← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 47

Sashe 43

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Jamal nagaji fah, wlh nagaji tunanina bazai iya dauka ba, waini sai yaushe zanji dad'i inama na mutu tun ina kar.......

Wani tsawa Jamal ya buga mata wadda yasata yin shiru batare da ta shirya ba"

Kina hauka ne? Karna sakejin kin fadin irin wannan mgnr, duk inda kika samu kanki ki godewa Allah

Kuka take ahankali"

Shima hawaye ya share tare da ajiyan zuciya yace.....

Husna dan Allah karki yadda arabamu, deeni ba sonki yake ba, sha'awarki kawai yake yi, natabajin shi yana miki karyan banza da wofi, har yana kiran Ki da Furan sa, idan natuna inajin takaici, agidan ubanwa kika zama furan sa? Darajan Ki ta wuce ta fura, babu abinda da za'a kwatantaki dashi, yaudaran ki yaki yake, kuma ni tundaga ranan natsani fura
ko ganinta bana so yi"

Kosawa tayi yabar mgnr, dan tasan yana iya birkice mata, yanzu nan, dan haka tace....

Yaya Jamal kabar wannan mgnr"

Dif, yayi xuwa can yace.....

Husna daddy ya bani daganan zuwa gobe, nakawo mishi sakin ki, dan haka adaren nan zabar garin bazan dawoba sai daddy ya janye kudurin shi akaina, zabar wayata agida dan kada anemeni ke kuma Ki ringa barin wayarki akunne dan zan nemeki, idan na isa inda zan tsaya, sannan aurena nakan ki karki yadda da sako arubuce, ban rubutaba, kuma bazan rubuta ba"

Ban aiko kowa ba, kuma bazan aiko ba, karki yadda da kowa, idan bani kika gani idona da nakiba"

Kuka ta fasa, cikin kukan tace......

Yaya Jamal karka tafi ka barni dan Allah"

Husna nima ba'a son raina zantafi ba"

Cikin matsanan cin kuka tace toh ka tafi dani wlh zan bika.....

Heart beat
*Mmn Yazeed*​

h💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


*Masoya BUGUN ZUCIYA kuyi hakuri pls🙏🏻🙈 abubuwa ne sukamin yawa, naso yau nabaku mamaki amman nakasa, gobe insha Allahu page 2 ko 3 zan turo, nagama typing editing ne ya rage, wadan da sukamin mgn ban amsa ba kuyi hakuri pls🙏🏻 sakon ne yamin yawa*

1⃣0⃣3⃣

Indan katafi ka barni zan shiga wani hali bansan inda Zanyi ba"

Husna kiyi hakuri, nima bansan inda zani ba, kinga bekamata na dauki da karamin ciki inkaiki inda xaki wahala ba"

Cikin kuka tace nidai wlh xan bika, duk Inda ka zauna nima zan iya zama, wlh yaya karka tafi ka barni"

OK toh shikenan daina kuka, maza Ki share hawayen ki kuma ki saki ranki"

Make kafada tayi kamar tana gaban Sa, sannan tace a'a saika min alkawarin bazaka gudu ka barni ba"

Namiki husna, ki shirya yau dinnan inanan tafe, amman karki gayawa kowa"

Dahaka sukayi sallama, jikin ma'u sanyi ya kara haka ta takure guri daya taita kuka"

Jamal ko yana gama waya da ma'u ya tashi ya dingisa, mahimman abubuwan shi ya hada guri daya sannan ya sauya kaya"

Awaya ya kira drive bayan ya shigo yace ya dauki jakar yasa amota gashi nan zuwa"

Drive ya fita babu dadewa Jamal ya fito, babu kowa afalon dan haka har ya fita babu wadda ya ganshi"

Hanya suka dauka acikin su babu me cewa kala, yamma likis suka isa Kano"

Sauka Jamal yayi ya nufi cikin gidan cike da zumudin son ganin ma'u

Salama yayi abakin falon, daga ciki mama ta amsa"

Ma'u tunda taji muryan Jamal ta mike tare da ajiyan zuciya"

Cikin ladabi ya shiga falon yana dingisawa tare da sunkuyar da kanahi kasa"

