← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 47

Sashe 5

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakin gadon ya koma ya zauna sannan yace kince dada ce ta aike ki dan haka inason ki gayamin inda ta aike ki"

Tsintan kanta tayi tana fadin carbin ta ne ya tsinke tace nakai mata gyara"

Carbi? Jitayi yasake hada mata mari akumatunta duka guda biyu, bata kara sanin inda take ba"

Zuwa can ta bude ido taga matar yaya usman zaune agefenta tana mata fifita"

Muryanta adashe tace anty zainab kina gidan nan kikabar yaya yana neman kashe ni?

Rufe mata baki tayi idonta cike da kwallah tare da fadin Asmau naso na shigo mama ce ta hanani"

Kuka ma,u taitayi Anty zainab na lallashinta"

Washegari da safe ma,u ta tashi jikinta ya mata tsami ga fuskanta duk ya kunbura, jin muryan dada afalo yasata farin ciki , tashi tayi tana takawa ahankali ta fito falo"

Salati dada tasa lokacin da idonta ya sauka afuskan asmau sannan ta juya ta kalli abba tace"

Au yanzun nan saida ka duki yariyar nan?, aida kasani ka hada haddani tunda nice babban me laifi, amma ba komai Allah ya baka hakuri, juyawa tayi zata fita ranta bace"

Hakuri abba yaita bawa dada, daker ta yadda ta dawo, rike asmau tayi suka shige daki, bayan sun zauna ne dada ta kalli asmau cikin tohuma tace"

Toh asmau mgn nazo muyi me mahimmanci, kuma inason kisa aranki wannan mgn tsakanin ni dake ne babu mejinta"

Gyada kai ma,u tayi tana share ragowan hawayen dake fuskanta"

Asmau menene tsakanin ki da wannan ibbilishin yaro?

Shiru tayi tana kallon kafar ta, tare da zubo da wasu sabbin hawaye"

Takwara badake nake mgn ba?

Cikin kuka tace dada ni wlh babu komai tsakanina dashi ahankali takwashe duk yadda akayi ta gaya mata"

Shiru dada tayi tana mamakin hali irin na asmau, ace yariya ba'abin da tasa agaba sai tsokana, zuwacan ta kalli ma,u sannan tace"

Karki kara irin wannan rashin hankalin, ban da kuruciya me ya dameki dashi? Mutumin da manya ma gudunshi suke, shine ke zakina shige mishi?, kinatsu sosai kisan me kike keba karamar yariya bace, koko so kike kisa ubanki atashin hankali?

Girgiza kai tayi sannan tace aina bari baza sake kulashi ba kuma dan Allah idan yaya usman ya tambaye kice kika aikeni"

Hmmm takwara kenan, naji kuma zan fada amman saikin min alkawarin baxaki sake kula wannan shaidanin yaron ba"

Har cikin zuciyarta batajin dadin sunan da Dada take kiran deeni, dan haka saida ta runtse ido sannan tace, nayi alkawari"

Bayan kwana biyu jikin ma,u yayi sauki saidai har yanzun akwai shaidan duka ajikinta kuma fuskanta be gama sabewa ba"

Shiryawa tayi cikin kayan mkrnt sannan tayiwa mama sallama ta wuce"

Wata zuciyar ce tace kibi ta gurin mana ko hangoshi ne kyayi daga nesa, a'a nayiwa dada alkawari ta fada afili, koda takai daidai lungun fasa bi tayi dan jitake idan bata gansa ba kaman wani abu zai faru"

Tunkafin ta isa gurin ta hangoshi sai waige2 yake kamar dai yana neman wani, zuwa can ya juyo da kallon sa, gurinta, wani munafukin murmushi ya sake sannan ya fara tahowa"

Kaucewa ma,u take, tare da kara sauri, amman duna sai dad'a binta yake"

Ganin haka ma,u tasa kuka, tare da tsayawa cak"

Wani irin kallo yake mata, tare dason kallon kwayar idonta, zuwa can ya mika hannun sa ya shafi kuma tunta shedan yatsu ya gani kwance"

Nan danan idonshi ya rikice ya kuma jawur, sannan ya karkata kai yace"

Shedan hannun waye afuskan ki?? uban waye ya dake ki??

