← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 47

Sashe 8

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kumafa hakane usman ya fada yana kallon ma,u zuwa can yace asmau kafin mu isa gida nasameki acan, idan har kika bari na rigaki isa gida kashinki ya bushe"

Arude tace yaya amota kake fa ?

Muryan bakon taji yace ke!!, dakaran ya yabiyoki bakiyi gudu ba?

Idonshi nakan jaridan dan haka ta murguda baki tace nayi?

Toh irinshi zakiyi, idan kuma kikabari har mukaje gida bakizo ba, zan kirga mintocin da kika kara duk minti 5 yana da bulala 15, be jira mezatace ba yace usman muje"

Figar motan sukayi kankace me suyi nisa sai kellin motar take hangowa"

Cije lebe tayi sannan tace lallai abokin yayan nan bakin mugune har yafi yaya mugunta idan ba samun guri ba daga zuwanka bakunta zakace zaka dake ni ko gidan ma bakaje ba?

Cafdin ta fada afili wlh bazan tsaya ka dakeni ba idan ko ya dakeni da abba zan hada su"

Juyawa tayi ta fara tafiya lokacin data shiga gida ana kiran mangariba"

Aharaban gidan taci karo dasu zasu masallaci"

Abokin yaya taga ya kalli agogon dake daure ahannu shi sannan yaci gaba da tafiya batare daya kalleta ba"

Koda ta shiga gida mama bata nuna fushinta ba"

Dakinta ta wuce tayi wanka sannan ta dauro alwala Riga da siket ta saka na atamfa sannan ta saka babban hijjabi. ta tada sallah"

Bayan ta idar ta wuce dakin mama"

Tana shiga mamata tace ke kuma garinyaya kare ya tareki kinason kizama ballagaza ko?

Shiru tayi dan haka mama taja tsaki sannan tace wuce Ki dauki abinci ki kai falon abban ku"

Bata kawo komai a xuciyarta ba, ganinta abba zata ajewa abinci kafin ya shigo dan haka da karfinta ta shiga falon"

Turus tayi lokacin da taga abokin yaya zaune akan doguwan kujera ya miki kafa fuwan shi"

Cikin sauri ta aje abincin ta juya zata fita taji muryan yaya usman yace"

Ke zonan?

Dawowa tayi ta tsaya tana kokarin matso hawaye".

Jitayi ya sake cewa *JAMAL* gata"

Kaman jira yake ya juyo ya sakko da kafan shi kasa sannan yace kina da bulala 30"

Kallon su kawai take dan ita gani take wasa suke zuwa can taga wadda yaya usman ya kira da suna *JAMAL* ya mike sannan ya saka hannu a aljihun gaban gaban wandon shi daidai guiwa ya ciro wata zafgegiyar bulala sannan yace daga zanin Ki.....

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
.鈥�
[22:50, 12/19/2017] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挆馃挐馃挐馃挆
鈥�*BUGUN ZUCIYA*鈥�
( 鈥婬eartbeat鈥�)

馃挀馃挐馃挆
馃挆

馃挀馃挐馃挆
鈥婤y鈥�
馃挆
鈥嬧€�*Fadeela Lamido*

*@AM拢拢NCI WRITER'S ASSOCIATION馃*

1鈨�7鈨� to 1鈨�8鈨�

馃摍 Na daga zani ? Lailai wannan dan rainin hankali ne aiko yaya betaba cewa na daga zanina ba, bare wani katon banza"

Muryan yaya usman taji yana cewa wai bada ke ake mgn ba?

Karya murya tayi sannan tace ai ba zani bane siket ne"

Abokin yaya taji yace koma menene ki dageshi sama"

Cikin sauri ta kalleshi saidai shi ba ita yake kallo ba"

Mikewa yaya usman yayi ya fice dan haka Asmau taita zubawa abokin shi harara"

Zuwa can taga ya fara tahowa yanazuwa daidai inda take yasa kafa ya kwasheta"

Ganinta kawai tayi akasa cikin sauri ta fara kokarin mikewa amma ina jitayi kwankwasonta ya rike"

Daker ta iya dago kanta ta kalleshi daidai lokacin daya dago hannu ya sauke mata mari"

Innalillahi wa inna ilaihir rajun'un ta fada da karfin saboda zafin marin ya shigeta, zaki daga ko bazaki dagaba?

