← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 89

Sashe 66

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

3⃣3⃣Alhaji bashir ya kalli Hajiya sauda, sannan ya 6alli karas din data wanke masa yakeci, sbd likitansa yace, lallai yana da kyau ya dinga cin karas sbd yana qarawa masu ciwon suga qarfin ido. Yace, "kina dai korata ko?" ba haka bane, ta yaya zan gaji dakai? Yace to kince in tafi Abuja. Tace kawai naga ka dade bakaje bane, kusan tunda ka sallamawa yaran nan kasuwancinka, sau daya kaje. Gashi har anyi azumi, an gama, yau kuma sallah. Yace, shikenan zance Nafisa ta tattaro yarannan gaba dayansu, suzo katsina suyi sallah anan katsina. Sam bana jin dadin yin sallah ko ina inba gida ba. Kinsan wannan. Tace, shikenan suzo nan din. Yace, banda Na'ima tanada tsohon ciki, da sun zo da ita nan itama cikin danginta. Sauda tace, zaiyi wuya minister yabarta, yadda naji kana fadin yanaji da jikansa. Yace, hakane kam. Sai kuma Mimi ta fado mata a rai. Ko ynxun ina Mimi take? Ko tana cikin wane hali? Anya kuwa ba zata bi shawarar Hajiya mardiyya bane? A wani zuwa da tayi ne, suna zancen Mimi, tace ynxun ke Hajiya sauda kin biyema zancen mazannan, kinbar 'yarki ba tare da kinsan halin da take ciki ba? Kiyi tunani fa, su maza ba kamar mu bane, zai iya jure rashin ta, kuma koda wane irin hali take ciki. Hajiya sauda tace, ni banason yace, banji maganarsa ba. Tace, a 6oye zakisa a bincika miki inda take, sai kije ki ganta. Sauda ta danyi shiru tana nazari, can tace, yayi min bayani kuma na gamsu, harma nayi masa alqawari. Hajiya mardiyya tace, shikenan tunda kince haka.
Alhajin ne ya katse mata tunani da cewa, kina tunanin Mimi ne ko? Ta kalleshi. Yace, sauda nima tana raina. Hawayen data jima tana tarawa suka zubo mata. Ya zaro idanu, cikin matuqar mamaki. "Sauda keda kk bani haquri, kuma yau kece da hawaye? Lallai haqurinki ya soma gazawa. Tace, Alhaji inason Mimi kamar yadda kowace uwa takeson danta. Kaga kuwa dole in damu da lamarinta. Da ace mutuwa tayi, na tabbata da ynxun na dangana. Amma tunda tana raye dole in zama cikin tunaninta. Kila ma ynxun ta rasu.
3⃣4⃣Ya matsa hannunta, ba ta mutu ba, ta samu sauqi tun watannin baya, an sallameta daga Asibiti, kuma tana zama gidan 'yar uwar mijinta wadda sukayi zaman jinyarta tare, ko da bata fita, ina zaton zuwa ynxu ta saba da irin rayuwarsu. Ta kalleshi da mamaki, "duk ina ka samu wannan labarin? Yayi murmushi, ke kinsan son da nake yiwa Mimi bazan iya yin da nake tayin iqirari ba. Sbd haka nayi bincike akanta. Tun daga kan likitan daya amshesu har zuwa can Unguwar tasu. Kuma an tabbatarmin yaron yana kula dasu sosai. Haka nan tunda ta shiga gidan 'yar uwar tasa bata ta6a fita ba. In ma ta fita, to mai bani labarin yace, shi bai ta6a ganinta ba. Hajiya sauda tace, lokaci yayi daya kamata mu nemeta, tunda ta horu. Yace, a'a lokaci baiyi ba. Ki sake yin haquri kadan, sbd ynxun haka batun da nake miki mijin nata bayanan, yana madina yana karatu. Sannan akwai wata yarjejeniya tsakanin Mimi da mijinta. Likitan ke bani bayani. Bai fadamin yarjejeniyar da sukayi ba, amma ya bani shawara akan kar mu nemeta da wuri, domin akwai yiwuwar ta sake guduwa. Ya tabbatar min cewa zai nememu da kansa in lokaci yayi, don ya kawo mana ita da kansa, a wata fira da sukayi. Don haka inason ki qara haquri.
