← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 89

Sashe 34

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hankalin isma’il yayi mutukar tashi lokacin da aka
juyada motar domin gaba daya khalil yadagargaje
har kwanyarsa tanzuba juyawa yayi yana salati kmar
yadda sauran sukeyi bai iya sake kallon grinba har
aka faito da mimi sai da aka zuba su amota sannan
mahmud yazoya kama kafadun isma’il yana cewa
karka damu isma’il mutafi asibiti sun nufi motar
kenan mahmud ya hango wani daga cikin masu
kawo daukin ya kunkuci dan akwatin mimi dajakar
khalil ya gane akwatin mimi ne sbd a gabansa tafito
lkacin dazata tafi dasauri mahmud yanufishi yana
cewa kaiba ni kayan nan konakane?

Yace ammm dama inace za aje gurin yansadane
mahmud yace nanne hanyarguri yansandana,a gurin
sojoji zaaje ba yan sandaba irinku ne masu yin sada
in anyi hadariko? Mutumin ya miko akwatin tare da
cewa bani kadi bane yanuna wani gawanda yadauki
waya chan! mahmud ya kwada masa kira, kai zonan
bani wayar hannunka shi ma babu kunya yamiko ta
muhmud yace kuji tsoro allah batare da ya jira jin ta
bakinsu yajuya ya nufi motar hamisu ya zuba kayan
sannan ya shiga yana cewa “muje hamisu!” kuwwar
motar yansanda itace ta tsaidasu,suka iso.
Sannan suka nufi asibitin tare. Cikin sauri aka amshi
su aka yi emergency dasu, musamman dayake
angansu da yan sanda.isma’il yana tsaye cikin
matsanancin hali.addu’o’in da isma’il yake yine
sukasa jikinsa ya daina bari saidai kallo daya zakayi
masa ka san cewa yana cikintashin hankali.daya daga
cikin yansandan ya nufosu.ya kalli mahmud waiyaya
abin yafarune? Mahmud yakalli dan sandan gudu
yakeyi sosai,dan sandan yace naji lokacin da mukazo
gurin,wani yana cewa,koyasha wani abune? Sai wani
ne acikin motar yace,irin yaran masu kudin nan ne
suke dauko mota suzo sunamugun godu
atiti.mahmud yce, yarinyar da suke tare matar
wannance, yanuna isma’il.jiya aka daura musu aure
shne yazo ya dauketa zasu gudu, shine fawannan
hadarin yafaru.dan sandan yakalli isma’il batason
kane?
Lsma’il yace, babanta ne yahada nida ita ranka
yadade baxan iya saniba.kafin dan sandan
yasakecewa wani abu,sai ga likitan da sauri.ya ce,
kune yan uwan masu hadarin nanko? dasuri
mahmud ya taso,mune likita.likitan yace kun san
cewa namijin yarasu ko? duk da cewa dama suna
tunanin cewa ya mutu,saida suka dauki kabbara.
Sannan suka ce, allh yajikansa da gafara.isma’il
yakama hannun likitan yana fadin”doctoh itafa?
“yace,kar kadamu,munayin iyak kokarinmu.ta samu
karaya guda biyu a kafarta, da kuma guda daya a
hannu.sannan munaso ne ta farfado don mu sani ko
ta samu wata matsala awani guri daga cikin kanta,
saboda ta zubar da jini sosai.yaba shi wata takarda,
kaje gurin sai da magani,gashi can zasu baka
wadannan,yanxun kakawo mana.
Isma’il yace to,sannan ya kalli mahmud,gashi kudin
suna gida.mahmud yace,to muje kadauko mana.
Daga nan sai mutan gadan su san halinda ake
ciki.kafin su wuce saida suka dauko jakar khalil da
wayarsa suka ba wa yan sandan.don tasa aka gani ba
agata mimi ba. hamisu yajasu, kai tsaye gidan
suka koma, inda isma’il ya aje jakar mimi,sannan ya
dauko kudinsa duka na aikinsa da alhaji ya bashi.