Wlh zan daga arude ta Kwaye zanin har zuwa guiwa, tare da tsiyayar da hawaye"

Bulalan ya daga sannan yace idan kinga dama ki kirga, dan ni ba kirgawa zanyi ba, kuma idan kika sosa bandashi alissafi"

Fukanta cike da hawaye ta kalleshi acikin zuciyanta tace lallai wannan bakin mugune so yake yaga karshena, nan danan taji wata dakiya tazo mata, dan haka ta tsaya cak"

Kin shirya?

Eh tafada tana kauda idonta gefe"

Bulalan ya daga yaita zula mata tuntana daurewa harta kasa taita zuba uhu"

Shiko *JAMAL* kaman kara zugashi take har wani tsalle yake yi"

Goggo tani ce tajiyo uhunta tundaga cikin gida harda gudunta ta nufi idan take jiyo sautin kukan daker ta kwaci ma,u ahannun sa"

Hargun mama goggo tani takai ma'u tanaci gaba da korafin cewa adaina mata irin wannan dukan haka kwanaki usman ya mata dan banzan duka kartaxo ta saba da duka"

Mama batace komai ba mikewa kawai tayi tabar dakin"

Nan ma,u ta kwanta tanajawowa *Jamal* Allah ya isa acikin zuciyarta"

Ko ina ajikin ma,u ciwo yake dan yau abin ya mata yawa ga wahalan da *Duna* ya bata gana wannan dan iskan abokin yayan"

*****

Washegari ma haka ta tashi batajin kwarin jikinta dan haka batace zata makaranta ba"

Misalin 11 tayi wanka ta danji dadin jikinta, falon Abba ta wuce acan ta samu mama"

Gaban abba ta zauna ta tankwashe kafa sannan ta fashe da kuka"

Nan danan hankalin Abba ya tashi, zaman shi ya gyara tare da kura mata ido sannan yace"

Mamana waye ya taba ki?

Cikn kukan tace ba yaya usman bane yacewa abokinshi wai banajin, shikuma kawai sai ya ciro bulala ya hau dokana"

Abokin nasa?

Eh Abba"

Duka fa kika ce mamana?

Xanin ta ta fara dagawa tare da fadin eh abba kagama gurin"

Babban mgn Abba ya fada bayan yaga inda jikin ma'u yai rudu2"

Mikewa yayi sosai sannnan ya daga waya ya kira usman"

Cikin Monti 15 suka iso, dukka su jallabiya ce ajikin su fara kar"

Tunkafin su zauna abbba yake fadin a'a wanake gani kaman *Jamal*"

Mumurshi kamal din ya saki yana shafa keya yake fadin nine abbba"

Bayan sun gaida abbba hira suka hauyi, dan haka ma'u ta Kule"

Mikewa tayi tana kokarin tafiya Abba ya dakatar da ita sannnan yace"

Mamana kinga wannnan sunan shi Jamal yayanki ne shima, nida mahaifin shi tare mukayi wasa, dan haka yadda usman yake da daman hukuntaki shima yana da dama kijji ko"

Tana barin falon ta fara kunkunai kai tsaye ta wuce dakin mama dan daman tuni ta bar musu falon, zama tayi tare da share guntun hawayenta sannan taci gaba da kunkunan ta"

Mama na gefe tanajinta jefi jefi tana tsintan abinda take cewa, zuwa can tace"

Kee!!!! Tashi kibani guri, haka kurun zakizo kisani agaba kinamin mita toh me kikeso nayi rama miki zanyi kome?, yariya banda fitsara ba abinda kikasa agaba ke wacece da baza'a dakeki ba?, to kici gaba kece zakisha wahala"

Dahaka mama ta fice tabarta adakin"

Itama mikewa tayi tabar dakin"

Tundaga ranan asmau bata sake zuwa makaranta ba har wani satin ya zagayo, gashi kewan deen ya dameta, dan tasan yanzun har ya gaji da zuba ido"

***

Yau ta kama asabar dan haka tunda wuri ma'u tayi sallama ta fito"

Saidai tana fitowa taci karo dasu yaya suna kokarin shigowa"

Dauke Kai tayi taja gefe sanan tace ina kwanan Ku murya ciki2"

Yaya usman ne kawai ya amsa amman jamal gaba yayi, harta kusa fita taji jamal na cewa usman, kunabin bayan yariyar nan Kuwa....