Ta sauke ajiyar zuciya. Shikenan Allah yasa munada rabon ganawa, ya sada mu da alkhairi. Yace, insha Allahu zamu gana da ita. Tace, to Allah yasa. Mutuwa ce gatanan da take ci kamar rana. Ynxun kuna tare da mutum, Anjima ace maka ya mutu. Yace, hakane, Allah dai ya bamu cikawa da imani. Dubi maqocin nan namu mutuwarsa ta kada ni sosai. Tare fa mukayi sallar isha'i, lafiya mukayi sallama dashi. Amma sai muka wayi gari ya zama gawa. Sauda tace, ikon Allah kenan. Allah yasa mu cika da imani, in tamu tazo. Ameen, inji Alhaji. Sannan ya miqe yana fadin bari indan fita. Itama tashi tayi donyi masa rakiya. Bayan dawowarta ne ta nufi dakin su hasana don tabasu labarin data samu game da Mimi. Domin kullum suma cikin zancenta suke.
[19/09 6:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

3⃣5⃣Kwanci tashi mai cinye kwanakin bawa. Yau gashi mun wayi gari su Na'ima anayin naquda. Da qyar ta kira wayar momy Nafisa ta fada lata, sbd azaba. Tace, Momy kizo marata tana yimin wani irin ciwo wanda ban ta6a ji ba, ina zaton ma dai mutuwa zanyi. Momy tace, ganinan haihuwa ce. Saida tabi ta gidan Hajiya Nana ta dauketa suka nufi asibiti. Hajiya Nana tace mata ki kira mara mutuncin ki fada masa mana. Ta kira Abbas har sau biyu bai dauka ba. Don haka sai ta kira uwarsa ta fada musu. Ba'ayi minti talatin ba sai gasu a asibitin. An gaisa sama-sama, sannan suma suka nemi wani mazaunin suka yada nasu zangon. Momy Nafisa tana fatan 'yarta ta sauka lfy, yayin da Hajiya Bilkisu ke fatan jikanta ya iso lfy. Kusan awa biyu a haka sannan wata Nurse ta fito tanayi musu albishir da haihuwar 'yarsu, kuma ta samu da namiji kamar yadda hoto ya nuna. Nan aka kaure da murna. Su Hajiya Bilkisu kam tasu murnar tayi yawa. Nan suka shiga kiraye-kirayen 'yan uwa suna fadawa dangi tare da daukan yaron hotuna kala-kala. Qa'idar asibitin, ko lafiyarki lau kk haihu, sai kinyi kwana biyu kafin a sallameki sbd su tabbatar da babu wata matsala. Hakan ta kasance ga Na'ima. Amma randa aka sallameta, rannan tsiya taso ta kaure a Tsakanin su. Domin Hajiya Bilkisu tace, gidanta za'a je, yayin da mai jego tace, itafa ba zataje can ba, Gidansu zataje. Momy Nafisa tace, tunda bataso abarta. Hajiya Bilkisu tace, sam. Nanma Abbas dinne ya kira Alhaji wanda ke umra, ya fada masa halin da ake ciki. Ransa ne yayi matuqar 6aci, ya kira Momy Nafisa yayi mata tatas. Yace kula ta bar masa mata yayi yadda yakeso da abarsa. Kuma yana mai sake sheda mata kar ta bari tayi sanadiyyar auren yarinyarnan. Ba tada yadda zatayi, cikin takaici ta bari suka tafi.
