← Book details Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 89

Sashe 50

Canjin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

qalau. Dayan yace, kawai inna ki fada masa gsky.
Kanaji ko malam. Wannan matar tun ranar da suka
kawo ‘yarsu aka bata gado, bata biya kudin gadon ba,
sannan akwai cikon kudin magani, wanda zata bada
ciko, amma taqi, kullum sai tace, sai alhaji yazo.
Yau likita ya ba sallama kurum, sai dai wannan
abokin aikin nawa ya ganta a bakin Gate zasu hau
tasi. Kaga mu taja mana kenan, ace mu muka cinye
kudin. Ismail yace, nawa ne kudin? Inna cikin kunya
tace, umm ai da ma ka barshi kawai, Alhajin dama
yayi tafiya ne shiyasa. Mutumin yace, inna ki bari
kurum a biya muku. Ba wani Alhaji, kullum kina
zaizo, amma shiru. Ya kalli Ismail, dubu biyar. In
kuma za’a basu ragowar maganinsu, dubu shida da
dari uku da saba’in. Ismail ya saka hannu cikin
aljihun wandonsa ya ciro ‘yan dubu dubu ya miqa
musu dubu shida. Sannan ya ce, jiya canji na nawa
na bari anan?
Dayan yace dari bakwai da hamsin. Ismail yace, ku
cire cikon ku bani sauran canjin. Kanta a qasa tace,
an gode Ismail. Ta juya zata tafi, suka ce, ki tsaya
mana ki amshi sauran magungunan da kuma
takardar shedar biya. Ismail ya amshi canjin sa,
sannan ya kalli innar Zainabu, “Allah ya qara sauqi”
bai jira amsarta ba, ya wuce. Ita kuwa dama kunya ta
hana ta amsawa. Zainabu ta nufo gurin, sbd itama
tasa baki, ko zasu yarda za’a kawo musu daga baya.
Sam basuga juna ba, saida suka zo daf. Itace ta soma
ganinsa. Tsayuwar da tayi ne yasa shi ganinta.
Tayi sauri ta juya baya. Ismail ya runtse ido ya bude.
Gabansa yaci gaba da faduwa. Shima yayi saurin
dauke idanunsa daga kallon bayanta. Da qyar yace,
“yaya jikinki? Tace, da sauqi, cikin rawar murya dake
dauke da kuka tayi magana. Yaya taka mai jikin? Ya
dubi inda take, a ransa yace, ashe taji. A fili yace ta
samu sauqi. Yaja qafafunsa wadanda sukayi masa
nauyi yace, sai anjima. Ta bishi da kallo bayan ya
wuce. Sam ta kasa ko motsi, sai kuka har innarta ta
iso tana tambayarta lafiya? Zainabu tace, an cuce ni.
Dajin haka innar tasan Zainabu taga Ismail. Cikin
borin kunya tace, “kina ta an cuce ki.
Matar mutum ai kabarinsa ko? Ki barshi a qaddara.
Zaizo ya sameni shi kuma Alhajin. Ya sanni, ni walki
ce ina daidai da qugun kowa. Zainabu dai bata tanka
ba, sai ta fita abinta. Tunda suka koma gida ko
yaushe Zainabu tana cikin qunci da kuka.
Musamman da innarta ta fada mata cewa, Ismail
dinne ya biya kudin gado. Innarta tanason Alhajin
yazo ya biya kudin da suka kashe, indai yanason
zama da Zainabu. Ita kuwa Zainabu ba haka nata
tunanin yake ba. Jiran Alhajin takeyi. Ko nawa zai
kashe, batajin cewa, zata koma gidan Alhajin.