Daidai lokacin suka sha kwana dan haka bataji amsan da yaya usman ya bashi ba"

Tana tafiya tana waige dan gani take kaman Jamal zai biyo ta"

Hango deen akofar gida shine yasata ta manta komai tundaga nesa ya sakar mata murmushi itama mayar mai tayi tare da sunkuyar da kanta kasa"

Tana isa gaban shi taja ta tsaya tare da kara sunkuyar da kanta kasa"

Babu abinda deen yake banda kallonta acin tuhuma ya dago fuskanta sannan yace"

Me yasame ki kwana 2 ?

Shiru tayi tana kara tsurawa kafarta ido"

Girgiza kai yayi sannan ya cije lebensa na kasa Yasa ke daga ido ya kalleta cikin bacin rai yace"

Yayan kin yasake dukan ki ne?

Kanta na kasa ta girgixa kai"

Kanshi ya daga ya kalli sama sannan yace yasin zanyi rashin mutunci wlh, fuskanki ya nunamin an cuceki kuma kina cikin bacin rai wai wanene wannan yayan naki? a ina zan sameshi ?

Nan danan hawaye ya fara zubo mata dan bakaramin takaici takeji ba, haka kurun daga zuwan shi zaisa bulala ya zane ni"

Murya kasa2 tace ba yayana bane, abokin shi ne"

Abokin sa ? Idon shi daya ya rufe sannan ya karkata dayan yace dukan ki yayi?

Hannu tasa ta share hawayen daya zubo mata sannan tace eh"

Uban wanene ya bashi iznin ya dake ki?

Bata iya cewa komai ba illah kukanta daya karu"

OK shikenan dena kuka kingane?, ban ni dashi zan nuna masa daya tabaki gara yaje ya tari babban mota, haduwan mu bazaiyi kyauba naratse sai uwassa ta kasa gane shi"

Yana mgnr ne yana daga hannuwan shi tare da karkace baki"

Ganin inda yake fada yana tiriri yasa ma'u jin dadi ko banza tasamu wadda zai kwatan mata enci, amma tafison deen yayi abin cikin sirri ba baro baro ba dan batason kowa yasan shi arayuwar ta"

Dago kanta tayi sannan tace bari na shiga makaranta idan antashi zan shigo nagaida ummi....

Batajira me zaice ba ta fara tafiya tana jiyo muryan shi yana cigaba da babatu"

Ko a makaranta batayi karatun kirki ba, kawai tunanin hanyan daukan fansa take"

Zuwa can tunanin duna ya fado mata, tabas duna kadai ya ishi jamal amman idan deen ne duka zasu masa dan suma suna takama da karfi, karshema kila su kamashi, amman duna zai iya basu whl batare da sun san waye ya turoshi ba"

Kwashewa tayi da dariya sannan tace inama ina gurin inga ya zasu yi?

Takarda ta samu ta fara rubuta yadda takeson abin ya kasan ce, tana cikin rubutun aka tashi tsayawa tayi ta karasa sannan ta fito"

Lokacin da tafito babu sauran dalubi amakaranta duk sun fita"

Gabanta ne yayi mummunan faduwa sakamakon hango Jamal tsaye shida baba idi"

Batasan me suke cewa ba, tana kokarin fita taga jamal ya wuceta"

Abakin makarantar taga motar yaya usman, budewa Jamal yayi ya shiga, har sun tada mutar yaya usman yace shigo mutafi"

Wani haushi ne ya kamata, tasan duk shirin jamal ne, bayan ta zauna suka fara tafiya banda masifa babu abinda yaya usman ke yi, Jamal ko kauda kansa gefe yayi ya bude jarida"

Ma,u ko hankalinta yana kan dakalin da deen yake zama, yana nan zaune sai raba ido yake"
Chapter 8 · 0% Book details