3⃣6⃣Ranar suna yaron yaci sunan mahaifin Abbas, wato Aqilu. Sam Na'ima bataso wannan sunan ba, domin itama taso ne tasa sunan nata mahaifin. Amma yace, ba tada ikon za6a ma dansa suna. Tace, kai kayimin naqudar yaron? Yace ai ba ruwa kk sha kk samu cikin ba. Haka dai take ganin qarfin hali iri-iri akan san da ta haifa. Sai kace wanine cikinsu yayi mata wahalar cikin. Hajiya sauda da Hajiya Binta, duk sun halarci sunan, amma Gidan Momy Nafisa suka yada Zango. Sai dai 'ya'yansu ne sukaje can gidan sunan, domin harda su usaina akaje. Sai yamma sannan su Hajiya sauda sukaje gidan mai jego. Sai dai Hajiya sauda tayi matuqar mamakin ganin yadda Na'ima take a kode, a rame, Na'ima mai garin jiki, amma harda qashin wuya. Hajiya sauda ta kasa dannewa tace, Na'ima kinyi ciwo ne kafin ki haihu? Kai ta sunkuyar, "nayi ciwo sosai Hajiya. Hajiya Binta kuwa baki ta ta6e, tare da cewa, Ai dama hangen dala ba shiga birni ba. Alhaji Bashir kuwa, ta Abuja ya sauka don yaga sabon jikan nasa tare da 'yar tasa. Duk da yana namiji, yayi matuqar mamakin ganin lalacewar Na'ima. Amma sai yayi shiru sbd ya san cewa haihuwa tayi, kuma baisan irin wuyar da tasha ba.
[19/09 6:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa
3⃣7⃣Ismail da Mahmud suna zaune a farfajiyar makarantarsu, inda sukan hadu da abokansu don qarama junansu sani, da qaruwa da basirar juna. Yau kam su biyu ne saura basu riga sunzo ba. Mahmud yake cewa, Ismail kasan me nake tunani? Ismail ya dago kansa daga littafin dake hannunsa, yana dubawa yace, sai ka fada. Mahmud yace, wannan hutun da zamu samu tunda na qarshen shekara ne, yanada tsawo, zamuje gida. Ina tunanin da matata zan taho. "wace matar?" Mahmud yace, Rabi'a mana. Aure zansa a daura mana. Dariya sosai Ismail yayi, sannan yace, ba kace ka fasa ba? Mahmud yace, kai malam haqurina ya qare. Kullum cikin mafarkai, gara kai gwanin azumi ne. Ismail yace, in kaga zaka takura kuwa yin hakan shine mafita. To amma ya batun aikin hajinmu? Don gsky koda hutuna zai qare banje gida ba, nayi wa kaina alqawarin aikin hajji. In na samu yadda nakeso la duk shekara sai nayi har in gama karatu. Mahmud yace, munada lokaci ma, tunda sai an yi fiye da sati biyu da gama aikin hajji za'a koma hutu. Ka ga kuwa har zamuje mu dawo. Ismail yace, Allah ya kaimu lokacin, ai hutun ma ya qarato. Su Ismail sun dan tara kudi sakamakon wani aiki da sukayi tare da amincewar hukumar makarantarsu. Wadanasu masu hannu da shuni ne suka nemi makarantar ta taimaka musu da dalibai wadanda zasuyi musu rabon abincin sabil, da yake can qasar kowa so yake yi yaga an cinye nasa. Shine makarantar ta nemi dakiban ta tuntu6e su ko akwai wanda keson yi. Ismail da Mahmud suka shiga cikin sahun wadanda suke son yi. To anan ne suka samu kudi. Kamar yadda suka tsara hakan ce ta kasance, domin sunyi aikin hajji lfy sun gama lfy. sannan suka koma makaranta sukayi shirye-shiryensu suka nufi gida Nigeria. Abuja aka sauke su. Zukatansu fal da farin ciki mara misaltuwa. Ismail yace, gsky Gida daban ne, duk da cewa Abuja ba katsina bace, sai naji wani irin dadi, duk da cewa qasar dana baro tafi tawa komai, amma farin cikin na daban ne. "Ai Gida yayi." inji Mahmud.
[20/09 12:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa
Chapter 66 · 0% Book details