Ya kulle dakin ,sannan yashiga cikin gdan yasanar da
su inna abin daya faru.bai tsaya amsa tambayoyin
dasu innar sukeyi masa akan wai yaya akayi haka,ko
unguwa suka fita?ya fita suka koma asibiti suka sai
magungunan. lokacin ne ma dansandan yake fada
musu cewa,yakira iyayan khalil.sunyi amfani da
wayar khalil din ne. yakuma sanar dasu cewa,dansu
yayi hatsari, kuma ya rasu.suzo su dauki
gawarsa.isma’il ya girgiza kai don jinjina yadda
mahaifan khalil zasuji wannan lamari.alhaji yakira
hamisu don yaji ko ya kosa kaduna.
Zai sa shiya amsar masa sako gurin wani abokinsa na
maganin diabetes ne na hausa da abokin nasa yace
xaiba shi,don shima yaji dadinsa. Hamisu
yace,matsala aka samu alhaji,ko katsina ban baroba
har yanxun.alhaji ya ce, meya faru kuma? Hamisu ya
sanar da shi komai. ran alhaji ya bace mutuka dajin
cewa mimi tasake yankurin guduwa.cikin bacin rai
yace ma hamisu,”kataho kawai!”yace,alhaji yarinyar
nan tana cikin mawuyacin hali sosai,don duk
akakkarye taka.alhaji yace,hamisu kabarsu kawar.
Babu abin da zan iya yi mata, kaima bbu abin daxaka
iyayi mata,don haka kayi abin da nace kawai.yace,
shikenan,alhaji zan taho yanxun.”yace,” to, kana kusa
dashi malam isma’il din ne? Yace, “eh ina kusa
dashi.yace,toka bashi!”ya mikama isma’il wayar.sun
gaisa,alhji yace,”ashe abinda yafaru kenan?”isma’il
yace kwarai kuwa alhji.yace Allh yakyauta.”cikin
tashin hankali isma’il y2e,alhji kayi mata duk abinda
takeso,zata iya rasa ranta,domin shi khalil din ya
rasuma.”duk da alhajin ya jinjina batun mutuwar
khalil a ransa,amma afili sai yace,”karka damu
malam isma’il,tunda yanxun ta karye ai bazata sake
yankurin guduwa ba.ka ba hamisu wayar.”isma’il
yace alhji kuzo ku taimaka mata.”alhji yace,isma’il
inayi maka jajen abin da yafaru da iyalinka,amma
kayi hakuri ba zan iya taimaka mata ba.kaba hamisu
wayar!”cikin rawar hannu,isma’il ya mika ma hamisu
wayar.
(Za mu ci gaba)….
(Tare da Halima K Mashi)
Canjin rayuwa
A sanyaye ya koma ya jingina da bango. Sai
lokacinne ma ya tuna ya kamata ya sanar da hajiya
sauda. Ya kalli mahmud, “ya kamata in sanar da
mahaifiyar yarinyarnan ko? ” Mahmud yace, “tabbas
ya kamata ka sanar da ita” kan benci ya zauna,
sannan ya soma kiran layinta. Bata jima ba ta daga. A
sanyaye ya gaishe ta. Ita kam yanayin muryarsa tasa
ta faduwar gaba. Tace, Ismail ta sake guduwa ne?
Yace Eh hajiya, amma sunyi hatsari akan hanyar su
ta guduwa. Yanxu haka muna asibiti. Tace, Inna lillahi

wa inna ilaihi raji’un! Da sauqi dai ko? Yayi ajiyar
zuciya, to da sauqin dai za’ace amma shi ya rasu… Ya
rasu?? Ta katse shi. Yace tabbas, ita dai sunce suna
jira ta farfado. In har ta farka a cikin hayyacinta, to
suna ganin karayar data samu ce guda biyu a kafarta
daya kuma a hannunta sune kawai matsalar, cikin
kuka hajiya tace, wane asibitin kuke? Yace babbab
asibiti, tace shikenan bari in Kira alhaji zanzo ynxu,.
Kafin ya amsa da cewa Alhaji ya kirashi, har ta kashe
wayar.
Hajiya ta soma kuka. Su hasana suka fito da sauri
suna tambayar ta lafiya? Tace musu mimi ce sukayi
hadari. Nan suma suka shiga damuwa. Tace bari in
kira Alhaji Muje mu ganta. Ta shiga kiran layin
Alhajin, tana soma ringing ya daga, Tace cikin kuka
Alhaji kaji abinda ya faru? Yace naji. Ko ba hadarin
su mimi ba? Tace ashe ka sani. To dama zamu tafi da
yara ne. Ga mamakin ta sai taji yace, ban amince ba,
yaci gaba da cewa, ki Fadama duk sauran ‘ya’yanki
banyi wa kowa izinin zuwa duba ta ba, matsawar na
isa. Mamaki ya cika hajiya sauda, tace sbd me Alhaji?
Yace cikin fushi, ban isa ince ga abinda nakeso ba
saina fadi dalilina kenan ko? Tace kayi haquri. Yace to
na saka Allah ya isa! Daga kanki har sauran da suke
qarqashi na matsawar kuka taka gurinta! Ya kashe
wayarsa.
Shi kansa Alhajin cikin damuwa yake, amma ya tsara
ma kansa cewa, dole ya haqura don wani dalili nasa,
sannan yasan cewa, abin Ya ta6a zuciyar hajiya
sauda, sbd hk ya yanke Shawarar sake kiranta. Ta
daga, har lokacin kuka take, a nata ganin bai dace
abar mimi cikin wannan halin ba. Yace amma hajiya
don Allah kiyi haquri, akwai dalilin da yasa dole sai
nayi hakan.
Zan yi miki bayani daga baya. Sannan ina mai
jaddada miki ban haquri na, ki taimaka kuyimin
wannan. Nasan zaki iya saka ‘ya’yanki su dangana da
zuwa gurin mimi. Kuma daga baya zaki daina jin zafi
na in kinji dalilina. Kin fahimceni ? Tayi ajiyar zuciya,
shikenan zanyi duk yadda kk so. Shima ya sauke tasa
ajiyar zuciyar. Na gode, Allah yayi miki albarka, ya
saka miki da aljannah. Sai nazo. Tace to Allah ya
kawo ka lfy.
Ta kalli su usaina tace, inaso kubar maganar nan
anan, ko su yayanku abba, bana son su sani. Hasana
tace sbd me hajiya? Tace sbd hk dadynku ya buqata.
Kuma banison ku damu da cewa sai kun san dalili.
Zamu dinga jinya lafiyarta daga bakin mijinta. Suka
kalli juna da ido, suka mamakin zancen mahaifiyar
su, sannan suka miqe suka shiga dakinsu. Ita kuma
sai ta daga waya ta kira layin Ismail. Cikin sauri tare
da yin sallama, ya amsa a sanyaye, yace kun iso ne?
Chapter 34 · 0% Book details