← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 89

Sashe 14

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya saurare ni, mina ta ce,in kin ga zai wuce gona da iri,ki mari fuskarsa,suka sa dariya ta ce,kin san ba na son taba jikin talakawa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (59)Amma zan tsirta mishi yawu,mina ta ce,haka yayi. yaya khalil dinki? oshshh!kin tabo rabin rayuwata,yana lafiya,ya ya faisal dinki?mina ta ce,sun gama hutunsu ya koma jiya, ta ci gaba da cewa,ina mamakin irin son da kike yi wa khalil dinki,kamar ba ki tsane shi ba,MIMI ta ce,kin san me mina?can dama ina son khalil tun lokacin da na soma ganin shi,na ja aji na ne kawai.mina ta ce,don ALLAH da gaske?MIMI ta ce,ALLAH kuwa,mina ta ce,kin iya jan aji kuwa to, shikenan in kunyi waya ki ce,ina gaida shi,MIMI ta ce, zai ji.bayan sun yi sallam ta shiga nazarin mau'du'in wulakancin da ya kamata ta dinga yiwa malami. Tara daidai lokacin cin abincin su na dare kenan,ta sauko da 'yar jar doguwar rigarta da kadan ta wuce gwiwarta,kamar kullum ta yi ado da gashin kanta,kowa ya hau kan teburin,tuni yara sun soma ci ma,sai da ta isa kusa da mahaifinta ta gaida shi, sannan ta dawo gurin zamanta ta kalli momi nafisa,mommy kin dawo?ta ce,ai ban dade ba MIMI,alhajin ya ce,ina kika je?ta ce,gidan hajiya adama na je,in duba masu takalma,ta dawo daga lngila.MIMI ta ce,kin samo mana?ta ce,duk kina da shigen su,ke kuma na san baki son duk wani abin ki ya zama gama gari.amma ta ce,wasu kayan na zuwa. MIMI ta ce,mommy ki bar shi ma kawai.takalma sun min yawa,akwai wadanda har yau ban sa su ba.na'ima ta ce,sis ina wadanda ki ka ce za ki ba ni?MIMI ta ce,ki tuna min da safe,ALLAH ya sa suyi miki,ke da katon kafar nan na ki,duka suka sa dariya. Alhaji ya ce,MIMI ke komai na ki daidai aka yi maki,kuma mai kyau,kalmar ta soki zuciyar momy nafisa ta ce,duk dai dan adam tara yake bai cika goma ba,ya ce,me ki ke nufi?ta maida abin wasa. ahaji na gani ne koyaushe sai ka wasa mamarka cikin dariya tayi maganar,shima cikin dariya ya ce,kin ga laifina kenan. Ya kalli MIMI,uwata ci abinci mana,ta zuba farfesun kaza ta soma ci tana yi,tana chating,bayan sun gama ne,alhajin ke ce ma MIMI zai yi bako ranar lahadi,ina so ayi masa tarba ta musamman, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (60)Nan zamu yi diner da shi,inda zai zo da iyalansa,sai na fi yin murna. mommy nafisa ta ce wane ne?ya ce alhaji akilu bala, ministan man fetur,MIMI ta kalli mahaifinta,dad,ka samu ganawa da shi kenan,ya ce,uwata ai yanzu mun zama abokai tamkar tare muka taso.shi yasa na gayyace shi don ya ga iyalaina,MIMI ta ce dad insha ALLAH za mu tarbe su.kiran hajiya sauda ya katse shi,ya daga bayan sun gaisa ta ce,ya binciki MIMI ko ta yi karatun,ya ce,ki daina damun kanki sauda,za ta yi,suka ci gaba da maganarsu,jin haka ne bayan ya gama wayar ya mike daga kujerar ya nufi dakin shi,MIMI ta ce.amma dad dama ina so muyi magana a kan malamin nan.lna son a tsaida lokacin da zan dauka,don koya min karatu,ya ce kamar ya ya?ta ce,dad yau karatun minti hudu ya yi min,ya ce, ok na gane,da safe zan neme shi mu yi magana.ta ce,ok dad ni ma zan fito da wuri don a yi komai a gaba na ya ce,to bari in shiga ciki,ta ce tam,dad ni ma zan koma