Sashe 49
Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
bata zo ba. Suka ce. Shikenan. Mu dama munga har
kwatancenka anyi mata tace kaine.
Yace to bari inje qila bayan mun fita ne tazo. Shiru
sukayi masa don sun kasa fahimtarsa, kamar yadda
shima ya tafi ba tare da ya fahimcesu ba. Ya shiga
dakinsu ya isa gadon mimi, ya leqa fuskarta har
lokacin idonta biyu. Yace, mimi bayan fita ta anyi
wata baquwa? Tace A’a sai dai ina neman wata
alfarma guda daya. Ya zagayo saitin fuskarta.”ina
saauraronki” yadan rusuna sbd Mimi bayayin
magana da qarfi dama ita. Tace, banason ka sake
cemin mimi, sbd sunan yana tunamin da gidanmu.
Idanunta sukayi narai-narai. Ya girgiza kai, a hankali
yake magana tamkar rada wane suna kk fi son in
kiraki dashi? Tace, khadija kadai ya isheni. Yayi
murmushi. Nima zanfi so ince miki khadija. Sbd
suna ne mai dadi da ma’ana. Allah yasa halayenki su
rikide su koma irin nata. Ta kalleshi, idanunta sun
nuna alamun son qarin bayani. Yace matar manzon
Allah ta farko sunanta kenan, kuma itace mace ta
farko data soma kar6ar musulunci a tarihi.
Ta sadaukar da dukiyarta sbd addinin musulunci.
Sa’annan itace ta haifawa ma’aiki ‘ya’ya guda shida.
Kinga ko anan aka tsaya ta kai daraja. Mimi ta
lumshe ido, ta bude bata ce komai ba. Cikin zuciyar
ta taji dadin jin asalin sunanta a takaice. Shi kuma
ganin bata yaba ba, sai yace aransa, ashe wannan fa
bata san kan musulunci ba. Allah yasa ta san
wadanda nake magana a kansu. Ya dago ya dubeta.
Kin fahimci wadanda nake magana akansu? Ta
dubeshi da sauri, sai kace ba musulma ba? Duk
wanda aka haifa a cikin musulunci, kai ko ba
musulmi ba yasan mai tsira da Aminci.
Ismail yayi murmushi mai sauti, sbd shi in har za’a yi
hira akan addini yana Jindadi. Sannan yace, nasan
kinsan shi mana. Na zata dai baki fahimceni bane.
Kinsan tarihinsa ai? Tayi shiru don bata sani ba. Yace
inada wani littafi da wani malamn sunna Mutumin
kirki ya fassara shi zuwa hausa da turanci, zan kawo
miki in naje gida. In kin karanta aciki zakiji tarihin
Annabin Rahma, da iyalansa, da nasabarsa, zuwa
jarumtarsa har zuwa mutuwarsa. Har lokacin bata ce
masa qala ba.
Ya sake cewa, in kin gama dashi zan sake baki
wadansu littattafan ki karanta na Addini. Zasu
taimaka miki wajen fahimtar me musulunci ke nufi.
Tsaki taja, sannan tace, kana nufin can dama bansan
komai a musulunci ba? Yace ba haka nake nufi ba.
Tace shikenan, ni inason ka fadama doctor na gaji da
qafafuna a haka ni kam a sauke min qafafuna daga
wannan sagalewar na kasa varci. Yace, to zan fada
masa. Amma ynxun kiyi varcinki. Shiru tayi masa.
Bayan ya idar da sallar nafilolinsa cikin dare, sannan
ya nufi gadon mimi yayi mata addu’o’i ya shafa mata,
sbd yau ya manta bai mata ba har varcin farko ya
daukesh. Sannan ya koma kan gadonsa ya kwanta
yana tunanin rayuwa mai juyi da canji a kowane
lokaci. Tunanin wadda akace tazo nemansu ya fado
masa, to ko wacece? Ko kuma cikin ‘yan uwanta ne?
Haka yayi ta tambayar kansa amma babu amsa. Sai
kuma yaya Amina ta fada masa cewa, dasu inna suka
zo tare da matan yayyinsu sunce zasu je su duba
Zainabu. Sai yake cewa, lallai kuwa yaga innarta da
yalwa Aminiyarta anan asibitin, to me ya samu
Zainabun? Yaya Amina tace, oho. Kai ina ruwanka ma
da wata Zainabu tunda matar wani ce? Yace hakane.
Daganan abubuwa sukayi yawa, bai sake tuno da
batun ba sai yanxun. Sai dai duk da haka bai kawo ko
a ransa cewa, Zainabu ce tazo nemansu ba.
Yaya Amina ta shigo, lokacin likitan da yayi dori yazo,
kuma yace, komai yana tafiya daidai. Sannan yasa an
cire mata qafafun sai aka dora mata su kan filo.
Sannan yace, bayan sati biyu in ya dawo sai ayi
hoton qafar sbd a gani ko qashin ya hadu da kyau.