Mama naganin Jamal tace ah'ah Jamal kai da kanka ka kwaso hanya kana fama da kafar ka"

Shafo keyarsa yayi tare da satan kallon ma'u yana murmushi"

Itako ma'u tsaye tai ta kasa cewa komai, kallon Jamal kawai take tare sonjinta jikin shi"

Bayan sun gaisa mama ta shiga kitchen sannan ta kira ma'u"

Bin bayanta yayi da kallo tare da hadiye miyau"

Zuwa can ta dawo dauke da kayan marmari ta aje gaban shi"

Tana kokarin ajewa ya rike hannunta tare da kokarin dagota"

Kan cinyar shi yaso zaunar da ita ta cije tare da fadin ciyon ka fah?

Gefe ya nuna mata tare da fadin daga nan zaki zauna"

Zama tayi sannan ya hada hancin shi da tana tare da fadin kince zaki bini ko?

Kai kawai ta daga almar eh"

Cikin sauri ya wawuro bakinta, nisa yayi sannan ya fara shafa jikinta"

Ummi ce ta sawo kai bakinta dauke da sallama, cikin sauri ta juya tun batakai ga karasawa ba"

Hakan yayi daidai lokacin da suke kokarin rabuwa da juna"

Ganin mama tajuya ya tabbatar musu ta gansu dan haka takaici yasa ma'u ta fara kuka"

Jamal ma kunya ta kamashi, amman fuskan sa na dauke da murmushi yake kallon ma'u, zuwa can yace......

Ke dai kuka be miki wuya, yanzun dan Allah meye abin kuka?

Cikin kukan tace mama fa ta ganmu"

Toh menene husna?, nifa mijin Ki ne bare kice za'amiki fada, dallah ni tashi ki dauko gyalen ki, sai kice ma mama zaki rakani naganu Firdausi"

Wlh yaya bazan iya ba, ni yanzun kunyan hada ido da mama zanji"

Mikewa jamal yayi tare da fadin toh shike nan, ni bari na wuce, dan bani da lokaci'

Rikeshi tayi da sauri, tare da fadin to yaya ai kai ya kamata ka gaya mata"

Shiru yayi yana kallon ta zuwa can yace....

Ok toh yanzun abin da za'yi, kije ki Debi kayan ki kadan kisa amota"

Yana tsaye harta dawo sannan ya matsa kofar mama yace.....

Mama zantafi"

Fuskarta dauki da fara'a tace yau yau din nan ai na dauka kwana zakayi"

Cikin jin kunya yace a'a yau zantafi nazo ganin Firdausi ne"

Murmushi kawai mama tayi dan haka jamal ya sake cewa......

Zamuje da Husna ne ta raka ne"

Adawo lfy Jamal kaida matar ka"

Dan sosa keya yayi sannan yajuya ya kalli ma'u yace dauko gyale"

Basu wani zauna agidan usman ba suka fito bayan Jamal ya gama tofawa yariyar addu'oi"

Tasha Jamal yasa drive yakai su sannan suka sauka tare da kayan su"

Gargadi yawa drive sosai cewa duk wadda ya taban baye shi yace kano ya kawo shi, daganan karya kara komai"

Saida drive ya wuce sannan suka hau motan sokwato"

Drop suka dauka dan haka karfe 10 da wasu mintoci suka shiga cikin garin sokwato, lokacin har Bacci ya kwashe ma'u tana manne ajikin Jamal"

Har suka isa kofar gidan da Jamal yama drive izinin shiga, ma'u bata tashi ba, kallonta Jamal yayi, bacci take kuma dagani tanajin dadin macci"

Kallonta yake vabu kyaukyautawa muryan drive yaje yace oga nagama sauke kayan"

Azabure jamal ya kalleshi sannan yace......

Toh kashi kuma madam tana bacci ni kuma inada matsalan kafa bazan iya daukanta ba"

Cikin sauri drive yace oga tashinta zakayi ai"

A'a bazan tasheta ba, hukuri zakayi har ta tashi ko wani abu ne saina kara maka, dan babu kyau mutum yana bacci atasheshi"

Shiru drive ban yayi acikin zuciyar yace......

