← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 47

Sashe 26

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru momy tayi zuwa can ta waiga ta kalli nafisa sannan tace"

Nafisa kira min umma me lalle"

Mikewa nafisa tayi ta zura hijjabi sannan ta kama hanya"

Cikin kan kanin lokaci nafisa ta dawo da me lalle"

Bayan sun gaisa Momy ta nuna ma'u tace kitso zaki mata da lalle"

Cikin kankanin lokaci ma'u ta fito ras, yamma likiss jamal ya dawo lokacin ma'u na zaune afalon Momy"

Sallama yayi sannan ya nemi guri ya zauna"

Idon shine ya sauka akan lallen hannun ma'u, ya ilahi ya fada azuciyan shi, cikaba yayi da cewa tunda nake ban taba ganin irin wannan lalle ba, gani yayi fuskan ma'u ta kara wani irin kyau, dan haka ya sakankance yana kallonta"

Zuwa can yaga tana kokarin dago kai cikin sauri ya maida kanshi kasa tare da saka hannu aljihu ya Ciro wayar shi"

Daga ta yayi ya kare fuskan shi, zuwa can yaga bazai iya hakuri ba, kautar da wayar yayi daidai lokacin da ma'u ta dago idonta dan haka cikin sauri ya maida wayar"

Camera ya shiga yayi saitin ma'u sosai, ya kura mata ido, har ya shagala da kallonta"

Gyara zaman shiyayi, harda kishin gid'a, yana kara mata kallo babu wadda ya lura dashi"

Momy kallon Jamal take ajikin zuciyanta tace wannan kwai miskilin jaraba, wato ko kallota bama bazaiyi ba, harda wani tare fuska da waya"

momy harara kawai take jefawa Jamal, dan babu namijin da zai kalli ma'u beso ya kara kallonta ba sai Jamal"

Shiko Jamal tuni kwakwalwar shi ta nitsa cikin kogin tunani, kallon ma'u yake yayin tunanin shi ke kimanta masa wani sura tata"

Be Ankara ba yaga ma'u ta mike tana kokarin barin wajen"

Aranshi yaji beji dadin tashinta ba dan haka yaja tsaki ya sauke wayan"

Wani haushi ne ya sake kama ummi wato, saida yaga asma,u ta tashi sannan ya aje wayan, itace beson ya kallah kenan"

Ummi ce ta juya tace Jamal ka tashi ka tafi part din ku, ga asma'u can ta wuce, kuma dan Allah karkai nisa da ita, dan naga tana da tsoro"

Mikewa kawai yayi, saida ya fara tafiya sannan yace saida safe"

Allah ya tashemu lfy momy ta fada, cikin sauri ya nufi part din dan ya kosa Yasa ma'u a idon Sa"

Adakinta ya sameta sai dube2 take, abakin gadonta ya zauna sannan ya bita da ido"

Daker ya iya furta me kike nema ne?

Kuka ta fara matsuwa tare da fadin jakatace bangani ba"

Jaka ? Kuma ? Menene ajikin jakar"

Rasa abincewa tayj dan haka taca kayan kwalliya ne aciki"

OK indai kayan kwalliya ne karki damu zan saya miki

Ko inda yake bata kalla ba, taci gaba da neme2 ta, shima bekara bin ta kanta ba, waya ya sake cirowa ya kare fuskan shi, hotuna ya fara daukan ta, duk inda tabi saitin ta yake bi"

Lokaci lokaci ma,u na waigowa ta kalle shi acin ranta take cewa shi kuma wannan me yakeyi anan bayan ba shigowa yake ba"

Gajiya tayi dan haka ta koma gefe ta zauna, ko banza sarkan deeni tana debe mata kewa, idan ta kalli sarkan har kanshin deeni takeji, hawaye taji yana zubo mata, tasa hannunta ta share, sannan ta fara neman hanyar da Jamal zai bata aron wayar shi"

Kara karfin kukanta tayi, ahankali ya juyo ya kalleta, kewai baki gajiya da kuka ne?, kulum kuka, kullum kuka, yanzun kukan kayan kwalliyan kike?