Ismail ya jima zaune akan katifarsa kafin ya tashi ya
dauki bokitinsa ya nufi cikin gidan, suna ta nasu
harkoki. Yayi sallama suka amsa sannan ya gaidasu,
ya nufi dakin Inna, tana ta gyangyadi, ya gaida ta. Ta
tambayi mai jiki, yace, da sauqi, tace kai dama ashe
Yarinyar nan ba sonka takeyi ba? Ismail yayi
murmushi, tare da cewa ai wannan ya wuce Inna. Ya
miqe ya nufi bandaki. Tace, haka dai kk kullum
ba’ajin cikinka. Jeka can ka qarata. Bayan ya fito ne
yaga wata yayarsu tazo ya gaida ita, zai wuce, fatu
tace, kin masa jaje kuwa?
Yaya shafa tace, meya faru dashi? Fatu ta tuntsire da
dariya. “huce haushi akayi masa da mace. Ashe bata
sonsa ta gudu, sai kuma tayi hadari a hanya. Shafa ta
kalli Ismail wanda shi yana daf da zaure tace, to ashe
haka akayi Ismail? To Allah ya kyauta. Yace, Ameen
tare da shigewa zauren. Ya gama shirinsa tsaf cikin
yadi mai kalar sararin samaniya marar nauyi. Ya saka
hula sannan ya feshe jikinsa da turarukansa na
musamman da yake hadawa a gurin masu saida
turaruka sannan ya fita ya nufi gidansu Mahmud don
amsa kiran malam Aminu.
Da Mahmud ya soma haduwa, sai dai irin fara’ar da
ya gani a fuskar Mahmud din ta bashi mamaki. Yace,
malam ko anyi maka baiko da rabi’atu ne? Mahmud
yace, qila da hakan ne zaiyi wuya ka gane a fuskata.
Gara ma inda ranar daurin auren ce. Ismail ya
dafashi, to sanar dani mana game da farin cikinnan
naka? Mahmud ya kama hannun Ismail. “Zomuje kaji
daga bakin malam. Tunda na iya jure daren jiya dana
samu labarin, na jure safiyar yau, to kuwa zan jure
ynxun muje kaji da kanka. Na yafe goron albishir
din. Cike da fara’a suka gaisa da malam yace, malam
Ismail yaya mai jiki?
Jiki da sauqi Alhmdlh. Malam yace, masha Allahu. Ka
samu labari daga bakin dan uwanka ko? Cikin
zaquwa yace, bai fadamun ba malam. Yace, inji daga
gareka. “malam ya fadada fara’arsa, sannan ya kalli
Mahmud dake zaune gefe, yana murmushi, ya maido
da kallonsa ga Ismail, “Scholarship dinku ya samu.
Shekaran jiya malam mukktar yazo ya sameni da
batun. Don haka sai ku soma shirye-shirye, nan da
wata daya Matsalarmu kudin da zakuyi amfani dashi.
Ismail yayi mutuwar zaune, jinsa yake tamkar a
mafarki. Wai malam madina yake nufi ko zariya? Da
darsuwar wannan zargin, sai ya kalli malam. “Malam
wai madina dinne?
Malam yayi dariya, ka samu nutsuwa Ismail, madina
ce zaku tafi, kaida dan uwanka. Saiku soma shiri, tare
kuma da neman kudin da zakuyi ‘yan abubuwan
daya kamata. Sam Ismael baisan lokacin daya
rungume malam ba. Sunyi murna sosai harda

sujjada don nuna godia ga ubangiji. Ismail ya soma
tunanin wa zai soma fada mawa? Duk lokacin da
wani abin farin ciki ko baqin ciki ya sameshi, sai ya
tuna mahaifinsa, ‘yar qwalla ta taru a cikin idanunsa,
amma sai ya daure ya cije. Yace musu bari yaje ya
fadawa yaya Amina da mutan gidansu. Mahmud
yace, to sai ya shigo anjima, a gaida ‘yar amana.
Ismail yayi murmushi, “zata ji.”
Sam ya manta da Damuwar Zainabu daya baro
asibiti da ita. Saida ya idar da sallar azahar sannan ya
nufi cikin asibitin, zuciyar sa fal da murna. Yana shiga
yaya Amina tana nunke sallaya, ta idar da sallah.
Ismail yana shigowa sai ya rungume ta, ta tsorata
sbd bata ta6a ganin haka ba. Ya sake ta yana dariya,
“naga kin tsorata?” Tace ai dole Ismail ban ta6a ganin
haka ba.
Yace, zamu tafi karatu madina, nida Mahmud. Yaya
Amina ta sake rungume shi, cikin tsananin murna
tace, Allah da uwana? Allah mun gode maka. Sai
kuma ga hawaye suna zubar mata. Ya ciro hankici
yana share mata hawayen. Ba ason kuka a cikin
murna yaya, cewa zakiyi “Alhmdlhi llazi bini’imatihi
tatimmussalihat. Ta maimaita abinda ya fada, sannan
sukayi murmushi. Ta kalli mimi. Wadda take
kallonsu, kinji ko khadija? Mimi tace, Allah yasa
alkhairi. Ismail yace, Ameen.
Sannan suka zazzauna yaya tace, to ya batun
karatunka na nan? Yace yaya ai kuma ba wannan
zancen. Tunanina ina zamu samu kudi sbd tafiyata
da kuma sauran hidimomi. Yaya tadan yi shiru, can
tace “to ko daura zamuje wajen su kawu a saida
gonarmu ta gurin mamarmu? Ismail a’a yaya gonar
fa ba ta ni kadai bace, gaki kuma kema mai buqata
ce. Yaya tace, ko ni na siya da kudina bazan sadaukar
maka da ita ba, balle gadonta mukayi. Haba dan
uwana abin duniya fa na duniya ne. Ya kama
hannunta “nagode yaya, Allah ya kaini lokacin da
zanga nayi miki fiye da abinda kikai min.
Tace Ameen Ismail, in jikin khadija ya qara sauqi sai
muje dauran ko? Yace to hakan za’a yi. Dama basu
san komai game da auren nan nawa ba. Sai kuma sai
kuma ya kalli mimi, tunda ba wai lallai auren ya dore
ba, mubarsu kawai. Yaya ta gane yana fadin hakane
don kar mimi taci gaba da rikicinta. Kafin kwana
goma labarin tafiyar su Ismail ya zaga dukkan ‘yan
uwa da abokan arziki, sai murna akeyi wa Ismail da
Mahmud. Mimi kuwa jiki ya soma sauqi, gashi
tanacin abinci amma fa rabin abincinta kifi ne.
Hajiya sauda ta shiga damuwa sakamakon rashin
samun Ismail a wayarsa. Ynxun ma da take zaune
saida ta dauko wayarta da zummar ta sake gwadawa,
kamar wasa sai layin ya shiga. Cikin Jindadi tace,
Chapter 50 · 0% Book details