Jikin asma'u banda kerma ba abin da yake, agigice ta kauce tana kokarin guduwa"

Damkanta yayi tare da fadin ina wasa dake ne? Ashe yau unguwar nan babu zaman lfy indai baki fadamin wadda ya bata miki fuska ba ton wlh duk wadda nagani sara ne"

Rudewa asma'u tayi cikin kuka tace a'a wlh yaya nane"

Yayan ki?, toh wlh sainaci uwassa, zai shaida cewa bakin rijiya bawajen wasa makaho bane, yasin saina canza mai halitta

*Mmn Yaxeed*馃崄鈥�
[22:50, 12/19/2017] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挆馃挐馃挐馃挆
鈥�*BUGUN ZUCIYA*鈥�
( 鈥婬eartbeat鈥�)

馃挀馃挐馃挆
馃挆

馃挀馃挐馃挆
鈥婤y鈥�
馃挆
鈥嬧€�*Fadeela Lamido*

*@AM拢拢NCI WRITER'S ASSOCIATION馃*

1鈨�2鈨� to 1鈨�4鈨�

馃摉 Hannu asmau ta daura akai 馃檰馃徏馃檰馃徏 domin kalaman deeni sun tsuratata tsugunawa tayi sannan tace dan Allah kayi hakuri karka masa komai yaya na ne, kuma abba nane yasa shi ya dake....

Bata kaiga karasawa ba taji andauketa cak ana tafiya da ita"

Wuntsula kafa take tare da kara me tsanani"

Tana kallo ya shiga da ita wani gida wadda kusan shine gida na marusu karfi agunwar"

Wata dattijuwar mata ce ta fito aguje tare da fadin auta yau lfyr ka kuwa?

Bece komai ba kokarin shegewa dakinsa da ma'u kawai yake, ganin haka mahaifiyar tashi ta sake shan gaban shi tare da cikuikuye hijjabin ma'u tace haba auta bansan ka da wannan dabi'a ba, ka dubeta dakyau mana islamiyya zata, idan ma wani abu ta maka toh kayi hakuri kaji?

Idonshi ya dago ya daura akan na mahaifiyar shi sannan yace ummi ba abinda tamin, kawai naga tsohunta bashi sonta ne"

Hmmm auta kataba ganin Mutun ya haifi da yace baya so?, yanzun dai sauketa sai muyi mgn"

Ummi da inason ne nasata akatifa tayi bacci"

Sai wannan lokacin ma'u ta samu bakin mgn cikin kuka tace wlh ni banajin bacci mkrnt zani"

Sai kinyi bacci wannan dole ne"

Daker da sidin goshi deeni ya sauke ma'u amman duk da haka hannunta na cikin nashi"

Kujera ummi ta aje guda 2, kan daya ya zaunar da ma,u sannan yaja dayan ya zauna, cikin Wata irin murya yace ummi kawo mata kokona tasha dan da ganinta bata karya ba"

Zare ido ma'u tayi domin ita bata iya shan kokoba baya ga hakama ai makaranta zata, gashi lokaci na kurewa, hawaye kawai taji yana zobo bata acikin zuciyarta tace meyasa ban kyauce ma hanyar da zamu hadu da deeni ba? Waini me yake shirin faruwa dani?, Allah ina rokonka karkasa nazama sanadin BUGAWAR ZUCIYAN Abbana"

Daidai lokacin ummi ta ajiye babban kofi cike da koko, sannan ta mikawa ma'u ludayi"

Girgiza kai tayi tare da fadin ummi wlh ni akoshi nake nakarya kafin na fito, mikewa ta fara sannan ta sake cewa inason zan wuce mkrnt dan abbana bayanson ina tsayawa ko ina"

Fincikota deeni yayi ya maidata kan kujera sannan ya dauki kofin kokon Yasa ludayi ya deba ya nufi bakinta, yace bude"

Girgiza kai tayi sannan tayi raurau da ido tace nifa wlh akoshe nake"

kibude nace ko dan ni babu ruwana da koshin ki"

Babu yadda ta iya dole ta bude baki deeni yaita dura mata koko tasha kusan rabi amai ya kece mata, daga deeni har ummi suna tsaye akanta hartayi ta gama"