Dago kanta tayi ahankali ta kalleshi, cikin sanyin murya tace inaso ne, nayi waya da mutanen gidan mu"

Murmushi yayi kadan, sannan ya dannan wayar ya mika mata"

Gani tayi har ya danna kira, Abba ta gani akan wayar cikinta ne ya duri ruwa domin ita deeni taso kira"

Muryan Abba ce ta katse mata tunani, cikin karsashin shi yake cewa, Jamal ya Kuke, yagida"

Rasa abin cewa tayi, zuwa can Abba ya sake cewa Jamal kanajina kuwa?

Cikin kuka tace Abba bashi bane ni ce"

Jim abba yayi zuwa can yace"

Yaya aka yi?, shiru yaji dan haka yacigaba ta cewa"

Kinanan da halin naki ko kuma ya dan lafa?, ki kula kisan abin kike idan kinason kiga fara'a ta kaman da, to kiyiwa mijinki biyayya, ki kwantar da hankalin ki kikautawa mijin ki, kinji ko?

Hankali tace toh abba"

Sosai abba yaji dadin inda ta amsa, dan haka ya mikawa mama wayar"

Itama nasiha ta mata sosai, sannan sukayi sallama"

Jamal ta juya ta kallah zuciyanta cike da haushin shi, tabas Jamal be da makusa, ya hadu sosai, kuma ya iya daukan wanka, sabanin deeni da kullum yana nan dai cikin kananun riguna kusan kullum jikin shi abude yake, dan wandonan shi da wuya su wuce guiwa"

Tunawa tayi da yadda batan Jamal take sheki luf luf, sannan ta hango ta deeni data baci da sara kaca kaca"

Juyawa ta sakeyi ta kalli Jamal, sannan ta kyauda idonta gefe, acikinranta tace ni babu ruwana da wai kyan ka, duk da haka nidai deeni nake so"

****

Tundaga ranan haka Jamal yake lalacewa wajen kallon lallen ,ma,u ko gaban Momy da daddy ko haka zaiyi saitin da wayar shi,

Har aka kwashe tsayon sati 2 zuwa wannan lokacin lallain ma'u ya fita dan haka ya farajin babu dadi, besan yana son lalle ba sai wannan lokaci"

Ranan da ta cika sati uku momy ta sake kiran me lallai, Momy cewa tayi wannan karon kiyi mata na gargajiya"

Juyawa Momy tayi ta nufi dakinta, afili take fadin nikam narasa gane kan Jamal, wannan wacce rayuwa ce?, nidai nasan babu namijin da zai kalli ma'u yace beso, amman al'amarin Jamal ya fara bata tsoro, ko kallo ma'u bata isheba"

Jamal be kula ma'u tayi lallai ba sai washegari nan ya lalace gurin kallo har ya makara fita gurin aiki"

Koda yajema haka yake lalacewa gurin kallon hotonan ma'u

Har lallen ma'u ya fita Jamal be nuna yana so ba ko sha awan shi ba, dan haka momy bata sake kiran me lallai ba, aramta ta fara tunani kila ba lafiyaye bani, ganin tun tasowan shi bashi da budurwa, duk da cewa yan mata da yawa suna cewa suna sanshi amman saiya ce wai sun rainashi ne"

Tunanin hajiya asabe ne ya fado mata, kodai tayiwa Jamal wani abu ne dan ta cerai mai sha'war mace, dan ta kula kiyayyan da hjy asabe take nunawa Jamal tayi yawa"

*****

Ran da lallen ma'u yayi sati 1 da fita Jamal ya gaji da jiran ganin sabon lalli, dan haka daya shirya tafiya ya fito afalo ya samu ma'u"

Bayan ta gaidashi yasa hannun a aljihu yaciro, dubo 20 yaje agefen ta, tare da fadin gashinan kiyi lalle da kitso"

Dasauri ma'u ta kalleshi sannan tace, aini daman momy ce take cewa ayimin, bani nake zuwa ba"

Shiru yayi zuwa can yace toh Ki rike kudin saikije kicewa momy kinason amiki lalle"

Turo baki tayi kamar me shirin kuka tace nifah daman bason nake ba, dan dai momy ce kawai nake tsayawa"

Wani haushi ne ya kamashi cikin fada yace"

OK rashin kunya zakimin kenan ?

