← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 47

Sashe 18

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan danan jikin dada ya rikice, haki ta fara babu kyau2 tawa dan haka usman yaje ya kira likita, cikin mintocin da basu wuce 7 ba, dada ta fita cikin hayyacinta dole tasa aka bata gado"

Mama da momy ne suka kwana akan dada yayin da Alhaji Musa da su Jamal suka kwana akan abba, babu bacci dan Abba sai kusan asuba ya samu bacci"

*****

Washegari Abba ya tashi jikinshi yayi dama dama bakaman jiya ba, saidai jikin dada sai kara rikicewa yake"

Da misalin karfe 1:23pm Alhaji inuwa manga ya iso duba jikin abokin shi"

Bayan gaishe2 tsanin alhaji inuwa manga da alhaji musa, matsawa yayi gurin Abba"

Mgn suke ahankali abba da kanshi yabawa alhaji inuwa lbrn halin da ake ciki"

Nasiha yamai tare da tare da kara bashi shawar wari, nan Abba yadan ji sanyi aranshi"

Zuwa can abba yaji bacin rai ya sake taso mai, dan haka ya kira jamal da usman yace musu..... Maza kuje gida kutaru Ku karya min asma'u"

Kaman jira suke suka fita cikin sauri, Alhaji inuwa nakiran su ina, sun riga sun fice"

Bayan fitan su alhaji inuwa yakalli alhaji musa yace inason ganin ka"

Waje suka fita sun dan juma sannnan suka dawo fuskan su dauke da murmushi"

Abba kallo ya bisu dashi, koda besan me suka tattauna ba, ya san magana ce me mahimmanci"

Ganin inda yake kallon su, yasa alhaji musa cewa......rana ita yau za,a daura auren *Asma,u* da *Jamal* mahaifin shi ya neman mai aureta aguri na kuma na bashi"

Cikin farin ciki Abba yace Allah ya nuna mana"

*****

Ma'u ko yadda taga rana haka taga dare ba abun da yake damunta ban da tunanin abban ta, kasa komai tayi nan danan ta rame tai zuro2 goggo tani ce taita lallashin ta ruwa kawai take iya sha"

Misalin karfe 3:00 goggo ta matsa mata tai wanka, dan haka ta mike ajikinta babu kwari tacire kaya ta dauko towel ta daura, toilet ta shiga harta tube ta murza kunfa, tafarajin ana kwala mata kira, cikin hargagi, muryan yaya usman ta gane aciki, hayaniya irin nasu na sojoji"

Arikece ta mike ta dauki towel dinta ta daura, daidai lokacin taji an banko kofar daki"

Saida ya kira sunanta so uku ajere sannan asma'u ta amsa adabur ce"

Fito dan uban ki"

Cikin rawan murya tace yaya wanka nake yi"

Idan kika bari nashigo bazan miki da wasa ba"

Kara rikicewa asma,u tayi, sannan ta rushe da kuka, batai aune ba taga yaya usman acikin bayin, mari ya wanka mata, kafin ta ankara take karajin saukan wani, dan haka ta riki ce tayi waje rike da towel dinta dake kokarin warwarewa"

Mutum take gani dishishi kamar yaya Jamal zaune agefen gadonta cikin kakin sa, yana danna waya"

Gani tayi ya rabun mata kashi2 duk inda ta waiga shi take gani, daga can ta hango yaya usman yayo kanta, Dan haka aguje ta tayi kan abin da take ganin shi kaman gizon yaya jamal

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[22:53, 12/19/2017] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挆馃挐馃挐馃挆
鈥�*BUGUN ZUCIYA*鈥�
( 鈥婬eartbeat鈥�)

馃挀馃挐馃挆
馃挆

馃挀馃挐馃挆
鈥婤y鈥�
馃挆
鈥嬧€�*Fadeela Lamido*

*@AM拢拢NCI WRITER'S ASSOCIATION馃*

鈥�

Dedicated馃憞馃徎
*Miss xoxo*
I love u, so much馃槝
*Kaunarki gareni daga Allah ne*

3鈨�8鈨o4鈨�0鈨�

馃ず馃ず馃ず

馃ず Duk da cewa Jamal yayi kaman beganta amman yana ganin inda ta nufoshi gadan2 yasa ya ajiye wayar shi agefe sannan ya miki cikin sauri"

