← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 89

Sashe 52

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan
mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi
gefe, yana sheqa varcinsa.
Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi
gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba.
Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta
samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon
babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin
kashewa, ynxun dai fada min me za’a yi? Hajiya Nana
tace, tsabar katan qamshi za’a hada masu fizgar
hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba.
Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan
Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka
turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta
bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce.
Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza,
wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya.
“kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne?
Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace,
ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi.
Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana
bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido
kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da
batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan
suka nufi gidan Na’ima.
Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm.
Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume
momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa
bayan sun zauna a bakin gadon Na’imar. Tana fadin
momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan
ba. Hajiya Nana tace, “ke da Allah natsu! Na’ima ta
tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata
daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki.Nan
ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna
kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk
ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen
da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya.
Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya
kafin mu kafu a cikin gidajenmu.
Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da
kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu
sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka
karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata
shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace,
kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du,
yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija
mana dariyar ‘yan baqin ciki. Da ma gashi jikin
dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda
aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da
hankali, suka fita, suka tafi.
Sha biyu da kusan minti arba’in na dare lokacin ne
Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga

bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa.
Na’ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da
jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa
kiranta. “Na’ima in na shigo sai na ci miki mutunci.
Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da
kallo tun daga qasa zuwa sama. ‘yar mitsilar rigar
varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa
fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi.
Cikin wata kidima ya rungume Na’ima a zaton ta
abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi.
Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta
mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin
dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni.
Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna
qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na’ima tana kukan
takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan
mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi
gefe, yana sheqa varcinsa, amma yana ambatar
sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya
fadi gefe, yana sheqa varcinsa.
Na’ima tayi kuka, iya kuka cikin daren kafin varci yayi
gaba da ita. Qarfe takwas ya farka. Halin daya ganshi
ciki ya sashi kallon gefensa. Na’ima ya gani kwance
cikin irin yanayin daya samu kansa. Ya soma tunanin
da yaushe har tazo masa daki akai hakan? Ya dai iya
tuno jiya sun samu matsala da Jennifer. Yarinyar
daya kawo ta Abuja da kansa ya kama mata gida tana
zamansa, ynxun kuma sai ta dinga munafuntarsa.
Jiya yaje mata zuwan bazata sai ya sameta ta kawo
wani gidan. Yayi mata magana tana fada masa cewa,
itafa ba matarsa bace bare ya dinga yi mata dokoki.
Yayi mata duka kafin ya baro gurin ta ya nufi club
dinsu inda suke hadewa da abokansa suna shayeshayensu. Ya fada musu halin da yake ciki, nan suka
bashi shawarar cewa, yasha mayensa ya manta da
ita, ya daina zuwa ta gani in akwai wanda zai mata
kwatankwacin abinda yake mata. Sha yayi sosai, don
bai ta6a sha irin haka ba. Ko iyayensa basu san yana
sha ba, domin baya sha da yawa.
Ya kasa komai don haka suka kawoshi gida. Tuna
hakan yasa shi gane cewa, maye ne ya suranta masa
Na’ima a matsayin Mimi. Tsaki yaja sannan yasa
hannu ya daddaka mata duka. Firgigit ta farka tana
kallonsa, fuskarsa daure. Yace, tashi ki fita! Tace
dama kai ka kawoni bani nazo ba. Ta soma kuka,
yace ban tambayeki wani dogon zance ba. Nace dai
ki fita. Na’ima ta saka rigar varcinta ta fita da kuka. Ya
jima shiru yana takaicin faruwar hakan Tsakanin su,
don bai tsara zaiyi hakan da ita ba. Amma sai ya
miqe ya nufi bandakinsa.
Na’ima ma bayan tayi wanka da sallah, ta koma ta

zauna tanata tunanin yadda mijinta yake mutuwar
son mimi. Kai ita da ta sani, da bata kawo kanta gurin
son maso wani ba. Can ta miqe ta nufi kicin, yauma
da kanta ta girka abinda zataci kifi ta gasa, irin gashin
da Mimi kansa ayi mata. Na’ima ta dan iya girki,
domin ko a gidansu tana shiga kicin gurin masu yi
musu girki jefi-jefi.
Ta gasa bread dinta, zata fito shi kuma zai shigo kicin
din, ya kalli tiren hannunta, “bani kiyi wani! Bata
musa ba, ta miqa masa don tanason su riqa ‘yar
hulda ko yaya. Ta koma ta hado wani abin karin.
Bayan ta karya ne ta shiga turare gidan da turarukan
da aka kawo mata. “Yayi qamshi. Ya fada, duk da ba
cikin walwala yayi maganar ba. Taji dadi, kuma taji
mamaki. Don haka bayan fitarsa, sai ta dauko sauran
abubuwan ta kama amfani dasu.
A waya Abbas ya kira Usman, yana bashi labarin
abinda ya faru a jiya. Usman yace, kai sakarai me
nace maka? Ai na fada maka kawai ka more
quruciyar Yarinyar kace a’a, to ynxun don ja nuna
ma Jennifer kurenta kawai, ka share ta kaci
amarcinka. Abbas yace, banason Yarinyar tayi
tunanin cewa, ina sonta ne. Usman yace, ai ba wai
zaka sakar mata fuska bane sosai. Ka gane? Abbas
yace, shikenan zan kwatanta. Tun daga ranar Na’ima
tadan samu sauqin mijinta. Zai sata ta dafa masa
abinci, kuma zai kirata shimfidarsa. Amma ba wata
soyayya, ko kulawa, ko hira ko sakin fuska.
Abin da ta lura amfaninta kenan tayi masa girki,
sannan yayi buqatarsa. Wani dare ya kirata a waya
taje samansa. Ta sameshi a falo tace gani. Yace ki
shiga mana. Kin tsayamin akai, sai kace wani sa’anki.
Ranta ya sosu, tace, wai kai kana bani mamaki. Kana
nema a gurina amma kayi ta dauremin fuska, kana
fadamin abinda kk so. Yace kar ki kawomin raini. Ki
wuce muje. Tace, ni varci nakeji, ta juya. Nan take ya
kamota, saida ya mammareta, sannan yayi abinda
yake so anan falon, ya kuma koreta zuwa dakinta.
Zahiri baya sonta, amma abubuwan da take sha, da
wanda take qamsasa jikinta suke fizgarsa gareta. Irin
Rayuwar da Na’ima ke ciki kenan. Gashi danginsa sun
tsane ta, musamman uwarsa wadda tace, Na’ima ta
bada ita a gaban Qawayen ta. Zainabu kuwa
tana can gidansu, saiga Alhaji ya diro da la’asar
sakaliya. Yayi sallama dz innar su Zainabu. Yau kam
fuska daure ta fita, da nufin bala’i tare da ita. Sai dai
shima tana kallon sa tasan cewa da hakan yazo,
kuma in ba sa’a bama shi ya dama ta ya shanye.
Kafin tayi magana ya riga ta.
Nazo daukar Zainabu ne. Ta lailayo ashar ta maka,
sannan tace, Zainabu ba zata koma ba, sai ya sauke
dubu ashirin da hudu na asibiti. Yace, tunda dai
Chapter 52 · 0% Book details