya binta,ni kuma bana son bacin ranki sam.ta ce,umm!ni yanzu lamuranka babu ruwa na da su,ya ce,don me kika ce haka?ta ce,na zata ni da kai duk daya ne,ko mutuwa zanyi don kishi ai ka fada min in ya so in mutu.kuma bayan kayi ma,ai sai ka fada min.ya ce,to nayi kuskure, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (55)Ai lokacin auren ne yazo babu shiri don ALLAH bari in fada miki yadda abin ya faru. Lokacin ina son sayan wasu filaye a cikin garin abuja,saboda ina son fara harkan gine-gine ina saidawa,to mahaifinta shine shugaba a maaikatar filaye, da safiyo,ni da lauya na muka je gidansa don ganawa ta musamman kamar yadda ya bukata, shine na ganta,amma har ga ALLAH ba sonta nake yi ba.don in samu saukin wannan harkan shi yasa na nuna ina sonta,kuma alhamdulillahi sai ya bani ita. su alhaji lsa mani ne suka amsar min aurenta, ban zaci zamu dade a cikin auren ba,domin nayi ne na wani lokaci,amma sai mutuncin mahaifinta,da yanda ya sakar min nake samun alherin filaye,shi yasa na hakura.abinda yasa ta kara shiga raina shine yadda take son MIMI sosai har ma wani lokaci ina cewa a ce ita ce mahaifiyar MIMI,domin bata takura mata.hajiya sauda ta ce,wato ita MIMI har da ita a munafunta ta,yayi mata kyau.ya ce,kar ki ga laifin ta,ta ce,kaima ba cewa nayi kayi laifi ba cewa,na yi don me ka boye min?ai aure ba laifi bane,na isa in hana ka yi? ya ce,ba zan kara ba,ta ce, nan gaba in zaka cike ta hudu na roke ka,ka sanar damu.ya ce,ai na gama sauda.ta ce,uhum,haka dai ka ce,ni yanzu na daina yarda da kai.ya shiga lallashinta da fada mata maganganu,tsakanin mata da miji sai ALLAH,nan dai suka sasanta tamkar basu taba samun matsala ba,har ranta tabar abin a kaddara. Tun da ya samu sauda da sauran danginsa suka san da nafisa,sai yaga bashi da matsala,tuni yake son ajiye MIMI a gurin nafisa amma babu hali saboda ina zai ce ya kaita? amma yanzu ga dama ta samu,tuni ya tattara ta ya maida ta,MIMI mata yi murna da hakan,don ta san momy nafisa na sonta. lokacin da za su tafi kalma daya ta fada mishi,alhaji tunda kana ganin zaman MIMI a can yafi guri na,to babu matsala,amma ina son kasan cewa,duk iyayen da basu sa dansu kuka ba, to wata rana sai dan ya sasu kuka ya ce,wannan kuma irin naki tunanin kenan,ni dai zan maida 'yata inda za ta samu 'yanci ta kuma huta. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (56)Lallai MIMI 'yargatace,domin a dankararren gidan da ya gina a abuja maitama,an tsara gidan sama ne hawa daya,amma saman na MIMI ne kowa yana kasa,dakin baccin ta komai pink don shine kalar data fiso.dayan dakin kayan karatun ta ne a ciki,shi kuma dayan an gyara shi an rufe.lokacin shekaranta goma kacal, momy nafisa tana yin iya yinta don ganin ta danne zuciyarta ta kauda kanta ga abinda alhaji ke yi ma MIMI,ba don komai ba,sai don ta samu shiga da kuma abin duniya da yake sakar mata.amma a badini bata son MIMI,bata kamar tana sonta,kullum burinta yanda zata shiga tsakanin su,don ko makaranta da zai sata wanda 'ya'yan jiga-jiga abuja ke zuwa yasata wata rana za shi katsina shi da MIMI ya ce bari su fara zuwa malumfashi don ya gasu hajiya binta,ya kuma ga gonarsa su wuce, tunda binta ta ganshi da MIMI ta hade rai,lokacin wayoyin hannu basu yi yawa ba,sai ta ga MIMI da dankareriyar waya mafi tsada a wannan lokacin.sai binta ta bata rai ta shiga jero zantuka marasa dadin ji,tana fadin ma alhaji cewa ya cika son kai,ba shi da hakki ya bambanta MIMI da 'ya'yansa nan fa ranshi ya baci an tabo rabin zuciyarsa ya ce,duk abin da zata yi,ta yi mishi don shine ya auro ta,amma ta cire sunan MIMI a bakinta, nan fa suka yi kaca-kaca abin har ya kai su da yi mata saki daya,ya tattara yaranta guda uku suka wuce katsina. Ran sauda ya baci matuka,ta duddungure MIMI a gabansa,ya dai daure fuska amma bai yi magana ba,ta matsa mishi lallai sai ya dawo da hajiya binta,ta ta sashi gaba suka je biko, bayan binta ta dawo ne ta zo kwasar 'ya'yanta amma sai zainab taki binta,saboda suna yin wasa dasu husna,ta yi-ta yi,yarinyar ta ki dole ta hakura ta barta. bayan husna hajiya sauda ta sake haihuwar hasina wadda ta zame mata auta, don ta sha wahala a haihuwar tamkar bazata tashi ba,sai da aka yi maka aiki,alhaji ya firgita sosai don haka ya ce da likita ayi masa taimako a tsaida haihuwar.hajiya binta ta kara biyu najaatu da fadila su biyar kenan. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (57)Momy nafisa ita ma ta kara biyu mas'ud da aisha.bayan MIMI ta kammala secondary ta ce da alhaji bishir mahaifinta, daddy ni fa nafi son in fita waje america ko england ko spain.ya ce ba matsala ta zabi duk wadda take so, ya sayi hannun jari da sunanta,banda kamfanin da ya bude duk wata ribar tana shiga asusunta,sai da ya gama komai sannan ya samu sauda da batun har yana kara fada mata cewa zata fita karatu waje,hajiya sauda ta ce duk bata yarda ba,sun yi rigima sosai dole ta kyale shi. Shi kuma jin ta kushe kasashen turawa,sai ya ba MIMI shawara ya ce ta tafi dubai,tunda can garin larabawa ne,da kyar MIMI ta yarda ta tafi don yin karatun law,zabin ta shine ta zama lauya,amma in a son mahaifinta ne tayi karatu a kan kasuwanci, don ya dora ta a kan alamuransa.abba ya gama digree dinsa a kan mass com,ya samu aiki a banki,ya na kaduna,kuma ya auri samira wadda suka hadu a a ABU zariya, mahaifinta shine ambasadan najeriya a Egypt.su na da yaro daya, wanda suka sa mishi sunan alhajin suna kiran shi ta karshe,don karatun shi mai tsawo ne,likita ne fannin magunguna.shima abdulkarim shekarar shi ta karshe yake,engineering ya ke karantawa.lta kuma MIMI ta cinye shekarar farko ne ta zo hutu,za ta shiga ta biyu,wannan shine asalin su MIMI. Tunda lsmail ya koma dakinsa yake mamakin MIMI,har me ta dauki kanta da take wani ji da kanta haka?shi kam ba maula yazo ba,don haka baya zaton zai kaskantar da kanshi,ya kira layin mahmud suka gaisa,mahmud yana tsokanarsa,da cewa mutanan abuja garin daula,lsmail ya ce,gaskiya duk da ban fita cikin garin ba a gidan da nike kadai na tabbatar cewa akwai daula.mahmood ya ce,ai mutumin nan ya shahara,to yaya kuka yi da yarinyar nan?lsmail ya ce,kai dai bari,nan ya sanar da shi duk yanda suka yi,mahmud ya ce kar ka ce zaka yi zuciya,ka natsu ka danne zuciyar ka in ta shiryu zaka samu lada.sannan ga mahaifiyar ta, ko don ita ya kamata ka jure.lsmail ya ce shikenan, amma fa sai dai mu zuba. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (58)Tunda lsmail ya koma dakinsa yake mamakin MIMI,har me ta dauki kanta da take wani ji da kanta haka?shi kam ba maula ya zo ba,don haka ba ya zaton zai kaskantar da kanshi,ya kira layin mahmud suka gaisa, mahmud yana tsokanarsa, da cewa mutanan abuja garin daula,lsmail ya ce, gaskiya duk da ban fita cikin garin ba a gidan da nike kadai na tabbatar cewa akwai daula. mahmood ya ce,ai mutumin nan ya shahara to ya ya kuka yi da yarinyar nan? lsmail ya ce,kai dai bari,nan ya sanar da shi duk yanda suka yi,mahmud ya ce kar ka ce zaka yi zuciya,ka natsu ka danne zuciyar ka in ta shiryu zaka samu lada sannan ga mahaifiyar ta,ko don ita ya kamata ka jure. lsmail ya ce shikenan,amma fa sai dai mu zuba. lta kuwa gimbiyar,wato MIMI,sintiri ta dinga yi a falon tana nazarin wannan mutumin wane irin hukuncin ya kamata ta yanke masa?wata zuciyar ta ce, don kin kore shi,ai ba ki rama ba,kin shirya me zaki ce ma hajiya?kar ki manta dai data gargade ki sosai sannan aka turo min ki shi.a fili ta ce,to me zan mi shi in huce?ta kalli wayarta, yawwa bari in kira mina dakingari. Bakin gadonta ta shiga, bedroom ta zauna,mina ta daga tare da fadin khadija masari ya?MIMI ta ce,lafiya dakingari,kin san mene ne? (ta ci gaba)mom di ta ce in fada miki ta dage sai wani malami ya koya min karatun islamiyya.mina ta ce,mene ne laifi?MIMI ta ce, dan rainin wayo ne,kinga yanda yake son nuna min iyaka ta?nan ta kwashe komai ta fada mata,mina ta ce,kin san me zaki yi masa? MIMI ta ce,aa,mina ta ce,in dad din ki ya dawo ki sa a kira shi,sai ki ce kina son a ware lokacin karatun ku minti talatin ko awa daya,yanda dai kika zaba, kinga ba zai taba tashi daga gurin karatun ba sai lokaci ya cika,MIMI ta ce, yawwa kin kawo shawara, kin ga sai in yi masa duk cin mutumcin da naso na tsawon lokacin,kuma dolen shi ya tsaya
Chapter 13 · 0% Book details