Itako asma'u tanazuwa ta fada jikin shi ko da tajita jikin shi ma, bata tsaya ba, kara kadandane shi take dan tasan idan tayi haka dole yaya usman yabarta, dan haka hannunta tasa guda 1 ta bayan sa yayin da dayan ta danne towel dinta dashi"

Ganin haka hankalin Jamal yayi mummanan tashi kokarin rabata da jikin shi yake tare dasa hannushi ya rike mata towel din kamar yadda yaga tayi, saboda gudun kartayi tsirara, cikin tsawa yake fadin usman bari, bari, menene haka ?"

Usman natada jijjiyan wuya yake fadin..... kasan Allah wlh saina sumar da yariyar nan"

Shima cikin tsawa yace naji ko ka shetama zakayi zaka iya amman ka bari tasa kaya ajikin ta"

Usman fah ranshi ya riga ya bacci banda jijiyoyi kan shi baka hango komai, dan haka jamal ya dauketa cak ya nufi toilet da ita, tare da kare dukan da usman yake kaimata"

Ciki ya sakata sannan ya jawo kofan tare da tsawa abikin toilet din dan usman har yanzun be hakura ba"

Kallo Jamal yabi usman dashi sannan yace dallah jin inda kake tada jijiyan wuya, mace ce fah, macen ma yar ficiciya"

Juyawa usman yayi yana huci, ya fice"

Usman na fita jamal yaja tsaki sannan yace ke kuma dallah karki cikawa mutane kune da kuka, nan dan ma'u ta kunshe bakin ta"

Zuwa can ya sake cewa fito ki saka kaya, ki fito falo ki same ni"

Sai da taji ta dainajin motsen sa sannan ta fito, tayi zuro2 da ita"

Saboda tsabar rudewa riga daban siket daban ta Saka, sannan ta daura Karamin hijjabi akai"

Afalo ta same su, Usman har yanzun bebar huci ba, Jamal ko kallo ya bita dashi, Sannan yace tsuguna kisa guiwar ki akasa"

Tsugunawa tayi kamar yadda yace tare da sunkuyar da kanta kasa"

Daga hannun ki sama sannan ki rufe idon ki"

Innalillahi, ta fada sanan ta miki tana dan bubbuga kafa alamar tsoro"

Mekewa jamal yayi tare da fadin eh lallai baki dakuba, rawa ma kike min ?

Cikin kuka ta tsuguna tana fadin wlh na daku, hannu nama ciwo yake min dan Allah kuyi hakuri"

Usman ne yace nagaya maka duka ne ya dace da yariyar nan, kace ba haka ba, mikewa yake kokarin yi Jamal ya tare shi tare da fadin banni da ita, karyan rashin kunya take"

Dasauri ma'u ta tsuguna tayi kamar yadda yace, idonta arufe amman hawaye na zuba a idonta, bayan kusan minti 30 taji daya daga cikin su ya fita, saidai bata san ko wanene ba"

Gaba daya jijjiyoyin hannunta ya sake, kuma hakan takejin kamar kallonta ake dan haka tayi saurin bude ido"

Jamal ta gani ya ya kurawa guri daya ido, bin inda yake kallo tayi da idonta, nan ta gane ashe sanadin daga hannunta sama rigarta ta daga dan haka cibiyanta baiyane yake, kuma indai idonta ba kizo ya mata ba' Jamal gurin yake kallo"

Cikin sauri tasa hannunta ta jawo siket dinta sama, zabura Jamal yayi tare da fadin ke!! Waye yace ki bude idonki"

Mayarwa tayi ta kulle, tare da kara tsanan Jamal, tsine mishi taitayi azuciyanta tare da mai fatan bala'i kala2, bata san abin da yasa ba, duk abin da yaya usman zai mata kadan yake bata haushi, amman na jamal yana mata kuna"

Saida Jamal yaga tana tangadi kamar zata fadi sannan yace zauna"