Lallai wannan ba karamin so yakewa matar nan tashe ba, ni ina ruwana indai za'abani kudi, Allah yasa ma karka tashi sai gobe"

Jamal babu abinda yake banda kallon ma'u, tun da yake betaba tsayawa ya kallita hankalin shi kwance kamar yau ba"

Tayaya daddy zaice saina sakeki, bayan na farajin dadin aurena, tayaya hakan zai kasan ce, Addu'a yayi azuciyar shi Allah yasa abba ya fahimci gaskiya"

Ma'u ce ta bude idonta tare da fadin nifa nagaji har yanzun bamu kawo ba"

Munkawo husna cewa nayi bazan tasheki ba sai kin gama baccin"

Wani irin kallo tamai tare da mamakin jamal, kwallah taji ya cika mata ido, Ashe Jamal zaisota haka?, lallai ta yadda kiyayya na komawa soyya"

Waigawa tayi ta kalli gidan tare da zare ido, barikine irin na sojuji, ko ina sojujin ne ke zurga zurga, suna fitowa daga cikin motar wani ya taho ya sarawa Jamal sannan ya mika masa key"

Ma'u na manne jikin shi ya bude kofar suka shiga"

Falo ne madaidaici me dauke da daki daya tak da bayi aciki, daga can gefe kuma akwai madaidaicin kitchen"

Bayan ya zaunar da ma'u yace ina zuwa bari nayi sallah ke kuma kibari ki huta"

Kallon shi kawai tayi yana fitowa toilet din ta shege, dan haka tare suka yi sallah"

Bayan sun idar yace bari naje na samo mana abinci"

Be dadeba ya dawo bayan sunci sunsha, ma'u ta fara hamma "

Kallonta Jamal yayi tare da fadin tashi kije Ki kwanta"

Hawa gadon tayi sannan ta kalli shi yana zaune akasa ya mike kafafuwan shi tace......

Yaya gidan nan fah ya mana kadan, yazun kai a inazaka kwanta?

Ban gane a ina zan kwanta ba?

Jan bargo tayi ta rufe idobta sannan tace naga gado daya ne, kai kuma mace bata hawa gadon ka"

Take sanda ya fada mgr ya dawo mai, dan haka yayi dariya sannan yace.....

Ke bakya mantuwa ne?

Bata sake cewa kalla ba ta rufe idotan tai shiru"

Tanajin shi ya mike ya sauya kaya, sannan yahau gadon tare da yaye bargon ya shiga, zuwa can ya mika hannun sa ya rungumota jikin shi"

*Abuja*

Bayan tafiyan jamal, zuwan momy dakin uku bata ganshi ba, lekawa waje tayi nanna megadin yake shaida mata Jamal ya fita tare da drive"

Momy bata tsorata ba, saida taga drive ya dawo babu Jamal"

Tambayan shi tayi ina jamal, kamar yadda Jamal ya fada mai haka ya fada"

Acikin zuciyarta tace wai meyasa Jamal bejin mgn, wannan kafar tashi so yake ta rube, idan ba hakaba me zai kaishi kano"

Da daddare daddy suka dawo tare da deeni da alhaji bashir harda ummi"

Rike daddy yake da deeni yana mai sannu"

Bayan sun zauna momy ta kawo musu abinci"

Daker deeni yaci kadan kallon shi momy tayi taga ya rame"

Shima daddy kallon Sa yayi sannan ya mike cikin sauri ya nufi dakin da Jamal yake"

Alhaji Momy ta kirashi, sannan tace......

Jamal baya nan"

Bayanan?, ina yaje?

Kwashe yadda sukayi da drive tayi ta gayamai"

Shiru daddy yayi na wani lokaci, sannan yace"

Ni Jamal zai watsawa kasa a ido?, shi kenan nasan abin da yake nufi, wayar sa ya dauka ya kira abba"

Bayan sungaisa yace Jamal yazo"

Daga can Abba yace........

Eh haka na samu lbr ance yazo amman ni bangansa ba"

Asma'u fah ?, tananan agida, koya dauketa ne?
Chapter 43 · 0% Book details