sama ne sai da safe ya ce,ALLAH ya kaimu. lsmail yana tsaye bakin kofar falon,tunda ya danna baa bude ba,kusan minti biyu,ya sake dannawa sai lokacin aka bude,daga ganinta 'yar aiki ce,kuma ba musulma ba ce,ta ce kaine malam?ya ce eh,ni ne,ta ce, ka shigo,a nan cikin falo ya same su dukkan su,ya kalli alhaji cikin girmamawa ya gaida shi,sannan ya gaida mommy nafisa,ya ce gani alhaji,malam hamisu ya ce,kana nema na. Alhaji ya nuna masa kujera zaka iya zama a kan kujera,MIMI ta kalle shi da gefen ido,aa dad kar ka bashi damar zama a kan kujera,ya kalle ta,saboda me?ta ce,dad bai kai matsayin ba,shi mabukaci ne a gurin mu,ta kalle shi, zauna a kan kafet,ya danne zuciyarsa,babu damuwa in maganar ba mai tsawo ba ce zan iya tsayawa alhaji,alhajin ya ce,kar ka damu zauna a kan kafet din abin ya bawa lsmail mamaki,amma sai ya zauna saboda alhajin ne ya bukaci hakan.ransa ya ce, lallai dama an ce karshen zamani baiwa zata haifi uwar gijiyarta. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (61)Muryar alhajin ta katse shi,malam wanene ma sunanka?ya ce lsmail, alhaji ya amshe da cewa, yawwa lsmail,MIMI ce ta bukaci ka sa lokacin da za ku dinga yin karatu,da kuma tsawo lokacin da za ka dauka gurin yin karatun. lsmail ya ce hakan yana da kyau,wane lokaci ne ta tsaida?alhajin ya kalle ta, uwata wane lokacin ki kafi so ya koyar da ke?ta dan yatsina baki sannan ta kalli damfareren agogonsu a jikin bango kirar dubai,ta ce, kamar sha daya sai ya dinga zuwa don kada ya ce sai an aika a kira shi,ni bana son jira,nafi son a jira ni.lsmail ya yi dan murmushi a ransa ya ce,son kai, amma a fili sai ya ce,to mu tashi nawa?ta kalle shi sama da kasa.tsawon awa daya za mu yi gurin karatun.lsmail ya kalli alhaji, ba damuwa kullum zan zauna karfe shadaya mu tashi sha biyu kenan.ba lallai hakan ba ta katse shi. zaka iya zuwa misalin sha daya ya zama ban sauko ba,kai dai in ka zo shadaya daga lokacin dana sauko, daga saman na zo gurin karatu shine zaa dauki awa daya,lsmail yayi murmushin takaici,babu laifi matsawar lokacin sallar azahar ba zai shigo ba,alhaji ya ce,sai batun albashi,hajiya ta ce min ka ce duk abinda aka baka,lsmail ya ce haka ne. alhaji ya ce,aa zai fi kyau ka fada,lsmail ya ce,alhaji me karantarwa ladan shi yana gurin ALLAH,abinda zaa ba mu kyautatawa ce,alhaji ya ce,to da kana samu dubu hamsin a wata?lsmail ya ce,aa gaskiya basu kai ba,ya ce,to zan dinga baka dari. da sauri lsmail ya kalle shi, sai MIMI ta fashe da dariya kudin sayan kayan kwalliya na kenan fa,ta kalli na'ima, dubi yanda ya rude,ashe ni ma zan iya biyan shi da kaina,alhaji ya ce,ka iya tafiya,sai lokacin ya yi.lsmail ya ce to,tare da mikewa, ransa bace ya fita,lallai yarinyar nan 'yar wulakanci ce,anya kuwa zai jure?. Alhaji ya kalli MIMI,uwata ki daina irin wannan a gaban mutum.ta kalle shi,dad wallahi duk duniya ba wanda na tsana kamar shi,na'ima ta ce,shine to zai dinga yi miki karatu?ta ce, eh,amma na tsane shi,ta ce to mu fa karatun mu yaushe ne sis? [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (62)MIMI ta ce,ku kan sai karshen sati.alhajin ya mike cikin murmushi bari na fita,mommy nafisa wadda kallo ya daukar mata hankali,ta mike don yi masa rakiya,ya shafi kumatun MIMI ki yi min addua uwata, ta ce,sai