Zama tayi tana share hawaye da hijjabinta, idon nan luhu2

Wuce kiban waje kuma duk ranan da kika sake Tayar da zancen me kare sai kinci kaniyar ki"

Tafiya ma'u tayi harta shege daki tana jerawa jamal Allah ya isa, tare da addu'an Allah yasa yana fita mota ta begeshi ya mutu"

Har Washegari su mama basu dawo ba, dan haka taji bazata iya hakuri ba, Sani ta samu ya dauketa suka tafi"

Tunda sani ya sauketa gabanta ke faduwa ba komai ke damunta ba sai haduwanta da Abba da mama, tasan suna fushi da ita"

Tana tura kofar dakin sukai idon 4 da mama, daga can gefen gadon ko, wani Mutun ne, me tsananin kama da Jamal sosai kamar harta baci"

Mama na ganin ma'u ta mike tana fadin.....

Me kikazo yi ?, menene ya kawo ki?, kinzo ki karasa su ne ?....

Sakin kofar ma'u taso yi, karafff taji anriketa, wannan mutumin ne me kama da yaya Jamal"

Hannnuta ya ruko suka shigo cikin dakin, sannan ya kureta da ido, zuwa can yace a shema yariya ce karama, rashin wayo ne yake damunta, kallonta ya karayi sannan yace..... Yi shiru kinji 'yata? Ki daina kuka"

Ta gaban mama ya wuce da ma'u agaban gadon da abba yake ya saketa sannan yace...maza ki tsuguna kibawa mahauifiki hakuri, nasan kinje makaranta kuma kinsan girman iyaye agare ki, daga yau kar akara ce miki ga abinda zakiyi, kice a'a, domin duk abin da babba ya hango yaro ko rimi yahau bazai iya hangowa ba, kuma wani lokacin zuciyarmu nason abu, wata kila ba alheri bane, dan haka kiyiwa iyayenki biyayya, ko kinason wani abu ya samu mahaifin ki ta dalilin Ki,?

Gargiza kai ma'u tayi hawaye na sauka aidonta"

Toh ki maida hankali Ki, gatan da uba zaiyiwa yarsa shine aure, kuma wada duk ya rasa wadda zai masa fada yayi asara"

Sosai maganga nun suka shiga jikin ma'u, cikin kuka tafara rokon Abba gafara, tare da nuna masa yayi yadda ya gadama da ita"

Koda abba bece mata kallah ba Amman yaji dadin kalamanta"

Alhaji inuwa kan mama ya juya yaita nuna mata mahimmanci jawo 'ya'ya ajiki, tare da nuna mata ta daina kyaran ma'u"

Bayan ya gama da mama ya sake jawo hannnun ma'u ya kaita har dakin da dada take, saidai dada naganin ma'u ta fara fadin Innahu Sulaimana Wa innahu Bismillahir Rahimu, Kalu lahaula, Lahaula wala kuwata, kufita min da ita , gata nan, gata nan"

Momy ce ta rike dada tana fadin dada Asma'u ce fah, takwaranr ki, ki kwantar da hankali ki mana"

Karasawa daddyn Jamal yayi ya kamo hannun dada ya hada dana ma'u, sannan yace mata ta bata hakuri"

Cikin kuka ma'u ta rike dada tace dada kiyi hakuri dan Allah nina bari bazan kara ba"

Arikece dada tace kikace kin bari, kin hakura dame karan?

Kai ma'u ta gyada mata"

Ke takwara da gsk kincire me karan azuciyar ki?, nidai indai kinsan baki hakura ba' to ki fada min, dan nasa amai dani mahaifata"

Hannu tasa ta share hawaye sannan tace nahakura dada"

To ko kefa, yanzun kinga ran juma'a za'a daura miki Aure"

Gabanta taji ya fadi rasss, sakamakon jin zancen dauren aure, amman yaya zata yi indai tana son zaman lfy, dole tabi umarnin iyayenta"

*****

Kwanan su uku a asibiti suka dawo gida, Allhamdulillahi jiki yayi kyau sosai, kuma aranan abba ya sanar da ita ranan juma'a zai mata aure"
Chapter 18 · 0% Book details