Deeni na rike da hannun asmau yana mata sannu, kan kujerar ya maidata sannan ya dauki ragowan kokon nan yacigaba da bata"

Tanashan kokon tana kuka samuda tsabar bakin ciki"

Duk abinda suke ummin deeni dake wanke2 agefe tana satan kallon su, ganin inda ma,u take hawaye yasata fadin haba auta ka kyale yariyar nan haka indai baso kake ta amaye yanhajinta ba"

Ummi nifa so nake nakoya mata sha saboda gaba"

Hmmm auta Allah ya shiryamin kai"

Saida tashanye kokon tas sannan ya juya yace ummi sammana goro"

Kallon shi tayi sannan tayi murmushi, mikewa tayi ta nufi daki tana kara binshi da kallo"

Zuwacan ta dawo dauke da roban da take jika goro ta ajiye agaban su"

Hannu deeni ya saka ya zabe fararen ciki ya mikawa asmau haka taita karba tanaci badan ranta naso ba"

Ummice ta gama wanke2 tamike ta dauki kayan zatakai kitchen kallonta ne yakai kan deeni daketa dirkawa ma'u goro tace"

Kai jama'a auta waikai meyasa baka da kan gado ne, ya zaka dauki goro kaita dirkawa yar mutane, kai komai bakayin shi ahankali saidai da karfin tsiya, kitchen ta shige tana cigaba da korafi"

Mayar da goron dake hannun shi yayi cikin ruwan sannan ya juya ya kalleta yace toh yanzun inna zan rakaki makaranta ko gida?

Ahankali tace karfe nawa ne yanzun?

11:15am ya fada yana kallon cikin idonta"

馃槼 Nashiga uku ni gida zani"

Daidai lokacin ummi tayi kiran deeni, dan haka ya mike yana fadin barin dawo"

Asmau bayan shi tabi da kallo tana ganin shiganshi ta ta mike ta kwashe takalminta ahannu ta fara ta fiya cikin sanda"

Ahankali ta bude kofar gidan ta fallah aguje"

Karan kofar gidan ne ya fito da ummi da deeni daga cikin kitchen din"

Ahanzar ce ya nufi kofar gida, hango ma,u yayi tana falla uban gudu dan haka abin yai matukar bashi dariya"

Dariya yake sosai besan cewa yayi nisa adariyar ba saida yaji muryuyin yan mkrntr su ma,u , cikin sauri ya murtuke fuska sannan ya nufi gida"

Kujerar da ma,u ta tashi yaje ya zauna sannan ya dauke alaiyahun da ummi take tsinkewa ya fara tayata"

Dagowa tayi fuskarta dauke da murmushi tace"

Auta wannan yariyar a ina ka samota?

murmushi yayi kadan sannan yace nan nake ganinta idan zata mkrnt"

Itama murmushi tayi tana kallo cikin idon deeni sannan tace auta da alama dai ka fada soyayya"

Murmushi yayi kadan sannan ya dan basar yace a'a ummi"

Fuskanta kara fadada tayi da murmushi tare da kara kallon cikin idonshi tace toh idan warin ya bunkasa ai zamuji, amman dai akwai shawaran da zan baka"

Kai ya daga ya kalleta sannan yace inajin ki ummi"

Auta ba atura soyayya da karfin tsiya, ita mace yar lallashi ce, idan har kana son tasoka toh ka daina ta kura mata in banda karfin hali irin naka da baka son azauna lfy ya zaka takura yariya dole saita sha koko"

Ummi jinayi kawai inason tasha"

Toh daga yau idan ka bata wani abu tace bataci karka matsa mata"

Zan bari ummi amman ni basonta nake ba, kawai jarumtar ta ke burge ni"

Hmmm kawai ummi tace sannan taci gaba da kallon sa"

Itako ma,u saida ta ganta aharaban gidan su ta tsaya tsayawa tayi numfashin ta ya dawo daidai sannan ta shiga gida"

Ranan wuni ma,u tayi tana tunanin duna, ita dai batasan abinda ke damunta ba hakanan takeson ganin sa, duk da cewa yau ya firgita ta besa taji tana kinsa ba"
Chapter 5 · 0% Book details