Mimi tace, yaya don Allah za’a iya yimin wanka? Yaya
Amina tace, ki qara haquri mim.. Ismail yace, “yaya
ta ce batason mimi dinnan, a kirata da khadija. Yaya
Amina tace, tanada gsky. To khadija kiyi haquri zuwa
dan kwana biyu, kada muje wanka wanka muyi fami.
Ba ga shi kullum inayi miki gugar jiki ba? A jikinki
babu datti. Takai hannu ta ta6a gashin kanta ta
sunsuna.
Allah yaya, sai inji kamar ina wari, har ta gashin
kaina. Yaya Amina tace, bakya warin komai khadija,
don dai kina da son wanka ne. Mimi ta lumshe ido
tana tuno gidansu da sasanta da dakinta. Ta tuno
gatan ta. Sai kurum taji Hawaye suna bin kumatunta.
Ismail ya dawo kusa ita yace, haba khadija. Menene
na kuka kuma a batun wanka? Wannan fa duk anayi
ne sbd lafiyar ki, garin wanka in aka turgude qafar ko
hannun, kinga sabon dori ya samu kenan ko? “Don
Allah malam ku barni inyi kukana, sbd in nayi ne
nakejin sauqin abubuwa. Ba wai inayi don na raina
qoqarinku bane, ina yi ne sbd ya zama dole inyi. Yaya
Amina tace, ki dinga sassauta wa zuciyar ki dai
domin wani ciwon zai shigar ki.
No related posts.
POST COMMENT
22
Let God take the burden off your shoulders.
Connect now.
GodLife OPEN
22
Ismail ya miqe “yaya ni dai bari in barki da ‘yar
rigimar nan taki inje gd inyi wanka. Sannan zanje
gurin malam Aminu. Su Mahmud dazun ya kira ni
wai lallai yana nema na. Tace to sai ka dawo. Amma
fa kar ka taushe hannu sbd yau waina nakeson yi,
zan koma gida da wuri. Ismail yace, zan dawo da
wuri insha Allah. Ya kalli mimi, khadija bari inje in
dawo, ko kina son wani abu inzo miki dashi?
Ta girgiza kai alamun a’a. Taci taci gaba da kukanta.
Yace, shikenan sai na dawo. Yasa kai ya fice mimi ta
qara sautin kuka. “yaya malam ya saba da ganin
kukana, ya daina lallashi na ynxun. Yaya tace a’a
bayason kukan ne, shiyasa. Kuma gashi inya
lallasheki bakyayin shiru. Ai khadija a rayuwa in
akace maka kayi haquri, to kayishi.
Karka ce wai kai zakayi tayi, mai lallashinka sai ya
gundira. Mimi tayi shiru. Can tace, Yaya wai kuma
baku da ‘yan uwa ne? Tace me kk gani? Tace naga ku
kadai ne kuke zuwa. Yaya Amina tace, muna dasu
khadija, amma dai basu damu damu ba. Ni da Ismail
ne muke uwa daya. Nan ta ba ta labarinsu. Bata 6oye
mata komai ba game dasu. Mamaki ya cik mimi, tace
dama ana samun haka? Ni kam kishiyar mama na
har tafi mamana sona. Ynxun haka nasan tanaa cikin
damuwa.
Yaya Aminu tace, bana zaton akwai wanda zaifi uwa
son ‘yarta. Khadija duk inda mahaifiyar ki take a
ynxun tafi kowa tashin hankali, sai dai in qila ita mai
kawaici ce. Soyayyar uwa da ‘ya na daban ne kinji.
Amma zaki gane haka nan gaba. Mimi tace, ko
qawayena sunsha fadamun haka, amma har yau ban
gamsu ba. Yaya Amina tace, to ke dame kk dogara
wanda har yasa kk ganin mahaifiyar ki bata sonki?
Mimi tace, zan baki labari, saina qara jin sauqi,
amma ina da hujjoji masu yawa.
Shi kam Ismail har ya Sauka samansu, ya dauki
hanyar fita, sai ya fasa, ya dawo ya nufi gurin saida
magani domin ya amshi canjinsa. Tun kafin ya
qarasa dan windon da zai amshi canjin nasa, sai ya
jiyo muryar innar Zainabu tana cewa, ni kudina sun
qare banida sauran ko na mota. Wani yace, ina
ruwanmu da qarewar kudinku. Kuma bamu damu
ku sai mata magani ba. Mu dai ku bamu kudinmu,
ynxun da wannan abokin aikin nawa bai ganku ba,
da ynxun kun gudu.
Ismail ya qarasa gurin su daidai lokacin da innar su
Zainabu take cewa, nima ba laifi na bane, Alhaji ne
baizo ba. Dayan yace, ku kirashi a waya mana babu
inda zakuje. Ismail ya miqa wa Mutumin hannu tare
dayi masa sallama suka gaisa, sannan ya kalli Inna
wadda tunda ta ganshi taji kunya matuqa, kamar
tace, qasa bude in shige. Yace, inna lfy kuwa? Tace lfy