Ganin ta sunkuyar da kanta kasa yasa ya fice, yana kada kai"

Bayan kwana biyo yaga bazai iya hakuri ba, dan idan yana kallon lalle wani irin nishadi yakeji part din Momy ya nufa yana sanye da jallabiya"

Momy da daddy ya samu afalon nafisa na kwance jikin momy,"

Bayan ya gaida su ya kalli nafisa yace"

Ke bannan?

Mikewa tayi ta fice"

Motse ya fara da bakin shi, ya rasa ta ina, zai fara zancen yana son husna tayi lalle, ai wani ma sai yace sonta nake"

Wata zuciyar ce tace, to meye dan motum yace yana son kawar sa tai lalle"

Daddy ne yace jamal kaman bakin ka da mgn"

A'a daddy ba komai"

Shiru sukayi zuwa can Jamal ya mike ya nufi fita har yakai tsakiyan falon ya tsaya, tare da Fadin momy ina son na ganki.....

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


6⃣0⃣to6⃣3⃣

🤳🏻🤳🏻🤳🏻 Yana gama fadin haka ya shige dakin momy"

Mikewa tayi tabi bayan sa, yayin da daddy ya bisu da kallo"

Bayan momy ta zauna ta kalli Jamal tace ina jika yaya aka yi?

Dariricewa yayi yarasa mema zan ce, zuwa can ya dan sosa keya sannan yace"

Yariyar can ne naga kafarta kaman na maza, ko dan irin kunshin nan babu"

Cikin mamaki Momy tace wacce yariya kenan?

Husna, ya fada atakai ce"

Hmmm Jamal Kenan, ka manta kanwar ka ce?

Dukar dakai yayi kasa sannan yace ban manta ba momy, ai bawani abu bane dan nace kanwata tayi kunshi ko?

Murmushi Momy tayi sannan tace"

Eh bawani abu bane, amman ina baka shawara tun wuri ka sauke girman kan nan naka, ka daina yaudaran kan ka"

Kanshi akasa yace momy ban gane yaudaran kaina ba?

Tsaki Momy taja tare da mikewa tsaye tana fadi, ni wlh bana son munafunci mutun naso yana kaiwa kasowa"

Har momy ta fice Jamal binta da kallo yake, sannan ya jigina kanshi jikin gado, runtse ido yayi idan na fahimci momy nufinta son husna nake, eh nasani tunda na daura husna a idona ban tajin wai basonta ba, inason ta amman bada Aure, sosai nakejin ta acikin zuciyata, dan haka nashige cikin lamarinta"

Haka yaita tunani daka karshe ya tashi ya bar gidan"

Momy ko koda ta koma gurin daddy mamakin halin Jamal taitayi, ita bataga amfanin mutum nason abu ba amman yaita wani kyauce kyauce, kwashe yadda sukayi da Jamal tayi ta fadawa daddy"

Dariya daddy yayi sosai tare da fadin tunda yana son kunshi daya fita kisa amata sabon design"

Itama momyn dariya ta sake yi, sannan tace"

Ni wlh mamaki ma abin yake bani, kofa kallonta baya yayi, amman kaji ashe idon sa ya gano masa kunshin ta"

Bayan fitan daddy momy kiran ma'u tayi, tace nafisa ta tsefe maki kai, anjima umma zata zo ta miki kitso"

Mgnr Jamal ce ta fado mata, take taji batason yin, kumshi kwata2, kanta tasa akasa sannan tace"

Momy abari sai gobe ne dan kaina yau ciwo yake min"

Shiru ummi tayi zuwa can tace toh Allah ya kaimo goben lfy, kin sha mgn ko?

Eh kawai tace, sannan ta mike zata fice"
Chapter 26 · 0% Book details