ka dawo dad ALLAH ya baka saa,na'ima ta ce,sai ka dawo dad,ya ce,yawwa na'ima. mommy nafisa ta zauna a kan kujerar madubi tana kallon na'ima wadda ta fada kan gado ta yi ruf da ciki,ta ce,na'ima taso ki ji,ki taso mana na'imata,ta dago fuskarta da jurwayen hawaye,ta ce,mommy dad ba ya so na,komai sis MIMI, ni kam na gaji.nafisa ta ce. amma me nike fada miki kullum?ba ke kadai ba ce yake yima haka,ku duka ne, amma nayi miki alkawarin sai ya so ki fiye da MIMI. na'ima ta soma kuka,na gaji da jin haka mommy,sai yaushe ne haka zata faru?mommy nafisa ta tashi ta koma bakin gado ta zauna,ta janyo na'ima zuwa jikinta,kar ki damu,mu bi a hankali da sannu za ki zama 'yar gaban goshi. akwai shirin da na jima ina shiryawa,na'ima ta kalle ta da gaske?mommy nafisa ta ce,kar ki yi shakka.ta share hawayanta,shikenan zan so in yi kamar abinda take yi,ko kuma fiye suka sa dariya. Shadaya daidai lsmaik ya shiga cikin falon,bayan me aikin ta zo ta bude,na'ima ce kadai a falo tana kallon fim din india,ya ce,ki fada mata nazo,ta yi mishi kallon banza,ba ta ce, in kazo ka jira ta bane?ga falon da kuka zauna can a jiya,zaka iya jiranta a ciki.ya nufi falon ransa bace,anya rayuwar gidan nan zata yiwun masa?mintinsa goma shabiyu,sannan ya soma da jin kamshin turaren ta,gabansa ya fadi,ta ja kofar wadda ta kasance ta gilashi,kallo daya ta yi masa yana sanye da jallabiyya fara sal,ya yi kyau matuka,ta tabe baki,ta zauna shima ya kalle ta kamar koyaushe shigarta babu tsari,ya kauda kai,ya ce,ta ina za mu fara?ta daga wayarta ta sa a kunne,hello dear ka tashi lafiya?ta dai yi jim,ok zamu yi waya anjima,yanzu ina tare da talakan nan ne,sai kuma tasa dariya,khalil kenan sai anjima din.ta kalli lsmail me ka ke fada?ya ce,ta ina zamu fara? [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (63)Yanda ya kafa mata ido hadi da hade ranshi,sai ta ji yayi mata kwarjini,ba za ta iya kallon shi ba,yayi da zata yi masa rashin mutunci,ta kauda idanunta gefe,ko ta ina ka fara mana,ka tsare ni da idanunka,yayi dan murmushin takaici,ya ce,to zamu fara daga huruful hija'iyya,alifun kenan.ta dube shi da sauri tun ina 'yar nursery na yi wannan, yanzun kam university nike, don haka sai ka koya min karatun da yayi daidai da ajina,lsmail ya ce,zan so in baki shawara,dul me neman ilimi ko bana addini ba zai fi kyau ya zama me biyayya da saukar da kai, girman kai ba ya kai mutum ga gaci. ta daga mishi hannu,baa dauke ka don ka bani shawara ba,an kawo ka ne kurum ka koya min karatu. ya ce,to bari mu fara daga fatiha sai mu shiga bakara zuwa kasa ko?ta tabe baki,ina jin ka,ya ce,zan karanta miki kamar sau uku,sai ke ma kiyi.tunda ya soma karatun danna wayarta ma take yi,ya gama ya dube ta,yanzu sai ki karanto fatihar in ji ke ma daga nan sai in dora miki daga bakara aya biyar-biyar zamu dinga yi duk kwana biyu sau biyu a sati sauran kwanakin kuma sai mu saka fikihu,hadisi da tauhidi.ta ce,me kake fada ne?ni fa duk ban jika ba,ya ce,karatun na ce kiyi,ta harare shi,yanzu fa ka ce, sai ka fara sannan zanyi ya daga murya,kina nufin baki ji karatun da nayi ba?ta ce,shine gaskiya,da kayi ai da naji,ya rufe kur'anin cikin takaici,ya zuba ma kafet din kasan idanu, shi kam ya gaji.ta katse mashi tunani,a
Chapter 14 · 0% Book details